Bayarwa

Ana nuna bayarwa a matsayin gwajin bangaskiya, ƙauna da ikon Ubangiji, tare da mai da hankali ga halin mai bayarwa, wanda ya kamata ya zama na ƙauna da farin ciki. Nassi yana nuna amfanin bayarwa, kamar ƙarin kusanci da Allah, lada a sama da albarka a duniya, yana kuma yin magana game da zakka a matsayin irin bayarwa.

Gwaje-gwajen bayarwa

Gwajin bangaskiya

Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa? A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini, sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani? Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce. (Yaƙub 2:14-17)

Gwajin ƙaunar Allah da ke zaune a cikinmu

In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? (1 Yohanna 3:17)

Gwajin ƙaunar maƙwabcinmu

Ba umarni nake ba ku ba, sai dai ina so in gwada gaskiyar ƙaunarku ne, ta wurin kwatanta ta da aniyar waɗansu. (2 Korintiyawa 8:8)

Misalin Basamariye Mai Kirki

Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa. Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa. Kashegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’ (Luka 10:33-35)

Gwajin ikon Ubangiji bisa rayuwarmu

Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.” Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai. (Mattiyu 19:21-22)
Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.” Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai. (Markus 10:21-22)
Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.” Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai. (Luka 18:22-23)

Halayen bayarwa

Halin Allah

Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. (Yohanna 3:16)
Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana. Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa. (1 Yohanna 4:16)
Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau. (Yaƙub 1:17)

Halinmu

Wane ne hali mai kyau?

Cikin ƙauna

In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba. (1 Korintiyawa 13:3)

Da farin ciki

Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. (2 Korintiyawa 9:7)

Ta yaya za mu bayar da ƙauna?

Ka ba wa Ubangiji a matsayin bayyana ƙauna da sujada

“Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo mini hadaya. Za ka karɓi hadaya daga hannun kowane mutum wanda zuciyarsa ta yarda yă bayar. (Fitowa 25:2)
“Sa’ad da za ku ƙidaya Isra’ilawa, dole kowanne yă biya domin yă fanshe kansa ga Ubangiji a lokacin da aka ƙidaya shi. Ta haka babu wata annobar da za tă buge su sa’ad da kuke ƙidaya su. Kowannen da ya ƙetare zuwa wurin waɗanda aka riga aka ƙidaya, dole yă ba da rabin shekel, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda nauyinsa garwa ashirin ne. Wannan rabin shekel hadaya ce ga Ubangiji. Duk waɗanda suka ƙetare, waɗanda shekarunsu ya kai ashirin ko fiye, za su ba da hadaya ga Ubangiji. (Fitowa 30:12-14)
Daga cikin abin da kuke da shi, ku ɗauki kyauta domin Ubangiji, duk wanda yana niyya, sai yă kawo wa Ubangiji kyauta ta, “zinariya, azurfa da tagulla; (Fitowa 35:5)
...duk waɗanda suke da niyya, waɗanda kuma zukatansu suka motsa su, suka kawo kyautai wa Ubangiji, don aikin Tentin Sujada, don duk aikinsa, da don tsarkakakkun riguna. Duk waɗanda suke da niyya, maza da mata, gaba ɗaya, suka kawo kayan ado na zinariya na kowane iri. ’Yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri-iri. Dukansu suka miƙa zinariyarsu a matsayin hadaya ga Ubangiji. Kowane mutumin da yake da shuɗi, shunayya ko jan zare, ko lallausan lilin, ko gashin akuya, ko fatun rago da aka rina ja, ko fatun shanun teku, suka kawo. Masu miƙa kyautar azurfa, ko tagulla suka kawo su a matsayin kyautai ga Ubangiji, kuma kowane mutumin da yake da itacen ƙirya don kowane sashin aikin, ya kawo. Kowace mace mai fasaha ta kaɗa zare da hannuwanta, ta kuma kawo abin da ta kaɗa na shuɗi, shunayya, ko jan zare, ko lallausan lilin. Kuma dukan matan da suke da niyya, suke kuma da fasaha, suka kaɗa gashin akuya. Shugabannin suka kawo duwatsun Onis. Da duwatsu masu daraja don a jera a kan efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Suka kawo kayan yaji da man zaitun don fitila da don man shafewa da kuma don turare mai ƙanshi. Dukan mazan Isra’ilawa da matan da suke da niyya suka kawo wa Ubangiji kyautai na yardar rai, domin dukan aikin da Ubangiji ya umarce su ta bakin Musa. (Fitowa 35:21-29)
Zai kuma kawo ɗaya daga kowace a matsayin hadaya, baiko ne ga Ubangiji. Wannan zai zama na firist da ya yafa jinin hadaya ta salama ne. (Firistoci 7:14)
Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayun da za a miƙa mini, dukan tsarkakan hadayun da Isra’ilawa suka ba ni, na ba ka su su zama rabonka da na ’ya’yanka har abada. Kai za ka riƙe sashe mafi tsarki na hadayun da suka ragu daga wuta. Daga dukan kyautai mafi tsarki na hadayun da suka miƙa mini, ko ta gari, ko don zunubi, ko kuma don laifi, wannan kashi naka ne da ’ya’yanka. Ku ci shi a matsayin abu mafi tsarki; kowane namiji zai ci. Dole ku ɗauke shi da tsarki. “Har yanzu kuma duk abin da aka keɓe daga kyautai na dukan hadayun kaɗawa na Isra’ilawa naka ne. Na ba da wannan gare ka da ’ya’yanka maza da mata, a kowane lokaci. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci. “Na ba ka duk man zaitun mafi kyau, da ruwan inabi mafi kyau duka, da hatsi mafi kyau duka na nunan farinsu da suke bayarwa ga Ubangiji. Dukan nunan fari na ƙasar da suke kawo wa Ubangiji, zai zama naka. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci. “Kome a Isra’ila da aka keɓe wa Ubangiji, zai zama naka. Kowane haihuwar fari, ta mutum, ko ta dabba da suka miƙa wa Ubangiji, naka ne. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram. Sa’ad da suke wata ɗaya da haihuwa, dole a fanshe su a bakin shekel biyar-biyar, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri da ake amfani da shi, wanda nauyinsa ya kai gera ashirin. “Amma kada ka fanshe ɗan fari na saniya, tunkiya, ko akuya; gama suna da tsarki. Ka yayyafa jininsu a bisan bagade, ka kuma ƙone kitsensu kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Namansu zai zama naka, haka ma ƙirji na kaɗawa da cinyar dama za su zama naka. Kome da aka keɓe daga tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da ’ya’yanka maza da mata a matsayin zaunannen rabo. Wannan madawwamin alkawarin gishiri ne a gaban Ubangiji dominka da zuriyarka.” Ubangiji ya ce wa Haruna, “Ba ka da gādo a ƙasarsu, ba kuwa za ka sami rabo daga cikinsu ba; ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra’ilawa. “Na ba wa Lawiyawa dukan zakka na Isra’ilawa a matsayin gādonsu, saboda aikin da suke yi yayinda suke hidima a Tentin Sujada. Daga yanzu zuwa gaba, kada Isra’ilawa su yi kusa da Tentin Sujada, in ba haka ba kuwa su sha hukuncin zunubinsu, su kuma mutu. Lawiyawa ne za su yi aikin Tentin Sujada, su kuma ɗauki nauyin kowane laifin da aka aikata a wurin. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce daga yanzu har tsararraki masu zuwa. Ba za su sami gādo a cikin Isra’ilawa ba. A maimako haka, na ba wa Lawiyawa zakka da Isra’ilawa suka kawo domin hadaya ga Ubangiji, a matsayin gādonsu. Shi ya sa na ce game da su, ‘Ba su da gādo a cikin Isra’ilawa.’ ” (Ƙidaya 18:8-24)
Sarki Dawuda ya miƙa waɗannan kayayyakin ga Ubangiji, kamar yadda ya yi da azurfa da kuma zinariyan da ya kwaso daga dukan waɗannan al’ummai. Edom da Mowab, Ammonawa da Filistiyawa, da kuma Amalek. (1 Tarihi 18:11)
Yawanci mutane suka kawo hadayun ƙonawa zuwa Urushalima wa Ubangiji da kuma kyautai masu daraja wa Hezekiya sarkin Yahuda. Daga lokacin zuwa gaba dukan ƙasashe suka girmama shi. (2 Tarihi 32:23)
Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan kayayyaki wa Ubangiji, yadda ya yi da zinariya, da kuma azurfa daga dukan al’umman da ya mallaka, (2 Sama’ila 8:11)
“Ku miƙa hadayar godiya ga Allah, ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka, (Zabura 50:14)
Zan zo haikalinka da hadayun ƙonawa zan kuwa cika alkawurana gare ka, (Zabura 66:13)
Saboda haikalinka a Urushalima sarakuna za su kawo maka kyautai. (Zabura 68:29)
Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro. (Zabura 76:11)
Gama a kan dutsena mai tsarki, dutse mai tsayi na Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, a can a ƙasar gidan Isra’ila gaba ɗaya za su bauta mini, a can kuwa zan karɓe su. A can zan bukaci hadayunku da sadake sadakenku mafi kyau, tare da dukan tsarkakan hadayunku. (Ezekiyel 20:40)
“Ki tashi ki yi sussuka, ya Diyar Sihiyona, gama zan ba ki ƙahonin ƙarfe; zan ba ki kofatan tagulla domin ki ragargaje al’ummai masu yawa.” Za ki ba Ubangiji dukan dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba, wadatarsu kuma ga Ubangiji dukan duniya. (Mika 4:13)

Duk abin da muke da shi daga Ubangiji ne, kuma muna mayar masa ne

“Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne. Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya. Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne. (1 Tarihi 29:14-16)

Misalin Yaron nan Kristi

Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima (Mattiyu 2:1)

Misalin rashin bayarwa ga Ubangiji

Ba ku kawo mini tumaki don hadaya ta ƙonewa ba, balle ku girmama ni da hadayunku. Ban nawaita muku da hadaya ta gari ba balle in gajiyar da ku da bukatar turare. Ba ku saya wani turaren kalamus domina ba ko ku gamshe ni da kitsen hadayunku. Amma kun nawaita ni da zunubanku kuka kuma gajiyar da ni da laifofinku. (Ishaya 43:23-24)

Ka bayar da farin ciki ta wurin miƙa kai ga Ubangiji / ka bayar da yardar rai

...don aikin zinariya da kuma aikin azurfa, don kuma dukan aikin da gwanaye za su yi. Yanzu fa wa yake da niyya yă miƙa kansa a yau don Ubangiji?” Sai shugabannin iyalai, shugabannin kabilan Isra’ila, manyan hafsoshin mayaƙa dubu-dubu da manyan hafsoshi mayaƙa ɗari-ɗari, da shugabannin lura da ayyukan sarki suka yi bayarwa da yardar rai. Suka bayar talenti dubu biyar na zinariya, talenti dubu goma na azurfa, talenti dubu goma sha takwas na tagulla da talenti dubu ɗari na ƙarfe don aiki a haikalin Allah. Duk waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka ba da su ga Yehiyel mutumin Gershon ma’ajin haikalin Ubangiji. Mutane suka yi farin ciki ganin yadda shugabanninsu suke bayarwa da yardar rai, gama sun bayar hannu sake da kuma dukan zuciya ga Ubangiji. Dawuda sarki shi ma ya yi farin ciki ƙwarai. (1 Tarihi 29:5-9)
“Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne. Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya. Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne. Na sani, Allahna, cewa kakan gwada zuciya, kakan kuma gamsu da mutunci. Dukan waɗannan abubuwa na bayar da yardar rai da kuma kyakkyawar niyya. Yanzu kuma da farin ciki na ga yadda mutanenka waɗanda suke a nan da yardar rai suka ba ka. (1 Tarihi 29:14-17)
To, ’yan’uwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya. Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci. Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu, sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka. Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah. (2 Korintiyawa 8:1-5)

Hali ya fi muhimmanci fiye da yawan abin da aka bayar

“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku, na’ana’a, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki, adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba. (Mattiyu 23:23)
“Kaitonku, Farisiyawa, domin kuna ba wa Allah zakka na na’ana’arku, da ƙarƙashinku, da kuma sauran ganyen lambunku iri-iri, amma kun ƙyale adalci da ƙaunar Allah. Ya kamata da kun kiyaye na ƙarshen, ban ba barin na farkon. (Luka 11:42)
“Waɗansu mutane biyu sun tafi haikali don yin addu’a. Ɗaya Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji. Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan. Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’ “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’ “Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.” (Luka 18:10-14)

Bayarwa da hali mai kyau / Ubangiji ya karɓi baiwar

Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo, (Farawa 4:4)
Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadayar da ta fi wadda Kayinu ya miƙa. Ta wurin bangaskiya aka yabe shi cewa shi mai adalci ne, sa’ad da Allah ya yi magana mai kyau game da bayarwarsa. Ta wurin bangaskiya kuma har yanzu yana magana, ko da yake ya riga ya mutu. (Ibraniyawa 11:4)
An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai. (Filibbiyawa 4:18)

Bayarwa da mugun hali / Ubangiji ya ƙi baiwar

Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji. Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo, amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace. (Farawa 4:3-5)
“Ku tafi Betel ku yi ta aikata zunubi; ku je Gilgal ku ƙara yin zunubi. Ku kawo hadayunku kowace safiya, zakkarku kowace shekara uku. Ku ƙona burodinku mai yisti kamar hadaya ta godiya, ku yi fariya game da hadayunku na yarda rai, ku yi taƙama game da su, ya ku Isra’ilawa, gama abin da kuke jin daɗin aikata ke nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “Na bar ku da yunwa a kowace birni, da kuma rashin abinci a kowane gari, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji. (Amos 4:4-6)
Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi, ba zan karɓa ba. Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta, ba zan ɗauke su a bakin kome ba. Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi, adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa! (Amos 5:22, 24)
“Kun kawo mini hadayu da sadakoki shekaru arba’in a cikin jeji, ya ku gidan Isra’ila? Kun ɗaga masujadar sarkinku, siffofin gumakanku, tauraron allahnku, wanda kuka yi wa kanku. Saboda haka zan tura ku zaman bauta gaba da Damaskus,” in ji Ubangiji, wanda sunansa ne Allah Mai Iko. (Amos 5:25-27)
Ga kuma wani abin da kuke yi. Kukan cika bagaden Ubangiji da hawaye. Kukan yi kuka kuna ihu gama Ubangiji ba ya mai da hankali ga hadayunku ko yă karɓe su da farin ciki. Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari. (Malaki 2:13-14)

Yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya

To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa. Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni. Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin? Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.” Da Ananiyas ya ji wannan, sai ya fāɗi ya mutu. Sai babban tsoro kuwa ya kama duk waɗanda suka ji abin da ya faru. Sai samari suka zo gaba, suka naɗe gawarsa, suka fitar da shi suka je suka binne. Bayan kusan awa uku, sai matarsa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba. Bitrus ya tambaye ta ya ce, “Gaya mini, kuɗin da yake da Ananiyas kuka sayar da filin ke nan?” Ta ce, “I, haka ne muka sayar.” Bitrus ya ce mata, “Ta yaya kuka yarda ku gwada Ruhun Ubangiji? Duba! Sawun mutanen da suka binne mijinki suna bakin ƙofa, za su kuwa ɗauke ki zuwa waje ke ma.” Nan take ta fāɗi a ƙafafunsa ta mutu. Sai samarin suka shigo ciki, suka kuwa same ta matacciya, suka ɗauke ta suka kai ta waje suka binne ta kusa da mijinta. (Ayyukan Manzanni 5:1-10)

Don a ba da hujjar zunubi

“Ina da hadaya ta salama a gida; yau zan cika alkawarina. (Karin Magana 7:14)

Amfanin bayarwa

Amfani ga mai bayarwa

Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ” (Ayyukan Manzanni 20:35)

Ƙaruwar kusanci da Ubangiji

Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance. (Mattiyu 6:21)
Gama inda dukiyarku take, nan ne zuciyarku ma take. (Luka 12:34)

Ƙaruwa a sama

Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata. (Mattiyu 6:20)
Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.” (Mattiyu 19:21)
Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za tă kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba. (Luka 12:33)
“Ka yi wa Lawiyawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka karɓi zakka daga Isra’ila da na ba ku gādo, dole ku miƙa kashi ɗaya bisa goma na wannan zakka a matsayin hadaya ga Ubangiji. (Ƙidaya 18:26)
Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.” (Luka 18:22)
Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku. (Filibbiyawa 4:17)
Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce. (1 Timoti 6:17-19)

Ƙaruwa a duniya

A ƙarshen kowace shekara uku, ku kawo dukan zakkarku na amfanin gona na wannan shekara, ku ajiye su a cikin birane, saboda Lawiyawa (waɗanda ba su da rabo ko gādo na kansu) da baƙo, da marayu, da kuma gwauraye, waɗanda suke zama a biranenku, su zo su ci su ƙoshi, ta haka Ubangiji Allahnku zai albarkace ku cikin dukan ayyukan hannuwanku. (Maimaitawar Shari’a 14:28-29)
...sai Azariya babban firist, daga iyalin Zadok ya amsa, “Tun daga lokacin da mutane suka fara kawo taimakonsu ga haikalin Ubangiji, muna da isashe don abinci da kuma da yawa da za mu rage, domin Ubangiji ya albarkaci mutanensa, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.” (2 Tarihi 31:10)
Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka; ta haka rumbunanka za su cika har su zuba, randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi. (Karin Magana 3:9-10)
Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye; wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci. Mutum mai kyauta zai azurta; shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi. (Karin Magana 11:24-25)
Ka jefa burodinka a bisa ruwaye, gama bayan kwanaki masu yawa, za ka sāke samunsa. (Mai Hadishi 11:1)
Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.” (Luka 6:38)
Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ya ba gajiyayyu hannu sake, ayyukansa na alheri madawwama ne.” To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah. (2 Korintiyawa 9:6-11)
Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu. (Filibbiyawa 4:19)

Ƙalubale a gwada Ubangiji don ƙaruwar abin duniya

Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki. (Malaki 3:10)

Ƙaruwar albarka

Mafi kyau na nunan farinku da kuma dukan kyautanku na musamman za su zama na firistoci. Za ku ba su rabo na fari na ɓarzajjen hatsinku saboda albarka ta kasance a gidanku. (Ezekiyel 44:30)
A can, akwai wani bawan wani jarumin yana ciwo, yana kuma a bakin mutuwa. Maigidansa kuwa yana sonsa sosai. Jarumin sojan ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu dattawan Yahudawa wajensa, yana roƙonsa yă zo yă warkar da bawansa. Da suka isa wurin Yesu, sai suka roƙe shi sosai, suka ce, “Wannan mutum, ai, ya dace a yi masa haka, gama yana ƙaunar al’ummarmu ta Yahudawa, har ya gina majami’armu.” (Luka 7:2-5)
A Yoffa akwai wata almajira mai suna Tabita (a harshen Girik sunanta shi ne Dokas); ita mai aikin alheri ce kullum, tana kuma taimakon matalauta. A lokacin nan ta yi rashin lafiya ta mutu, aka kuma yi wa gawarta wanka aka ajiye a wani ɗaki a gidan sama. Bitrus ya fitar da su duka daga ɗakin; sa’an nan ya durƙusa ya yi addu’a. Da ya juya wajen matacciyar, sai ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe idanunta, ta ga Bitrus sai ta tashi zaune. (Ayyukan Manzanni 9:36-37, 40)
A Kaisariya akwai wani mutum mai suna Korneliyus, wani jarumin Roma ne, a ƙungiyar soja da ake kira Bataliyar Italiya. Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma addu’a ga Allah ba fasawa. Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani mala’ikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!” Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?” Mala’ikan ya ce, “Addu’o’inka da kyautanka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah. ya ce, ‘Korneliyus, Allah ya ji addu’arka, ya kuma tuna da kyautanka ga matalauta. (Ayyukan Manzanni 10:1-4, 31)

Yawan abin da za a bayar

Zakka

Kafin Shari’a

Kuma albarka ta tabbata ga Allah Mafi Ɗaukaka wanda ya ba da maƙiyanka a hannunka.” Sa’an nan Abram ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome. (Farawa 14:20)
Sa’an nan Yaƙub ya yi alkawari cewa, “In Allah zai kasance tare da ni yă kuma lura da ni a wannan tafiya, yă kuma ba ni abinci in ci da tufafi in sa, har in dawo lafiya zuwa gidan mahaifina, to, Ubangiji zai zama Allahna kuma wannan dutsen da na kafa al’amudi, zai zama gidan Allah, kuma dukan abin da ka ba ni zan ba ka kashi ɗaya bisa goma.” (Farawa 28:20-22)

A ƙarƙashin Shari’a

“ ‘Ushirin kome daga gona, ko hatsi daga ƙasa, ko ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, na Ubangiji ne, mai tsarki ne ga Ubangiji. In mutum ya fanshi wani zakansa, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar. Ushirin gaba ɗaya na garken shanu, da na tumaki, kowane kashi ɗaya bisa goma na dabbar da ta wuce ƙarƙashin sandan mai kiwo, za tă zama mai tsarki ga Ubangiji. (Firistoci 27:30-32)

Rashin ba da zakka sata ne daga Allah

“Mutum zai iya yi wa Allah fashi ne? Duk da haka kun yi mini fashi. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka yi maka fashi?’ “A wajen zakka da hadayu. Kuna ƙarƙashin la’ana, dukan al’ummarku, domin kuna yin mini fashi. (Malaki 3:8-9)

An ci zakka a gaban Ubangiji

Ku tabbata kun keɓe kashi ɗaya bisa goma na amfanin gonakinku kowace shekara. Ku ci zakkar hatsinku, da na sabon ruwan inabinku, da na manku, da kuma na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da ya zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa, don ku koyi girmama Ubangiji Allahnku kullum. Amma in wurin nan yana da nisa sosai, Ubangiji Allahnku kuma ya albarkace ku, ba za ku kuwa iya riƙe zakkarku ba (Saboda wurin da Ubangiji ya zaɓa yă sa Sunansa ya yi nisa sosai), to, sai ku sayar da zakkar, ku tafi da kuɗin wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Yi amfani da kuɗin ku saya duk abin da kuke so, ko shanu, ko tumaki, ko ruwan inabi, ko dai wani abin shan da ya yi tsami, ko kuwa duk abin da kuke so. Sai ku da gidanku, ku ci a can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku kuma yi farin ciki. (Maimaitawar Shari’a 14:22-26)

An ba da zakka domin tallafa wa Lawiyawa da matalauta

“Na ba wa Lawiyawa dukan zakka na Isra’ilawa a matsayin gādonsu, saboda aikin da suke yi yayinda suke hidima a Tentin Sujada. Daga yanzu zuwa gaba, kada Isra’ilawa su yi kusa da Tentin Sujada, in ba haka ba kuwa su sha hukuncin zunubinsu, su kuma mutu. Lawiyawa ne za su yi aikin Tentin Sujada, su kuma ɗauki nauyin kowane laifin da aka aikata a wurin. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce daga yanzu har tsararraki masu zuwa. Ba za su sami gādo a cikin Isra’ilawa ba. A maimako haka, na ba wa Lawiyawa zakka da Isra’ilawa suka kawo domin hadaya ga Ubangiji, a matsayin gādonsu. Shi ya sa na ce game da su, ‘Ba su da gādo a cikin Isra’ilawa.’ ” (Ƙidaya 18:21-24)
A ƙarshen kowace shekara uku, ku kawo dukan zakkarku na amfanin gona na wannan shekara, ku ajiye su a cikin birane, saboda Lawiyawa (waɗanda ba su da rabo ko gādo na kansu) da baƙo, da marayu, da kuma gwauraye, waɗanda suke zama a biranenku, su zo su ci su ƙoshi, ta haka Ubangiji Allahnku zai albarkace ku cikin dukan ayyukan hannuwanku. (Maimaitawar Shari’a 14:28-29)
Sa’ad da kuka gama fitar da kashi ɗaya bisa goma na dukan amfanin gona a shekara ta uku, shekarar zakka, za ku ba da su ga Balawe, baƙo, maraya da kuma gwauruwa, don su ci a cikin garuruwanku su ƙoshi. (Maimaitawar Shari’a 26:12)
Ya umarci mutanen da suke zama a Urushalima su ba da rabon da yake na firistoci da Lawiyawa, don su ƙwallafa ransu ga Dokar Ubangiji. Nan da nan aka baza umarnin, sai Isra’ilawa suka bayar ’ya’yan farin hatsinsu, sabon ruwan inabi, mai da kuma zuma da dukan abin da gona ta bayar, hannu sake. Suka kawo zakan kowane abu da yawa. Mutanen Isra’ila da Yahuda waɗanda suke zama a garuruwan Yahuda, su ma suka kawo zakan shanu da na tumaki da kuma zakan abubuwa masu tsarki da aka keɓe ga Ubangiji Allahnsu, suka jibge su tsibi-tsibi. Sun fara yin haka a wata na uku, suka kuma gama a wata na bakwai. Sa’ad da Hezekiya da fadawansa suka zo suka ga tsibin, sai suka yabi Ubangiji, suka kuma albarkace mutanensa Isra’ila. Hezekiya ya tambayi firistoci da Lawiyawa game da tsibin; sai Azariya babban firist, daga iyalin Zadok ya amsa, “Tun daga lokacin da mutane suka fara kawo taimakonsu ga haikalin Ubangiji, muna da isashe don abinci da kuma da yawa da za mu rage, domin Ubangiji ya albarkaci mutanensa, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.” Hezekiya ya ba da umarni a shirya ɗakunan ajiya a haikalin Ubangiji, aka kuwa yi haka. Sa’an nan cikin aminci suka kawo taimako, zakka da keɓaɓɓun kyautai. Konaniya, wani Balawe, shi ne ke lura da waɗannan abubuwa, kuma ɗan’uwansa Shimeyi shi ne na biye da shi. (2 Tarihi 31:4-12)
“Ban da haka ma, za mu kawo wa ɗakunan ajiyar gidan Allahnmu, abincinmu na farko daga ƙasa, na hadayun hatsinmu, na ’ya’yan dukan itatuwanmu da kuma na sabon ruwan inabinmu da mai namu wa firistoci. Za mu kuma kawo zakkar hatsinmu wa Lawiyawa, gama Lawiyawa ne ke karɓan Zakka cikin dukan garuruwan da muke noma. Firist wanda yake daga zuriyar Haruna zai raka Lawiyawa sa’ad da suke karɓan zakka, Lawiyawan kuma za su kawo kashi ɗaya bisa goma na zakka zuwa gidan Allahnmu, su kawo a ɗakunan ajiya na baitulmali. (Nehemiya 10:37-38)
Na kuma ji cewa sassan da ake ba wa Lawiyawa ba a ba su ba, cewa kuma dukan Lawiyawa da mawaƙan da suke da hakkin hidima sun koma gonakinsu. Sai na tsawata wa shugabanni na kuma tambaye su na ce, “Me ya sa aka ƙyale gidan Allah?” Sa’an nan na kira su gaba ɗaya na sa su a wuraren aikinsu. (Nehemiya 13:10-11)

Lawiyawa su ba da zakka daga zakkar da suka karɓa

“Ka yi wa Lawiyawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka karɓi zakka daga Isra’ila da na ba ku gādo, dole ku miƙa kashi ɗaya bisa goma na wannan zakka a matsayin hadaya ga Ubangiji. (Ƙidaya 18:26)

Zakka a Sabon Alkawari

Fifikon firistancin Melkizedek

Wannan Melkizedek sarkin Salem ne da kuma firist na Allah Mafi Ɗaukaka. Shi ne ya sadu da Ibrahim ya albarkace shi sa’ad da Ibrahim ya dawowa daga cin nasara a bisa sarakuna, Ibrahim kuwa ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome. Ma’anar sunan Melkizedek ita ce, “sarkin adalci.” Amma da yake Salem yana nufin “salama,” shi kuma “Sarkin salama” ne. Ku dubi irin girman da Melkizedek mana. Ko kakanmu Ibrahim ma ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na ganima! Yanzu doka ta umarci zuriyar Lawi waɗanda suka zama firistoci su karɓi kashi ɗaya bisa goma daga wurin mutane, wato, ’yan’uwansu, ko da yake ’yan’uwansu zuriyar Ibrahim ne. Ko da yake Melkizedek ba daga zuriyar Lawi ba ne, duk da haka Ibrahim ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na abin da yake da shi, Melkizedek kuwa ya sa masa albarka, shi da aka yi wa alkawura. Kowa ya sani cewa na gaba shi yake sa wa na baya albarka. Firistoci ake ba wa kashi ɗaya bisa goma na abin da mutane suke samu. Amma dukan firistoci sukan mutu, sai dai Melkizedek, kuma nassi ya ce yana da rai. Ana ma iya cewa zuriyar Lawi, mai karɓar kashi ɗaya bisa goma daga mutane, ya ba da kashi ɗaya bisa goma ta wurin Ibrahim, (Ibraniyawa 7:1-2, 4-9)

Zakka a gidan ajiya

Hezekiya ya ba da umarni a shirya ɗakunan ajiya a haikalin Ubangiji, aka kuwa yi haka. Sa’an nan cikin aminci suka kawo taimako, zakka da keɓaɓɓun kyautai. Konaniya, wani Balawe, shi ne ke lura da waɗannan abubuwa, kuma ɗan’uwansa Shimeyi shi ne na biye da shi. (2 Tarihi 31:11-12)
Firist wanda yake daga zuriyar Haruna zai raka Lawiyawa sa’ad da suke karɓan zakka, Lawiyawan kuma za su kawo kashi ɗaya bisa goma na zakka zuwa gidan Allahnmu, su kawo a ɗakunan ajiya na baitulmali. (Nehemiya 10:38)
A lokacin an naɗa mutane su lura da ɗakunan ajiya don sadakoki, nunan fari da kuma zakka. Daga gonakin garuruwan da suke kewaye za su kawo sassan da Dokar ta umarta zuwa ɗakunan ajiya domin firistoci da Lawiyawa, gama Yahuda ya ji daɗin aikin firistoci da Lawiyawa. (Nehemiya 12:44)
Dukan Yahuda suka kawo zakan hatsi, sabon ruwan inabi da mai cikin ɗakunan ajiya. (Nehemiya 13:12)

Bayarwa gwargwadon abin da Allah ya ba ka

Sa’an nan ku yi shagalin Bikin Makoni ga Ubangiji Allahnku, ta wurin ba da hadaya ta yardar rai daidai da albarkun da Ubangiji Allahnku ya yi muku. (Maimaitawar Shari’a 16:10)
Sau uku a shekara dukan maza su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa; a Bikin Burodi Marar Yisti, da a Bikin Makoni, da kuma a Bikin Tabanakul. Babu wani da zai bayyana a gaban Ubangiji hannu wofi. (Maimaitawar Shari’a 16:16)
A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba. (1 Korintiyawa 16:2)

Misalan bayarwa gwargwadon abin da mutum yake da shi

Bisa ga ƙarfinsu suka bayar da darik 61,000 na zinariya, da maina 5,000 na azurfa, da rigunan firistoci guda 100. (Ezra 2:69)
Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudummawa ga ’yan’uwan da suke zama a Yahudiya. (Ayyukan Manzanni 11:29)

Abin da aka bayar gwargwadon iyawar mutum abin karɓuwa ne

Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba. (2 Korintiyawa 8:12)

Bayarwa ta sadaukarwa

Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin ɗakunan ajiya haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa. Amma wata matalauciya gwauruwa, ta zo ta saka anini biyu, da suka yi daidai da rabin kobo. Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin ɗakunan ajiya nan ya fi na sauran dukan. Dukansu sun bayar ne daga cikin arzikinsu; ita kuwa, daga cikin talaucinta, ta ba da kome, duk abin da take da shi na rayuwa.” (Markus 12:41-44)
Da Yesu ya ɗaga ido, sai ya ga waɗansu masu arziki suna sa baikonsu a ma’ajin haikalin. Ya kuma ga wata gwauruwa matalauciya, ta saka anini biyu. Sai ya ce, “Gaskiya ina faɗa muku, wacce nan gwauruwa matalauciya ta sa fiye da dukan sauran. Dukan mutanen nan sun ba da baikonsu daga cikin arzikinsu ne, amma ita daga cikin talaucinta, ta saka duk abin da take da shi na rayuwa.” (Luka 21:1-4)
To, ’yan’uwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya. Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci. Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu, sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka. (2 Korintiyawa 8:1-4)

Kada ka bayar da abin da bai ɗauki komai daga gare ka ba

Arauna ya ce, “Me ya sa ranka yă daɗe, sarki ya zo wajen bawansa?” Dawuda ya ce, “Don in saya masussukarka, saboda in gina wa Ubangiji bagade don a tsayar da annoban da suke a bisa mutane.” Arauna ya ce wa Dawuda, “Bari ranka yă daɗe, sarki yă ɗauki duk abin da ya ga dama yă miƙa shi. Ga shanu, don hadaya ta ƙonawa, ga kuma kayan masussuka da itacen shanu, don itace.” Dukan wannan, ranka yă daɗe, Arauna ya ba wa sarki. Arauna ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahnka yă karɓa.” Amma sarki ya ce wa Arauna, “A’a, dole in biya ka saboda waɗannan. Ba yadda zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da bai ci mini kome ba.” Sai Dawuda ya saya, ya kuma biya masussukar, da shanun a bakin shekel hamsin na azurfa. (2 Sama’ila 24:21-24)
Dawuda ya ce wa Ornan, “Ka ba ni masussukarka saboda in gina bagade wa Ubangiji, don annobar da take kan mutane tă daina. Ka sayar mini ita a cikakken kuɗinta.” Ornan ya ce wa Dawuda, “Ka karɓa! Bari ranka yă daɗe, sarki yă yi duk abin da ya ga ya yi masa kyau. Duba, zan ba da shanu domin hadaya ta ƙonawa, da itacen sussuka, da kuma alkama domin hadaya ta gari. Zan ba da dukan wannan.” Amma Sarki Dawuda ya amsa wa Ornan ya ce, “A’a, na nace zan biya cikakken kuɗinta. Ba zan karɓi abinka kawai don Ubangiji ba, ko in miƙa hadaya ta ƙonawar da ba tă ci mini wani abu ba.” (1 Tarihi 21:22-24)

La’ana idan an bayar da abin sata ko mai lahani

“Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bawa kuma yakan girmama maigidansa. In ni mahaifi ne, ina girman da ya dace da ni? In ni maigida ne, ina girman da ya dace da ni?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Ku firistoci, ku ne kuka rena sunana. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka rena sunanka?’ “Kun ajiye abinci mai ƙazanta a kan bagadena. “Sai kuka ce, ‘Yaya muka ƙazantar da kai?’ “Ta wurin cewa teburin Ubangiji abin reni ne. Sa’ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, wannan daidai ne? Sa’ad da kuka miƙa gurguwar dabba ko marar lafiya, wannan daidai ne? Ku gwada ba wa gwamnanku irin wannan ku gani! Kuna gani zai ji daɗinku? Zai karɓe ku ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “To, firistoci yanzu ku gwada ku roƙi Allah yă yi mana alheri. Da irin hadayun nan a hannuwanku ne zai ji ku?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kash, da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ba na jin daɗinku, ba zan kuwa karɓi hadaya daga hannuwanku ba” in ji Ubangiji Maɗaukaki. Sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta. A kowane wuri za a miƙa wa sunana turare da tsabtacciyar hadaya domin sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Amma kun ƙazantar da sunana ta wurin cewa ‘Teburin Ubangiji ya ƙazantu,’ kuka kuma yi magana a kan abincinsa kuna cewa, ‘Abin reni ne.’ Kun kuma ce, ‘Mun gaji da irin wannan wahala!’ Kuna hura mini hancin reni,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Sa’ad da kuka kawo raunannu, gurguntattun dabbobi, ko kuma dabbobi masu fama da cuta, kuka kuma miƙa su hadaya, kuna gani zan karɓi wannan daga gare ku?” In ji Ubangiji. “La’ananne ne macucin da yake da lafiyayyiyar dabba namiji a garkensa wadda ya yi alkawari zai bayar, amma sai ya miƙa hadayar dabba mai aibi ga Ubangiji. Gama ni babban sarki ne, za a kuma ji tsoron sunana a cikin al’ummai,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. (Malaki 1:6-14)

Yadda ake bayarwa

“Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bawa kuma yakan girmama maigidansa. In ni mahaifi ne, ina girman da ya dace da ni? In ni maigida ne, ina girman da ya dace da ni?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Ku firistoci, ku ne kuka rena sunana. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka rena sunanka?’ “Kun ajiye abinci mai ƙazanta a kan bagadena. “Sai kuka ce, ‘Yaya muka ƙazantar da kai?’ “Ta wurin cewa teburin Ubangiji abin reni ne. Sa’ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, wannan daidai ne? Sa’ad da kuka miƙa gurguwar dabba ko marar lafiya, wannan daidai ne? Ku gwada ba wa gwamnanku irin wannan ku gani! Kuna gani zai ji daɗinku? Zai karɓe ku ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “To, firistoci yanzu ku gwada ku roƙi Allah yă yi mana alheri. Da irin hadayun nan a hannuwanku ne zai ji ku?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kash, da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ba na jin daɗinku, ba zan kuwa karɓi hadaya daga hannuwanku ba” in ji Ubangiji Maɗaukaki. Sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta. A kowane wuri za a miƙa wa sunana turare da tsabtacciyar hadaya domin sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Amma kun ƙazantar da sunana ta wurin cewa ‘Teburin Ubangiji ya ƙazantu,’ kuka kuma yi magana a kan abincinsa kuna cewa, ‘Abin reni ne.’ Kun kuma ce, ‘Mun gaji da irin wannan wahala!’ Kuna hura mini hancin reni,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Sa’ad da kuka kawo raunannu, gurguntattun dabbobi, ko kuma dabbobi masu fama da cuta, kuka kuma miƙa su hadaya, kuna gani zan karɓi wannan daga gare ku?” In ji Ubangiji. “La’ananne ne macucin da yake da lafiyayyiyar dabba namiji a garkensa wadda ya yi alkawari zai bayar, amma sai ya miƙa hadayar dabba mai aibi ga Ubangiji. Gama ni babban sarki ne, za a kuma ji tsoron sunana a cikin al’ummai,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. (Malaki 1:6-14)

Tsarin bayarwa

Fifiko

“Shekara shida za ku nome gonakinku ku girbe amfanin gonar, amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun. (Fitowa 23:10-11)
“Ɗan fari na kowane mutum zai zama nawa, har da ɗan farin na dabbobi, ko na garken shanu ko na tumaki. (Fitowa 34:19)
“Ku kawo nunan farin amfanin gonarku mafi kyau a gidan Ubangiji, Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa.” (Fitowa 34:26)
Za ku iya kawo su ga Ubangiji kamar hadaya ta ’ya’yan fari, amma ba za a miƙa su a bagade kamar turare mai ƙanshi ba. (Firistoci 2:12)
“ ‘A ranar nunan fari, sa’ad da za ku miƙa wa Ubangiji hadayar sabon hatsi, a lokacin Bikin Makoni, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. (Ƙidaya 28:26)
Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, kuka mallake ta, kuka kuma zauna a cikinta, sai ku ɗauki ’ya’yan fari na dukan amfanin gonar ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ku zuba a kwando. Sa’an nan ku je wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă zama mazauni don Sunansa, (Maimaitawar Shari’a 26:1-2)
Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka; (Karin Magana 3:9)

Nan da nan

“Kada ku jinkirta fitar da zakarku daga rumbunanku, ko harajin kayan da kuka saya. “Dole ku ba ni ’ya’yan farinku maza. (Fitowa 22:29)
In fa kuka yi alkawari ga Ubangiji Allahnku, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama tabbatacce Ubangiji Allahnku zai neme shi daga gare ku, za ku kuma zama masu laifin zunubi. (Maimaitawar Shari’a 23:21)
Sa’ad da ka yi alkawari ga Allah, kada ka ɓata lokaci wajen cika shi. Ba ya jin daɗin wawaye; ka cika alkawarinka. (Mai Hadishi 5:4)

Da shiri

Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. (2 Korintiyawa 9:7)

A kai a kai

A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba. (1 Korintiyawa 16:2)

Na kai da kai

Ku fanshi ɗan farin jaki da na tunkiya, amma in ba ku fanshe shi ba, ku karya wuyansa. Ku fanshi duk ’ya’yan farinku maza. “Kada wani yă zo gabana hannu wofi. (Fitowa 34:20)
Dole kowannenku yă kawo kyauta daidai yadda Ubangiji Allahnku ya albarkace shi. (Maimaitawar Shari’a 16:17)
Dukan mutanen ƙasar za su yi wannan bayarwa ta musamman saboda amfanin sarki a Isra’ila. (Ezekiyel 45:16)
Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudummawa ga ’yan’uwan da suke zama a Yahudiya. (Ayyukan Manzanni 11:29)
A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba. (1 Korintiyawa 16:2)

Ajiya a ɓoye

A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba. (1 Korintiyawa 16:2)

Ba tare da girman kai ba

“Ku yi hankali kada ku nuna ‘ayyukanku na adalci’ a gaban mutane, don su gani. In kuka yi haka, ba za ku sami lada daga wurin Ubanku da yake cikin sama ba. “Saboda haka sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan tituna, don mutane su yabe su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. Amma sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yarda hannun hagunka yă ma san abin da hannun damarka yake yi, don bayarwarka ta zama a ɓoye. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka. (Mattiyu 6:1-4)

Da zuciya mai motsuwa

“Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo mini hadaya. Za ka karɓi hadaya daga hannun kowane mutum wanda zuciyarsa ta yarda yă bayar. (Fitowa 25:2)
Daga cikin abin da kuke da shi, ku ɗauki kyauta domin Ubangiji, duk wanda yana niyya, sai yă kawo wa Ubangiji kyauta ta, “zinariya, azurfa da tagulla; (Fitowa 35:5)
...duk waɗanda suke da niyya, waɗanda kuma zukatansu suka motsa su, suka kawo kyautai wa Ubangiji, don aikin Tentin Sujada, don duk aikinsa, da don tsarkakakkun riguna. Duk waɗanda suke da niyya, maza da mata, gaba ɗaya, suka kawo kayan ado na zinariya na kowane iri. ’Yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri-iri. Dukansu suka miƙa zinariyarsu a matsayin hadaya ga Ubangiji. Kowane mutumin da yake da shuɗi, shunayya ko jan zare, ko lallausan lilin, ko gashin akuya, ko fatun rago da aka rina ja, ko fatun shanun teku, suka kawo. Masu miƙa kyautar azurfa, ko tagulla suka kawo su a matsayin kyautai ga Ubangiji, kuma kowane mutumin da yake da itacen ƙirya don kowane sashin aikin, ya kawo. Kowace mace mai fasaha ta kaɗa zare da hannuwanta, ta kuma kawo abin da ta kaɗa na shuɗi, shunayya, ko jan zare, ko lallausan lilin. Kuma dukan matan da suke da niyya, suke kuma da fasaha, suka kaɗa gashin akuya. Shugabannin suka kawo duwatsun Onis. Da duwatsu masu daraja don a jera a kan efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Suka kawo kayan yaji da man zaitun don fitila da don man shafewa da kuma don turare mai ƙanshi. Dukan mazan Isra’ilawa da matan da suke da niyya suka kawo wa Ubangiji kyautai na yardar rai, domin dukan aikin da Ubangiji ya umarce su ta bakin Musa. (Fitowa 35:21-29)
Yowash ya ce wa firistoci, “Ku tattara dukan kuɗin da ake kawo a matsayin hadayu masu tsarki na haikalin Ubangiji, kuɗin da aka tattara a ƙidaya, kuɗin da aka tattara daga wa’adin da mutum ya yi, da kuma kuɗin da aka kawo na yardan rai a haikali. (2 Sarakuna 12:4)

Ƙa’idojin bayarwa

Gudanarwa da lissafi

’Yan’uwansu Lawiyawa kuwa su ne suke lura da ma’ajin gidan Allah da kuma baitulmali don kayayyakin da aka keɓe. (1 Tarihi 26:20)
Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa. (1 Tarihi 26:26)
Kore ɗan Imna Balawe, mai tsaron Ƙofar Gabas, shi ne yake lura da baikon yardan ran da aka yi wa Allah, don ya karkasa bayarwar da aka keɓe domin Ubangiji da hadayu mafi tsarki. Eden, Miniyamin, Yeshuwa, Shemahiya, Amariya da Shekaniya sun taimake shi da aminci a cikin garuruwan firistoci, suna ba da rabo wa ’yan’uwansu firistoci bisa ga sassansu, tsofaffi da yara. (2 Tarihi 31:14-15)
A lokacin an naɗa mutane su lura da ɗakunan ajiya don sadakoki, nunan fari da kuma zakka. Daga gonakin garuruwan da suke kewaye za su kawo sassan da Dokar ta umarta zuwa ɗakunan ajiya domin firistoci da Lawiyawa, gama Yahuda ya ji daɗin aikin firistoci da Lawiyawa. (Nehemiya 12:44)
Na sa Shelemiya firist, Zadok marubuci, da wani Balawe mai suna Fedahiya su lura da ɗakunan ajiya na kuma sa Hanan ɗan Zakkur, ɗan Mattaniya ya zama mataimakinsu, domin an ɗauka waɗannan mutane amintattu ne. Aka ba su hakkin raban kayayyaki wa ’yan’uwansu. (Nehemiya 13:13)
Ga shi mun aiko ɗan’uwanmu nan tare da shi, wanda ikkilisiyoyi duka suna yabo saboda hidimarsa ga bishara. Ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikkilisiyoyi sun zaɓe shi yă riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu. Muna gudu kada wani yă zarge mu, a kan yadda muke gudanar da wannan kyautar da aka bayar hannu sake. Gama muna iya ƙoƙari mu yi abin da yake daidai, ba a gaban Ubangiji kaɗai ba, amma a gaban mutane ma. (2 Korintiyawa 8:18-21)
Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawulu. (Ayyukan Manzanni 11:30)
In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima. In kuma ya dace in tafi, to, sai su tafi tare da ni. (1 Korintiyawa 16:3-4)

Misalan rashin neman lissafi

Ba su bukaci wani bayani daga waɗanda aka ba wa kuɗin don su biya ma’aikatan ba, domin sun yi aikinsu da aminci. (2 Sarakuna 12:15)
Amma ba sa bukata su ba da bayanin kuɗin da aka danƙa musu domin suna aikinsu da aminci.” (2 Sarakuna 22:7)

Inda za a bayar

Iyali

In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni. (1 Timoti 5:8)

Iyaye

Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’ Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’ ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku. (Mattiyu 15:4-6)
Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku! Gama Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma, ‘Duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.’ Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,’ (wato, abin da aka keɓe wa Allah), sa’an nan haka ba kwa ƙara barinsa yă yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu. Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin al’adun da kuke miƙa wa ’ya’yanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa.” (Markus 7:9-13)

Gwauraye

Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah. (1 Timoti 5:4)
In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata tă taimake su, kada tă bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi. (1 Timoti 5:16)

Misalin bayarwa ga iyali

Zan tanada maka a nan, domin akwai saura shekaru biyar na yunwa masu zuwa. In ba haka ba, kai da gidanka da dukan mallakarka za ku zama gajiyayyu.’ (Farawa 45:11)
Yusuf ya kuma tanada wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa da dukan gidan mahaifinsa, abinci bisa ga yawan ’ya’yansu. (Farawa 47:12)

Misalin bayarwa ga iyali

Sauran hadaya ta garin zai zama na Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta. (Firistoci 2:3)
Zai kuma kawo ɗaya daga kowace a matsayin hadaya, baiko ne ga Ubangiji. Wannan zai zama na firist da ya yafa jinin hadaya ta salama ne. (Firistoci 7:14)
Za ku ba da cinya ta dama ta hadaya don zumuncinku ga firist a matsayin baiko. Ɗan Haruna da ya miƙa jini da kitsen hadaya ta salama, zai ɗauki cinyar tă zama rabonsa. Daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa, na ɗauki ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka miƙa, na ba da su ga Haruna firist da kuma ’ya’yansa maza a matsayin rabonsu na kullum daga Isra’ilawa.’ ” (Firistoci 7:32-34)
Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza da suka ragu, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji ku ci ba tare da yisti ba, a gefen bagaden, gama tsattsarka ne. Ku ci shi a tsattsarkan wuri, gama rabonka ne da na ’ya’yanka daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji; gama haka aka umarce ni. Amma kai da ’ya’yanka maza da mata za su iya ci ƙirjin da aka kaɗa, da kuma cinyar da aka miƙa. Ku ci su a wuri mai tsabta; an ba da su gare ku da kuma ’ya’yanku a matsayin rabo daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa. (Firistoci 10:12-14)
Amma in mutumin da aka yi wa laifin ba shi da ɗan’uwa na kusa da za a biya diyya saboda laifin, sai diyyar tă zama ta Ubangiji, dole kuma a ba wa firist, haɗe da ragon da za a yi kafara da shi. Dukan tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka kawo wa firist za su zama nasa. Kowace tsarkakakkiyar kyauta da mutum ya kawo nasa ne, sai dai abin da ya ba wa firist, zai zama na firist.’ ” (Ƙidaya 5:8-10)
Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayun da za a miƙa mini, dukan tsarkakan hadayun da Isra’ilawa suka ba ni, na ba ka su su zama rabonka da na ’ya’yanka har abada. Kai za ka riƙe sashe mafi tsarki na hadayun da suka ragu daga wuta. Daga dukan kyautai mafi tsarki na hadayun da suka miƙa mini, ko ta gari, ko don zunubi, ko kuma don laifi, wannan kashi naka ne da ’ya’yanka. Ku ci shi a matsayin abu mafi tsarki; kowane namiji zai ci. Dole ku ɗauke shi da tsarki. “Har yanzu kuma duk abin da aka keɓe daga kyautai na dukan hadayun kaɗawa na Isra’ilawa naka ne. Na ba da wannan gare ka da ’ya’yanka maza da mata, a kowane lokaci. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci. “Na ba ka duk man zaitun mafi kyau, da ruwan inabi mafi kyau duka, da hatsi mafi kyau duka na nunan farinsu da suke bayarwa ga Ubangiji. Dukan nunan fari na ƙasar da suke kawo wa Ubangiji, zai zama naka. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci. “Kome a Isra’ila da aka keɓe wa Ubangiji, zai zama naka. Kowane haihuwar fari, ta mutum, ko ta dabba da suka miƙa wa Ubangiji, naka ne. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram. Sa’ad da suke wata ɗaya da haihuwa, dole a fanshe su a bakin shekel biyar-biyar, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri da ake amfani da shi, wanda nauyinsa ya kai gera ashirin. “Amma kada ka fanshe ɗan fari na saniya, tunkiya, ko akuya; gama suna da tsarki. Ka yayyafa jininsu a bisan bagade, ka kuma ƙone kitsensu kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Namansu zai zama naka, haka ma ƙirji na kaɗawa da cinyar dama za su zama naka. Kome da aka keɓe daga tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da ’ya’yanka maza da mata a matsayin zaunannen rabo. Wannan madawwamin alkawarin gishiri ne a gaban Ubangiji dominka da zuriyarka.” (Ƙidaya 18:8-19)
Daga sojojin da suka je yaƙin kuwa, ka ware ganima wa Ubangiji, ka ɗauki ɗaya daga cikin mutum ɗari biyar, da shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, da tumaki ɗari biyar. Ka ɗauki wannan sashe daga rabin rabonsu ka ba wa Eleyazar firist, a matsayin sashe na Ubangiji. Daga cikin rabin rabon Isra’ilawa, ka zaɓi ɗaya daga kowane hamsin na mutane, shanu, jakuna, tumaki, awaki ko kuma sauran dabbobi. Ka ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.” (Ƙidaya 31:28-30)
To, ga rabon da jama’a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa ta bijimi ne, ko ta tunkiya ce; sai su ba firistoci kafaɗar, kumatun, da kuma kayan cikin. Za ku ba su nunan fari na hatsinku, da sabon ruwan inabinku, da manku, da kuma gashi na fari daga askin da kuka yi na tumakinku. (Maimaitawar Shari’a 18:3-4)
Kada ku yi wa saniya takunkumi sa’ad da take tattaka hatsi. (Maimaitawar Shari’a 25:4)
“Mun kuma ɗauka hakkin kawo nunan fari na hatsinmu da kuma na kowane itace mai ba da ’ya’ya a gidan Ubangiji kowace shekara. “Kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka, za mu kawo ɗan fari na ’ya’yanmu maza da na garken shanunmu, da na tumakinmu, da kuma na awakinmu a gidan Allahnmu, don firistocin da suke aikin a can. (Nehemiya 10:35-36)
Saboda haka a kwanakin Zerubbabel da Nehemiya, dukan Isra’ila suka ba da sashe na kowace rana domin mawaƙa da matsaran ƙofofi. Suka kuma keɓe sashe don sauran Lawiyawa, Lawiyawan kuma suka keɓe sashe don zuriyar Haruna. (Nehemiya 12:47)
Za su ci hadaya ta gari, hadaya don zunubi da hadaya don laifi; da kuma kowane keɓaɓɓen abu a Isra’ila da za a ba wa Ubangiji zai zama nasu. Mafi kyau na nunan farinku da kuma dukan kyautanku na musamman za su zama na firistoci. Za ku ba su rabo na fari na ɓarzajjen hatsinku saboda albarka ta kasance a gidanku. (Ezekiyel 44:29-30)

Ma’aikatan Sabon Alkawari

“Kada ku riƙe wata zinariya ko azurfa ko jan ƙarfe a aljihunanku, kada ku ɗauki jaka don tafiya, ko ƙarin riga, ko takalma ko sanda; domin ma’aikaci ya cancanci hakkinsa. (Mattiyu 10:9-10)
Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku. (Markus 6:8)
Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka. Ya kuma aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya. Ya ce musu, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, wato, ba sanda, ba jaka, ba burodi, ba kuɗi, ba riga na biyu. (Luka 9:1-3)
Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum saba’in da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga. Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya. “Sa’ad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’ In akwai mutum mai salama a gidan, salamarku za tă kasance tare da shi, in kuwa babu, salamarku za tă koma muku. Ku zauna a wannan gidan, kuna ci kuna shan duk abin da suka ba ku, gama ma’aikaci ya cancanci albashinsa. Kada ku yi yawan sāke masauƙi, daga gida zuwa gida. (Luka 10:1, 4-7)
Duk haka, wanda aka koya wa maganar Kiristi, bari yă raba abubuwan nan na alheri tare da wanda ya koyar da shi. (Galatiyawa 6:6)
Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa. Gama Nassi ya ce, “Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi,” da kuma, “Ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.” (1 Timoti 5:17-18)
Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka taimaki Zenas lauyan nan da Afollos a hanyarsu ka kuma tabbata ba su rasa kome ba. (Titus 3:13)
Abokina ƙaunatacce, kana da aminci cikin abin da kake yi wa ’yan’uwa, ko da yake su baƙi ne a gare ka. Sun faɗa wa ikkilisiya game da ƙaunarka. Za ka kyauta in ka sallame su a hanyar da ta cancanci Allah. Saboda Sunan nan ne suka fito, ba sa karɓan wani taimako daga waɗanda ba masu bi ba. Saboda haka ya kamata mu nuna halin karɓan baƙi ga irin mutanen nan domin mu yi aiki tare saboda gaskiyan nan. (3 Yohanna 1:5-8)

An tallafa wa Yesu da kyautai a lokacin hidimarsa a duniya

Da Yowanna matar Kuza, manajan iyalin Hiridus; da Suzana; da waɗansu mata da yawa. Waɗannan mata suna taimaka musu cikin hidima, daga cikin abin da suke da shi na zaman gari. (Luka 8:3)

Ma’aikatan Kirista da ba su yi amfani da ’yancinsu na samun tallafi ba

Ko ni da Barnabas ne kawai ba mu da ’yanci a ɗauke mana aikin ci da kai? Wa yake ciyar da kansa yayinda yake aikin soja? Wa yake shukar gonar inabi, da ba ya cin amfaninta? Wa yake kiwon garke, da ba ya sha madararsa? Ina faɗin wannan bisa ga ra’ayin mutum kawai ne? Ashe, Doka ma ba tă faɗa haka ba? Gama yana a rubuce a cikin Dokar Musa cewa, “Kada ka sa wa saniya takunkumi sa’ad da yake sussukar hatsi.” Kuna tsammani a kan shanu ne Allah ya damu sa’ad da ya ce haka? Babu shakka, ya yi maganan nan saboda mu ne. Ko ba haka ba? I, an rubuta wannan saboda mu ne, domin sa’ad da mai noma yake noma, mai sussuka kuma yana sussuka, suna wannan ne da bege za su sami rabonsu daga girbin. In muka shuka iri na ruhaniya a cikinku, ashe, bai kamata mu yi girbin abin biyan bukatarmu daga gare ku ba? In waɗansu suna samun wannan taimako daga gare ku, ashe, mu ba mu fi cancanta mu samu ba? Amma ba mu yi amfani da wannan ’yancin ba. A maimakon haka, mun jure da kome, domin kada mu hana bisharar Kiristi yaɗuwa. Ashe, ba ku san cewa waɗanda suke hidima a haikali suna samun abincinsu daga haikali ba ne, waɗanda kuma suke hidima a bagade suna samun rabo a hadayar da suka miƙa ba ne? Haka ma Ubangiji ya umarta cewa ya kamata waɗanda suke wa’azin bishara, su sami abin biyan bukatarsu daga bisharar. Amma ban yi amfani da ko ɗaya daga cikin waɗannan ’yancin ba. Ba kuma ina rubuta muku wannan da fata za ku yi mini waɗannan abubuwa ba ne. Gwamma in mutu, da wani yă hana ni wannan abin taƙama. (1 Korintiyawa 9:6-15)
In na yi wa’azi da yardar rai, ina da lada; in ba da yardar rai ba, ina dai cika amana da aka danƙa mini ne. To, mene ne ladana? Ladana kaɗai shi ne, in yi wa’azin bishara, in kuma yi shi a kyauta, yadda ba zan yi amfani da ’yancina cikin wa’azin ba. (1 Korintiyawa 9:17-18)
Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku wa’azin bisharar Allah kyauta? Na yi wa waɗansu ikkilisiyoyi ƙwace ta wurin karɓar taimako daga wurinsu, domin in yi muku hidima. Sa’ad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama ’yan’uwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka. (2 Korintiyawa 11:7-9)
Yanzu a shirye nake in ziyarce ku sau na uku, ba zan kuma nawaita muku ba, don ba kayanku nake so ba, ku nake so. Gama ba yara ne da ɗaukar nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukar nauyin yaran. Don haka ina farin ciki in kashe dukan abin da nake da shi a kanku, har in ba da kaina ma dominku. In na ƙaunace ku fiye da haka, za ku rage ƙaunarku gare ni ne? To, shi ke nan, ban nawaita muku ba. Ashe, sai ku ce dabara na yi muku, na shawo kanku ta hanyar yaudara! Na cuce ku ne ta wurin wani daga cikin waɗanda na aiko a gare ku? Na roƙi Titus ya zo wurinku. Na kuma aiki ɗan’uwanmu tare da shi. Ko Titus ya cuce ku ne? Ba ruhu ɗaya yake bi da mu ba? Ba kuma hanya guda muka bi ba? (2 Korintiyawa 12:14-18)
Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu. Ba shakka kuna iya tunawa, ’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah. (1 Tessalonikawa 2:5, 9)
...ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku. Mun yi wannan, ba don ba mu da ’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi. (2 Tessalonikawa 3:8-9)

Kada ma’aikatan Kirista su yi hidima da mugun nufi na kuɗi

Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗan’uwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana. Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula, ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima; (1 Bitrus 5:1-2)

Mutane da yawa suna ƙoƙarin samun kuɗi ta wurin nuna kamar masu ibada ne

Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah. (2 Korintiyawa 2:17)
Gama akwai ’yan tawaye da yawa, masu surutun banza da masu ruɗi, musamman ƙungiyar masu kaciya. Dole a hana su yin magana, domin suna kawo rushewar iyalai ta wurin koyar da abubuwan da bai kamata su koyar ba don neman ƙazamar riba. (Titus 1:10-11)
Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya. Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci. (2 Bitrus 2:1, 3)

An gargaɗi almajirai su shirya

Sai Yesu ya tambaye, su ya ce, “Lokacin da na aike ku ba tare da jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma ba, kun rasa wani abu?” Suka amsa, “Babu.” Ya ce musu, “Amma yanzu, in kuna da jakar kuɗi, ko jaka, ku ɗauka. In kuma ba ku da takobi, ku sayar da rigarku, ku saya. (Luka 22:35-36)

Wuri Mai Tsarki / haikali

Gina Wuri Mai Tsarki

“Ga iri jerin kayan da za ka karɓo daga hannunsu, “zinariya, da azurfa, tagulla, shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin, da gashin akuya, fatun ragunan da aka wanke, fatun awaki masu kyau, itacen akashiya, mai domin fitila, kayan yaji domin man keɓewa da kuma turare mai ƙanshi, da duwatsun Onis, da duwatsun da za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. “Sa’an nan ka sa su yi mini wuri mai tsarki, domin in zauna a cikinsu. (Fitowa 25:3-8)

Sun bayar fiye da abin da ake bukata

Suka karɓa daga wurin Musa dukan kyautai da Isra’ilawa suka kawo don su yi aikin shirya wuri mai tsarki. Mutane suka ci gaba da kawo kyautai yardar rai kowace safiya. Sai dukan masu fasaha waɗanda suke aikin wuri mai tsarki suka ɗan dakata suka ce wa Musa, “Mutane suna kawo fiye da abin da ake bukata domin aikin da Ubangiji ya umarta a yi.” Sai Musa ya ba da umarni, suka aika ko’ina a cikin sansani cewa, “Kada namiji ko ta mace yă sāke kawo kyauta don wuri mai tsarki.” Ta haka mutane suka daina kawowa. Saboda abin da suke da shi ya fi abin da ake bukata domin aikin. (Fitowa 36:3-7)

Gina haikali

Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim. Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali, talenti dubu uku na zinariya (zinariyar Ofir) da tacecciyar azurfa dubu bakwai; don adon bangon gine-ginen, don aikin zinariya da kuma aikin azurfa, don kuma dukan aikin da gwanaye za su yi. Yanzu fa wa yake da niyya yă miƙa kansa a yau don Ubangiji?” Sai shugabannin iyalai, shugabannin kabilan Isra’ila, manyan hafsoshin mayaƙa dubu-dubu da manyan hafsoshi mayaƙa ɗari-ɗari, da shugabannin lura da ayyukan sarki suka yi bayarwa da yardar rai. Suka bayar talenti dubu biyar na zinariya, talenti dubu goma na azurfa, talenti dubu goma sha takwas na tagulla da talenti dubu ɗari na ƙarfe don aiki a haikalin Allah. Duk waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka ba da su ga Yehiyel mutumin Gershon ma’ajin haikalin Ubangiji. (1 Tarihi 29:2-8)

Haikalin ya ci kuɗi mai yawa

Bisa ga umarnin sarki sai suka cire manyan duwatsu masu kyau don a tanada tushen duwatsun da aka gyara domin haikalin daga wurin haƙar duwatsun. (1 Sarakuna 5:17)

Gyaran haikali

Yowash ya ce wa firistoci, “Ku tattara dukan kuɗin da ake kawo a matsayin hadayu masu tsarki na haikalin Ubangiji, kuɗin da aka tattara a ƙidaya, kuɗin da aka tattara daga wa’adin da mutum ya yi, da kuma kuɗin da aka kawo na yardan rai a haikali. Bari kowane firist yă karɓi kuɗi daga masu ajiya, sa’an nan a yi amfani da su a gyara duk wani abin da ya lalace a haikali.” Amma har zuwa shekara ta ashirin da uku ta mulkin Yowash, firistocin ba su yi gyara haikalin ba. Saboda haka Sarki Yowash ya kira Yehohiyada firist da sauran firistoci ya tambaye su ya ce, “Me ya sa ba kwa gyaran abubuwan da suka lalace a haikali? Kada ku sāke karɓan kuɗi daga masu ajiya, amma a miƙa su domin gyaran haikali.” Firistoci suka yarda cewa ba za su sāke karɓan kuɗi daga mutane ba, kuma ba za su yi gyaran haikalin da kansu ba. Yehohiyada firist ya ɗauki akwatin ya huda rami a murfinsa. Ya ajiye shi kusa da bagade a hannun dama na haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka zuba dukan kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji a cikin akwatin. Duk sa’ad da suka ga kuɗin sun ƙaru a akwatin, sai marubucin fada da babban firist, su ƙirga kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji su sa a jakankuna. Sa’ad da suka ga kuɗin ya yi yawa, sai su ba wa waɗanda aka zaɓa su lura da aikin haikalin. Da shi suka biya waɗanda suka yi aiki a haikalin Ubangiji, su kafintoci, da magina, (2 Sarakuna 12:4-11)
“Ka haura zuwa wurin Hilkiya babban firist ka sa yă shirya kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tara daga mutane. Ka sa su danƙa su a hannun waɗanda aka zaɓa don biyan ma’aikatan da suka yi gyara a haikalin Ubangiji, wato, kafintoci, da magina, da masu tsara gini. Ka kuma sa su sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu don a gyara haikalin. (2 Sarakuna 22:4-6)
Wani lokaci daga baya Yowash ya yanke shawara yă gyara haikalin Ubangiji. Ya tara firistoci da Lawiyawa wuri ɗaya ya ce musu, “Ku je garuruwan Yahuda ku karɓa kuɗin da ya kamata a biya shekara-shekara daga dukan Isra’ila, don gyaran haikalin Allahnku. Ku yi haka yanzu.” Amma Lawiyawa ba su yi haka nan da nan ba. Saboda haka sarki ya kira Yehohiyada babban firist ya ce masa, “Me ya sa ba ka bukaci Lawiyawa su kawo harajin da Musa bawan Ubangiji ya ce a biya daga Yahuda da Urushalima da kuma taron Isra’ila domin Tentin Sujada Shaida ba?” Yanzu ’ya’ya muguwar macen nan Ataliya maza sun fasa zuwa cikin haikalin Allah, suka kuma yi amfani da kayayyaki masu tsarki ma wa Ba’al. Bisa ga umarnin sarki, aka yi akwati aka sa a waje, a mashigin haikalin Ubangiji. Aka yi umarni a Yahuda da Urushalima cewa ya kamata suka kawo wa Ubangiji harajin da Musa bawan Allah ya bukaci daga Isra’ila a hamada. Dukan hafsoshi da dukan mutane suka kawo nasu kuɗin da aka sa musu da farin ciki, suna zuba su cikin akwatin sai da ya cika. Duk sa’ad da Lawiyawa suka fito da akwatin zuwa ga hafsoshin sarki, suka kuma ga cewa akwatin yana da kuɗi mai yawa, sai magatakardan fada da hafsan babban firist su zo su juya kuɗin daga akwatin su mai da shi wurinsa. Sun riƙa yin haka kullum suka tara kuɗi mai yawa. Sarki da Yehohiyada suka ba da shi ga mutanen da suka yi aikin da ake bukata don haikalin Ubangiji. Suka ɗauki masu gini da kafintoci don su gyara haikalin Ubangiji, da kuma ma’aikatan ƙarafa da tagulla don su gyara haikalin. Mutanen da suke lura da aikin natsattsu ne, kuma gyare-gyaren suka ci gaba a ƙarƙashinsu. Suka sāke gina haikalin Allah bisa ga ainihin fasalinsa suka ƙara masa ƙarfi. (2 Tarihi 24:4-13)
A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya, ya tsarkake ƙasar da haikalin, ya aiki Shafan ɗan Azaliya da Ma’asehiya mai mulkin birni, tare da Yowa ɗan Yowahaz, marubuci, su gyara haikalin Ubangiji Allah. Suka tafi wurin Hilkiya babban firist suka ba shi kuɗin da aka kawo cikin haikalin Allah, wanda Lawiyawa masu tsaron ƙofofi sun tattara daga mutanen Manasse, Efraim da dukan raguwar Isra’ila da kuma daga dukan mutanen Yahuda da Benyamin da kuma mazaunan Urushalima. Sa’an nan suka danƙa su ga mutanen da aka naɗa su lura da aiki a kan haikalin Ubangiji. Waɗannan mutane ne suke biyan ma’aikatan da suka gyara suka kuma mai da haikalin. Suka kuma ba da kuɗi ga kafintoci da magina don su sayi sassaƙaƙƙun duwatsu, da katakai don yin tsaiko da tankar ginin da sarakunan Yahuda suka bari yă fāɗi ya zama kango. (2 Tarihi 34:8-11)

Sake gina haikali

Sa’ad da suka isa haikalin Ubangiji a Urushalima, sai waɗansu shugabannin iyalai suka yi bayarwar yardar rai ta gudummawarsu domin sāke gina gidan Allah a wurin da yake. Bisa ga ƙarfinsu suka bayar da darik 61,000 na zinariya, da maina 5,000 na azurfa, da rigunan firistoci guda 100. (Ezra 2:68-69)
Za a jera manyan duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katako. Daga asusun sarki kuma za a biya kuɗin aikin. (Ezra 6:4)
Na kuma ba da umarni game da abin da za ku yi wa dattawan Yahudawa cikin aikin ginin wannan gidan Allah. Daga asusun sarki a kuɗin da yake shigo wa Kewayen Kogin Yuferites za a biya mutanen nan duka, domin kada aikin yă tsaya. (Ezra 6:8)

Kula da haikali

“Mun yi alkawari ba za mu ba da ’ya’yanmu mata aure ga mutanen da suke kewaye da mu ba, ba kuwa za mu auri ’ya’yansu mata wa ’ya’yanmu maza ba. Mutanen Isra’ila haɗe da Lawiyawa, za su kawo sadakokinsu na hatsi, sabon ruwan inabi da mai a ɗakunan ajiya inda ake ajiyar kayayyakin wuri mai tsarki da kuma inda firistoci, matsaran ƙofofi da kuma mawaƙa suke zama. “Ba za mu ƙyale gidan Allahnmu ba.” (Nehemiya 10:30, 39)

Rukunoni dabam-dabam

Waɗanda suke roƙon kyauta

Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka. (Mattiyu 5:42)
Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka. (Luka 6:30)

Dukan mutane, musamman masu bi

Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi. (Galatiyawa 6:10)
Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta ’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa. (Romawa 12:10)
Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi. (Romawa 12:13)

Abokan gāba

In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ba shi abinci ya ci; in yana jin ƙishi, ka ba shi ruwa ya sha. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta mai ci a kansa, Ubangiji kuma zai sāka maka. (Karin Magana 25:21-22)
A maimakon haka, “In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi; in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.” (Romawa 12:20)

Kada ka ba wa mai kisan kai

Mutumin da laifin kisa ya yi ta damunsa zai zama mai gudu don tsoro har mutuwa; kada wani ya taimake shi. (Karin Magana 28:17)

Bayarwa ga matalauta

Umarnin Allah da ra’ayinsa game da bayarwa ga matalauta

Kullum za ku kasance da matalauta a ƙasar. Saboda haka na umarce ku ku bayar hannu sake ga ’yan’uwa da kuma matalauta, da masu bukata a ƙasarku. (Maimaitawar Shari’a 15:11)
Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan, amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne. (Karin Magana 14:31)
Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne, zai kuwa sami lada game da abin da ya yi. (Karin Magana 19:17)
“Irin azumin da na zaɓa shi ne, a kunce sarƙoƙin rashin adalci a kuma kunce igiyoyin karkiya, a ’yantar da waɗanda ake zalunta a kuma kakkarye kowace karkiya? Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli, sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura, kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya? Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan; sa’an nan adalcinku zai tafi a gabanku, ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya. Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa; za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan. “In kuka kawar da karkiyar zalunci, kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu, in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani, sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu darenku kuma zai zama kamar tsakar rana. (Ishaya 58:6-10)
“ ‘To, fa, ga zunubin ’yar’uwarki Sodom. Ita da ’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba. (Ezekiyel 16:49)

Tanadin Tsohon Alkawari domin matalauta

Dokokin girbi da kalar hatsi

“Shekara shida za ku nome gonakinku ku girbe amfanin gonar, amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun. (Fitowa 23:10-11)
“ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku. Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku. (Firistoci 19:9-10)
“ ‘Sa’ad da kuka yi girbin gonarku, kada ku girbe har ƙarshen gefen gonar, ko ku yi kalar girbinku. Ku bar su wa matalauta da baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ” (Firistoci 23:22)
Sa’ad da kuke girbi a gonarku, sai kuka manta da dami, kada ku koma don ku ɗauka. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa, saboda Ubangiji Allahnku yă albarkace ku a cikin dukan aikin hannuwanku. Sa’ad da kuka kakkaɓe ’ya’yan zaitun daga itatuwanku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa. Sa’ad da kuka yi girbin inabi a gonar inabinku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa. (Maimaitawar Shari’a 24:19-21)

Alhakin biyan bukatu ba tare da iyaka ba

In akwai matalauci a cikin ’yan’uwanku, a duk wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku taurara zuciya, ko ku ƙi saki hannu ga ɗan’uwanku matalauci. A maimakon haka ku bayar hannu sake, ku kuma ba shi bashi gwargwadon abin da yake bukata a sauƙaƙe. Ku yi hankali kada ku riƙe wannan mugun tunani cewa, “Shekara ta bakwai, shekarar yafewar basusuwa, ta yi kusa,” har ku nuna mugun nufi ga ɗan’uwa mabukaci, ku ƙi ba shi wani abu. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku. Ku bayar hannu sake gare shi, ku kuma yi haka ba tare da gunaguni ba; saboda wannan fa Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan aikinku, da kuma kome da kuka sa hannunku a kai. (Maimaitawar Shari’a 15:7-10)

Bikin Purim

...a matsayin lokacin da Yahudawa suka sami huta daga abokan gābansu, da kuma a matsayin watan da aka mai da baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama ranar biki. Ya rubuta musu su kiyaye ranakun a matsayin ranakun biki da na farin ciki. Su kuma ba da kyautai na abinci ga juna, da kuma kyautai ga matalauta. (Esta 9:22)

Shekarar Murna

Ku keɓe shekara ta hamsin ku kuma yi shelar ’yanci a dukan ƙasar ga mazaunanta. Za tă zama shekarar murna gare ku; kowannenku zai koma ga mallakar iyalinsa, kuma kowa ga danginsa. (Firistoci 25:10)

Misalan bayarwa ga matalauta

...domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako, da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su. Mutumin da yake bakin mutuwa ya sa mini albarka. Na faranta wa gwauruwa zuciya. Na yafa adalci ya zama suturata; gaskiya ita ce rigata da rawanina. Ni ne idon makafi kuma ƙafa ga guragu. Ni mahaifi ne ga masu bukata; na tsaya wa baƙo. (Ayuba 29:12-16)
“In na hana wa matalauta abin da suke so, ko kuma in sa idanun gwauruwa su yi nauyi don kuka, in na ajiye burodina don kaina kaɗai, ban kuwa ba wa marayu abinci sa’ad da suke jin yunwa, amma tun suna tasowa na lura da su, kamar yadda mahaifi zai lura da ɗa, kuma tun da aka haife ni ina lura da gwauruwa. In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura, ko wani mai bukata da ba shi da riga, kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba don na yi masa sutura da gashin tumakina, in na ɗaga hannuna don in cuci maraya, domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a, bari hannuna yă guntule daga kafaɗata, bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi. Gama ina jin tsoron hallaka daga Allah, kuma domin tsoron ɗaukakarsa ba zan iya yin waɗannan abubuwa ba. (Ayuba 31:16-23)

Shugaba mai adalci

Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece ’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya. (Zabura 72:4)
Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako. Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa. (Zabura 72:12-13)

Mace mai kirki

Wa yake iya samun mace mai halin kirki? Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai. Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata. (Karin Magana 31:10, 20)

Sabon Alkawari

Yohanna Mai Baftisma

Sai taron suka tambaye shi, suka ce “Me za mu yi ke nan?” Ya amsa ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yă yi haka.” (Luka 3:10-11)

Yesu Kiristi ya ɗauki kansa ɗaya da matalauta

“Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama. Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki. Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa. “Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya. Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni, da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’ “Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha? Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura? Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’ “Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’ “Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa. Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba, da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’ “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’ “Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’ (Mattiyu 25:31-45)

Yesu ya nuna misalin bayarwa ga matalauta

Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi. Sai Yesu ya ce masa, “Abin nan da kake niyyar yi, ka yi shi maza.” Amma ba wani a wurin cin abincin da ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. Da yake Yahuda ne ma’aji, waɗansunsu suka ɗauka Yesu yana ce masa yă sayi abin da ake bukata don Bikin ne, ko kuwa yă ba wa matalauta wani abu. (Yohanna 13:27-29)

Wanda dā marar gaskiya ne ya bayar ga matalauta

Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata. (Afisawa 4:28)

Wasu misalai

Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare. Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa. (Ayyukan Manzanni 2:44-45)
Ɗaya daga cikinsu mai suna Agabus, ya miƙe tsaye ya yi annabci ta wurin Ruhu cewa za a yi yunwa mai tsanani wadda za tă bazu a dukan duniyar Romawa (Wannan ya faru a zamanin mulkin Kalaudiyus.) Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudummawa ga ’yan’uwan da suke zama a Yahudiya. Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawulu. (Ayyukan Manzanni 11:28-30)
Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ” (Ayyukan Manzanni 20:35)
Gama Makidoniya da Akayya sun ji daɗin yin gudummawa domin matalautan da suke cikin tsarkakan da suke a Urushalima. Sun kuwa ji daɗin yin haka, gama ya zama kamar bashi ne a gare su. Da yake Al’ummai sun sami rabo cikin albarkun ruhaniyar Yahudawa, ya zama musu kamar bashi su ma su taimaki Yahudawa da albarkunsu na kayan duniya. (Romawa 15:26-27)
Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi. (Galatiyawa 2:10)

Albarka da la’ana

Albarkar bayarwa ga matalauta

Albarkar sanin Ubangiji

Ya kāre muradin matalauta da mabukata, ta haka kome ya tafi masa daidai. Ba abin da ake nufi da ba san ni ke nan ba?” In ji Ubangiji. (Irmiya 22:16)

Albarkar rai

Ba ya cin zalin wani, amma yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa. Ba ya yi fashi amma yakan ba wa mayunwata abinci ya kuma tanada wa marasa tufafi riga. (Ezekiyel 18:7)
Yana bin ƙa’idodina yana kuma kiyaye dokokina da aminci. Wannan mutumin adali ne; tabbatacce zai rayu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. (Ezekiyel 18:9)
Bai ci zalin wani ko ya karɓi jingina ba. Ba ya fashi amma yakan ba da abincinsa ga mayunwata ya tanada tufafi wa marasa tufafi. Yakan janye hannunsa daga zunubi ba ya kuma ba da bashi da ruwa ko karɓan riba da yawa. Yakan kiyaye dokokina ya kuma bi ƙa’idodina. Ba zai mutu saboda zunubin mahaifinsa ba; tabbatacce zai rayu. (Ezekiyel 18:16-17)

Albarka a kan iyali

’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar; tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka. Ya rarraba kyautansa ga matalauta, adalcinsa zai dawwama har abada; za a ɗaga ƙahonsa sama da bangirma. (Zabura 112:2, 9)

Albarkar biyan bukatu

Duk wanda yake bayarwa ga matalauta ba zai rasa kome ba, amma duk wanda bai kula da su ba yana samu la’ana masu yawa. (Karin Magana 28:27)

Albarkar lafiya

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala. Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa; zai albarkace shi a cikin ƙasar ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba. Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi. (Zabura 41:1-3)

Albarkar amsar addu’a da shiriya

“Irin azumin da na zaɓa shi ne, a kunce sarƙoƙin rashin adalci a kuma kunce igiyoyin karkiya, a ’yantar da waɗanda ake zalunta a kuma kakkarye kowace karkiya? Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli, sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura, kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya? Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan; sa’an nan adalcinku zai tafi a gabanku, ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya. Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa; za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan. “In kuka kawar da karkiyar zalunci, kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu, in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani, sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu darenku kuma zai zama kamar tsakar rana. Ubangiji zai bishe ku kullum; zai biya muku bukatunku a ƙasa mai zafin rana ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku. Za ku zama kamar lambun da aka yi masa banruwa, kamar rafin da ruwansa ba ya ƙafewa. (Ishaya 58:6-11)

Albarkar kuɓuta da kāriya

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala. Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa; zai albarkace shi a cikin ƙasar ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba. (Zabura 41:1-2)

Albarkar daraja

Ya rarraba kyautansa ga matalauta, adalcinsa zai dawwama har abada; za a ɗaga ƙahonsa sama da bangirma. (Zabura 112:9)

Albarka a kan aiki da ta arziki

Ku bayar hannu sake gare shi, ku kuma yi haka ba tare da gunaguni ba; saboda wannan fa Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan aikinku, da kuma kome da kuka sa hannunku a kai. (Maimaitawar Shari’a 15:10)
Sa’ad da kuke girbi a gonarku, sai kuka manta da dami, kada ku koma don ku ɗauka. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa, saboda Ubangiji Allahnku yă albarkace ku a cikin dukan aikin hannuwanku. (Maimaitawar Shari’a 24:19)
Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece ’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya. (Zabura 72:4)
Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako. Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa. Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa. Bari yă yi doguwar rayuwa! Bari a ba shi zinariya daga Sheba. Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa su kuma albarkace shi dukan yini. (Zabura 72:12-15)
Wadata da arziki suna a cikin gidansa, adalcinsa zai dawwama har abada. (Zabura 112:3)
Ya rarraba kyautansa ga matalauta, adalcinsa zai dawwama har abada; za a ɗaga ƙahonsa sama da bangirma. (Zabura 112:9)
Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne, zai kuwa sami lada game da abin da ya yi. (Karin Magana 19:17)
Duk wanda ya tara dukiyarsa ta wurin ba da bashi da ruwan da ya wuce misali yana tara wa wani ne wanda zai yi wa talakawa alheri. (Karin Magana 28:8)
Saboda haka, ya sarki, ina roƙonka ka karɓi shawarar da zan ba ka; ka furta zunubanka ta wurin yin abin da yake daidai. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulaƙantawa, wataƙila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.” (Daniyel 4:27)

Albarkar yalwar ruhaniya

Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka taimaki Zenas lauyan nan da Afollos a hanyarsu ka kuma tabbata ba su rasa kome ba. Dole mutanenmu su koyi ba da kansu ga aikata abin da yake nagari, domin su iya biyan bukatunsu na yau da kullum kada kuma su yi rayuwar marar amfani. (Titus 3:13-14)

Albarka gaba ɗaya

Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka, gama yakan raba abincinsa da matalauta. (Karin Magana 22:9)

Albarkar farin ciki

Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi, amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata. (Karin Magana 14:21)

La’ana ga waɗanda ba sa bayarwa ga matalauta

La’anar addu’ar da ba a amsa ba

In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci, shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba. (Karin Magana 21:13)

La’anar talauci

Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta. (Karin Magana 22:16)

La’ana gaba ɗaya

Duk wanda yake bayarwa ga matalauta ba zai rasa kome ba, amma duk wanda bai kula da su ba yana samu la’ana masu yawa. (Karin Magana 28:27)

Batutuwa dabam-dabam na bayarwa ga matalauta

Halin tausayi

Ashe ban yi kuka domin waɗanda suke cikin damuwa ba? Ko zuciyata ba tă yi baƙin ciki domin matalauta ba? (Ayuba 30:25)

Ka bincika bukatun matalauta

Ni mahaifi ne ga masu bukata; na tsaya wa baƙo. (Ayuba 29:16)

An zargi mai ibada da rashin bayarwa ga matalauta

Ba muguntarka ce ta yi yawa ba? Ba zunubanka ne ba iyaka ba? Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci. Ka kori gwauraye hannu wofi, ka kuma karya ƙarfin marayu. (Ayuba 22:5, 7, 9)

Misalin ɗaukaka Allah maimakon bayarwa ga matalauta

Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci. Sa’ad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa! Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.” Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne. Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba. Sa’ad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don jana’izata. Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.” (Mattiyu 26:6-13)
Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa. Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka? Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.” Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta mana. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni. Matalauta dai suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu a duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba. (Markus 14:3-7)
Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi zalla, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren. Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba ya ce, “Don me ba a sayar da turaren nan aka kuma ba da kuɗin ga matalauta ba? Ai, kuɗin ya kai albashin shekara guda.” Ya yi wannan magana ba don ya kula da matalauta ba ne, sai dai don shi ɓarawo ne. Da yake shi ne mai ajiya jakar kuɗin, yakan taimaki kansa da abin da aka sa a ciki. Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta, an nufa ta ajiye wannan turaren don ranar jana’izata. Kullum za ku kasance da matalauta, amma ba kullum za ku kasance tare da ni ba.” (Yohanna 12:3-8)

Ana bukatar kula da gwauraye

A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum. Saboda haka Sha Biyun nan suka tara dukan almajirai wuri ɗaya, suka ce, “Bai zai yi kyau mu bar hidimar maganar Allah don mu shiga hidimar abinci ba. ’Yan’uwa, ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku waɗanda aka sani suna cike da Ruhu da kuma hikima. Mu kuwa za mu danƙa musu wannan aiki (Ayyukan Manzanni 6:1-3)
Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa. (Yaƙub 1:27)

Sakamakon ra’ayin mallaka daidai: babu matalauci

Dukan masu bi kuwa zuciyarsu ɗaya ne, nufinsu kuwa ɗaya. Babu wani da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, amma sun raba kome da suke da shi. Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka. (Ayyukan Manzanni 4:32-33)

Akwai tanadi domin matalauta su bayar da ƙasa

“ ‘In ba zai iya kawo tunkiyar ba, sai yă kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu ga Ubangiji a matsayin hakki don zunubinsa, ɗaya domin hadaya don zunubi ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. “ ‘In ba zai iya kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu ba, sai yă kawo humushin garwan gari mai laushi domin hadaya don zunubi. Ba lalle ba ne yă sa mai ko turare a kansa, saboda wannan hadaya ce ta zunubi. (Firistoci 5:7, 11)
“ ‘Sa’ad da kwanakin tsabtaccewarta don ɗa namiji ko ’ya ta mace suka cika, sai ta kawo ɗan rago bana ɗaya wa firist a bakin ƙofar Tentin Sujada don hadaya ta ƙonawa da tattabara ko kurciya na hadaya don zunubi. In ba za tă iya kawo ɗan rago ba, sai ta kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, ɗaya domin hadaya ta ƙonawa ɗayan kuma domin hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominta, za tă kuwa zama tsabtacciya.’ ” (Firistoci 12:6, 8)
“In kuwa mutumin matalauci ne ba zai iya samu waɗannan ba, to, dole yă ɗauki ɗan rago guda kamar hadaya don laifi a kaɗa don a yi kafara dominsa, tare da humushin garwa gari mai laushi haɗe da mai don hadaya ta gari, da moɗa na mai, da kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, wanda zai iya samu, ɗaya domin hadaya don zunubi ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. (Firistoci 14:21-22)
Sa’an nan zai miƙa kurciyoyi ko tattabarai, waɗanda mutumin zai iya, ɗaya kamar hadaya don zunubi ɗayan kuma kamar hadaya ta ƙonawa, tare da hadaya ta gari. Ta haka firist zai yi kafara a gaban Ubangiji a madadin wanda za a tsabtacce.” Waɗannan su ne ƙa’idodi domin mutumin da yake da cutar fatar jiki wanda kuma ba zai iya samun abubuwan hadaya ta kullum domin tsabtaccewarsa ba. (Firistoci 14:30-32)
In mai alkawarin matalauci ne da ba zai iya biyan ƙayyadadden abin da aka tsara ba, sai yă tafi wurin firist, shi firist kuma yă duba yadda mutumin da ya yi alkawarin zai iya biya. Sa’an nan mutumin zai biya abin da firist ya faɗa. (Firistoci 27:8)

Iyayen Yesu suna cikin wannan rukuni

Da lokacin tsarkakewarsu bisa ga Dokar Musa ya cika, sai Yusuf da Maryamu suka ɗauke shi suka haura zuwa Urushalima don su miƙa shi ga Ubangiji (yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, “Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji”), don kuma su miƙa hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Dokar Ubangiji cewa, “kurciyoyi biyu ko ’yan tattabarai biyu.” (Luka 2:22-24)

A lokacin ƙidaya mawadata da matalauta sun bayar daidai

“Sa’ad da za ku ƙidaya Isra’ilawa, dole kowanne yă biya domin yă fanshe kansa ga Ubangiji a lokacin da aka ƙidaya shi. Ta haka babu wata annobar da za tă buge su sa’ad da kuke ƙidaya su. Kowannen da ya ƙetare zuwa wurin waɗanda aka riga aka ƙidaya, dole yă ba da rabin shekel, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda nauyinsa garwa ashirin ne. Wannan rabin shekel hadaya ce ga Ubangiji. Duk waɗanda suka ƙetare, waɗanda shekarunsu ya kai ashirin ko fiye, za su ba da hadaya ga Ubangiji. Masu arziki ba za su bayar fiye da rabin shekel ba, talakawa kuma ba za su bayar ƙasa da haka ba, sa’ad da za ku yi hadaya ga Ubangiji don kafara rayukanku. (Fitowa 30:12-15)

Bayarwa ga matalauta na iya zama shaidar ceto

Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.” Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne. (Luka 19:8-9)

Misalan bayarwa dabam-dabam (ba ga Ubangiji ba)

Sa’ad da raƙuman suka gama shan ruwa, mutumin ya fitar da zoben hanci na zinariya mai nauyin giram biyar da woroworo biyu na zinariya masu nauyin shekel goma, ya ba ta. Sa’an nan bawan ya fito da kayan ado na zinariya da azurfa da kayayyaki na tufafi ya ba wa Rebeka; ya kuma ba wa ɗan’uwanta da mahaifiyarta kyautai masu tsada. (Farawa 24:22, 53)
Sa’an nan mahaifinsu Isra’ila ya ce musu, “In dole ne a yi haka, to, sai ku yi. Ku sa waɗansu amfani mafi kyau na ƙasar a buhunanku, ku ɗauka zuwa wurin mutumin a matsayin kyauta, da ɗan man ƙanshi na shafawa, da kuma ’yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta da kuma almon. Ku ɗauki ninki biyu na yawan azurfa tare da ku, gama dole ku mayar da azurfan da aka sa a cikin bakunan buhunanku. Mai yiwuwa an yi haka a kuskure ne. Saboda haka mutanen suka ɗauki kyautar, da kuma kuɗin da ya ninka na farko. Suka kuma ɗauki Benyamin, suka gaggauta suka gangara zuwa Masar suka kuma gabatar da kansu ga Yusuf. (Farawa 43:11-12, 15)
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗi a cikinka ya sa ka a kan kujerar sarautarsa a matsayin sarki don ka yi mulkin domin Ubangiji Allahnka. Saboda ƙaunar Allahnka wa Isra’ila da kuma sha’awarsa na riƙe su har abada, ya naɗa ka sarki a bisansu, don ka yi adalci da kuma gaskiya.” Sa’an nan ta ba sarki talenti 120 na zinariya, kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kasance da irin kayan yaji mai yawa kamar waɗanda sarauniyar Sheba ta ba wa sarki Solomon ba. (2 Tarihi 9:8-9)
Sarki Solomon ya ba sarauniyar Sheba duk abin da take so da kuma ta nema; ya ba ta fiye da abin da ta kawo masa. Sa’an nan ta tashi ta koma ƙasarta tare da masu rufe mata baya. (2 Tarihi 9:12)
Hezekiya sarkin Yahuda ya tanada bijimai dubu ɗaya da tumaki da kuma awaki dubu bakwai wa taron, fadawa kuma suka tanada musu bijimai dubu da kuma tumaki da awaki dubu goma. Firistoci masu yawa suka tsarkake kansu. (2 Tarihi 30:24)
Yawanci mutane suka kawo hadayun ƙonawa zuwa Urushalima wa Ubangiji da kuma kyautai masu daraja wa Hezekiya sarkin Yahuda. Daga lokacin zuwa gaba dukan ƙasashe suka girmama shi. (2 Tarihi 32:23)
Yosiya ya tanada wa dukan mutanen da ba firistoci ba ne waɗanda suke a wurin, tumaki da awaki dubu talatin don a yanka saboda hadayun Bikin Ƙetarewa, ya kuma ba su shanu dubu uku. Dukan dabbobin kuwa daga garken sarki ne. Fadawansa su ma suka ba da taimako da yardar rai ga mutane da kuma firistoci da Lawiyawa. Hilkiya, Zakariya da Yehiyel masu aiki a haikalin Allah, suka ba firistoci hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyu da ɗari shida da kuma shanu ɗari uku. Haka kuma Konaniya tare da Shemahiya da Netanel, ɗan’uwansa, da Hashabiya, Yehiyel da Yozabad, shugabannin Lawiyawa, suka tanadar da hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyar da kuma bijimai ɗari biyar domin Lawiyawa. (2 Tarihi 35:7-9)
Duk inda akwai mutumin Yahuda da ya rage, sai mutanen da suke zama kusa da shi, su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da kuma dabbobi, tare da kyautai na yardar rai saboda Gidan Allah wanda yake a Urushalima.’ ” Dukan maƙwabtansu kuwa suka taimake su da gudummawa na kayan azurfa da na zinariya, da kaya, da dabbobi, da kuma kyautai masu daraja bisa bayarwar yardar rai da suka yi. (Ezra 1:4, 6)
Waɗansu shugabannin iyalai suka ba da kyautai domin taimakon aiki. Gwamna ya ba da darik 1,000 na zinariya, kwanoni 50, da riguna 530 don firistoci. Waɗansu shugabannin iyalai sun ba da darik 20,000 na zinariya da mina 2,200 na azurfa don aiki. Jimillar da sauran mutane suka bayar ta kai darik 20,000 na zinariya, minas 2,000 na azurfa, da riguna sittin da bakwai don firistoci. (Nehemiya 7:70-72)
Sarki kuwa ya yi ƙasaitacciyar liyafa, liyafar Esta, wa dukan hakimansa da shugabannin masarautarsa. Ya yi shelar hutu ko’ina a larduna, ya kuma raba kyautai a yalwace irin na sarauta. (Esta 2:18)
Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai. (Zabura 72:10)
Amma, kafin Irmiya yă juya yă tafi, Nebuzaradan ya ƙara da cewa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, wanda sarkin Babilon ya naɗa a kan garuruwan Yahuda, ka zauna da shi a cikin mutane, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga dama.” Sa’an nan shugaban ya ba shi abinci da kuma kyauta sai ya bar shi ya tafi. (Irmiya 40:5)

Don a lallashi wasu

Ya kwana a can, daga cikin abin da yake tare da shi kuwa, ya zaɓi kyauta domin ɗan’uwansa Isuwa, Ku kuma tabbata kun ce, ‘Bawanka Yaƙub yana tafe a bayanmu.’ ” Gama Yaƙub ya yi tunani cewa, “Zan kwantar da ran Isuwa da waɗannan kyautai, kafin mu sadu fuska da fuska, wataƙila yă karɓe shi.” (Farawa 32:13, 20)
Isuwa ya yi tambaya, “Me kake nufi da dukan abubuwan nan da na sadu da su ana korarsu?” Sai Yaƙub ya ce, “Don in sami tagomashi a idanunka ne, ranka yă daɗe.” Amma Isuwa ya ce, “Na riga na sami abin da ya ishe ni, ɗan’uwana. Riƙe abin da kake da shi don kanka.” Sai Yaƙub ya ce, “A’a, ina roƙonka, in na sami tagomashi a idanunka, sai ka karɓi wannan kyautai daga gare ni. Gama ganin fuskarka kamar ganin fuskar Allah ne, yanzu da ka karɓe ni da farin ciki. Ina roƙonka ka karɓi kyautar da aka kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri kuma ina da kome da nake bukata.” Ganin yadda Yaƙub ya nace, sai Isuwa ya karɓa. (Farawa 33:8-11)
Kyautar da aka yi a asirce takan kwantar da fushi, kuma cin hancin da aka rufe a cikin riga kan tā da fushi mai tsanani. (Karin Magana 21:14)

Don a rinjayi wasu

Sai Shekem ya ce wa mahaifin Dina da kuma ’yan’uwanta. “Bari in sami tagomashi a idanunku, zan kuwa ba ku duk abin da kuka tambaya. Ku faɗa mini nawa ne dukiyar aure da kuma sadakin da zan kawo bisa ga yadda kuke so, zan kuwa biya duk abin da kuka ce. Ku dai bar ni in aure yarinyar ta zama matata.” (Farawa 34:11-12)

Don a nemi hikima

Dukan sarakunan duniya sun nemi su sadu da Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa. Shekara, shekara, duk wanda ya zo wurinsa yakan kawo kyauta, kayayyakin azurfa da na zinariya, da riguna, makamai da kayan yaji, da dawakai da kuma alfadarai. (2 Tarihi 9:23-24)
Ta kuma ba sarki talenti 120 na zinariya, da kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa haka kamar yadda sarauniyar Sheba ta ba wa Sarki Solomon ba. (1 Sarakuna 10:10)

Mugaye suna murnar mutuwar masu ibada

Mazaunan duniya za su ƙyaface su kuma yi biki ta wurin aika kyautai wa juna, domin waɗannan annabawan nan biyu ne suka azabtar da mazaunan duniya. (Ru’uya ta Yohanna 11:10)

Batutuwan bayarwa dabam-dabam

Wurin da za a bayar

“Dole ne ku kawo mafi kyau daga nunan fari na gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa. (Fitowa 23:19)
“Ku kawo nunan farin amfanin gonarku mafi kyau a gidan Ubangiji, Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa.” (Fitowa 34:26)
...a can ne kuma za ku kawo hadayun ƙonawa da sadakoki, zakkarku da kyautai na musamman, da abin da kuka yi alkawari za ku bayar, da hadayunku na yardar rai, da kuma ’ya’yan farin garkunanku na shanu da na tumaki. (Maimaitawar Shari’a 12:6)
...sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato, hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakkarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na alkawarin da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă sa sunansa. (Maimaitawar Shari’a 12:11)
Kada ku ci zakkar hatsi, da na sabon inabi, da kuma na mai a biranenku, ko kuwa na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki, ko kuwa duk wani abin da kuka yi alkawari za ku bayar, ko hadayunku na yardar rai, ko kyautai na musamman. A maimakon haka, sai ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, ku kuwa yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a kowane abin da kuka sa hannunku. (Maimaitawar Shari’a 12:17-18)

Wataƙila ba mu da kuɗin bayarwa, amma za mu iya bayar da Kristi

To, sai ga wani da aka haifa gurgu ana ɗauke da shi zuwa ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, inda akan ajiye kowace rana, don yă yi bara daga masu shigowa cikin filayen haikali. Da ya ga Bitrus da Yohanna suna gab da shiga, sai ya roƙe su kuɗi. Bitrus kuwa ya kafa masa ido, haka ma Yohanna. Sai Bitrus ya ce, “Dube mu!” Saboda haka mutumin ya mai da hankalinsa a kansu, yana fata samun wani abu daga gare su. Sai Bitrus ya ce, “Azurfa ko zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. A cikin sunan Yesu Kiristi Banazare, ka yi tafiya.” (Ayyukan Manzanni 3:2-6)

Mai karimci zai sami roƙe-roƙe da yawa

Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin mai mulki, kuma kowa na so a ce shi abokin mutumin nan mai yawan kyauta ne. (Karin Magana 19:6)

Ƙyashi na iya shafar bayarwa

Saboda haka, na ga ya dace in roƙi ’yan’uwan nan su ziyarce ku kafin lokacin, su kuma gama shirye-shirye saboda bayarwa ta yardar ran da kuka yi alkawari. Ta haka bayarwar za tă zama a shirye, ta yardar rai ba ta dole ba. (2 Korintiyawa 9:5)

Bayarwa tana kawo godiya ga Allah

Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah. (2 Korintiyawa 9:12)

Kada ka bayar kafin ka yi ƙoƙarin sulhu

“Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci, sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka. (Mattiyu 5:23-24)

Nassi yana ƙarfafa mu mu bayar

Duba, can a bisa duwatsu, ga ƙafafu mai kawo labari mai daɗi, wanda yake shelar salama! Ki yi bukukkuwanki, ya Yahuda, ki kuma cika wa’adodinki. Mugaye ba za su ƙara mamaye ki ba; domin za a hallaka su ƙaƙaf. (Nahum 1:15)
Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi. (Ibraniyawa 13:16)

Bayarwa na iya zama shaida

Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.” (Mattiyu 8:4)
“Ka lura kada ka gaya wa kowa wannan. Amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayun da Musa ya umarta saboda tsarkakewarka, don yă zama shaida gare su.” (Markus 1:44)
Sai Yesu ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.” (Luka 5:14)

Misalin bayarwa ga al’umma

“Bayan ’yan shekaru da dama da ba na nan, sai na dawo Urushalima don in kawo wa mutanena kyautai saboda matalauta in kuma yi sadaka. (Ayyukan Manzanni 24:17)

Abubuwan da suka fi hadaya

Ƙaunar Allah da ta maƙwabci

Nuna ƙauna ga Allah da dukan zuciyarka, da dukan ganewarka, da dukan ƙarfinka, da kuma nuna ƙauna ga maƙwabcinka kamar kanka, ya fi dukan hadayun ƙonawa da sadakoki.” (Markus 12:33)

Aminci ga Allah da saninsa

Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba, ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa. (Hosiya 6:6)

Biyayya

Amma Sama’ila ya ce, “Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya fiye da biyayya ga maganar Ubangiji? Yin biyayya ta fi hadaya a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna. (1 Sama’ila 15:22)
Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku, mene ne suke a gare ni?” Ina da isashen hadayun ƙonawa, na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba; ba na jin daɗin jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki. (Ishaya 1:11)

Adalci / gaskiya

Yin abin da yake daidai da kuma nagari Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya. (Karin Magana 21:3)

Hadayu

Na tilas

“ ‘A bukukkuwa da ƙayyadaddun bukukkuwa, hadaya ta gari zai zama efa tare da bijimi, efa da rago, da kuma ’yan raguna da ya ga dama, haɗe da kwalabar mai. Sa’ad da sarki ya ba da hadaya ta yardar rai ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa ce ko hadayun salama ne, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko hadayarsa ta salama yadda yakan yi a ranar Asabbaci. Sa’an nan ya fita, bayan kuma ya fita, sai a rufe ƙofar. “ ‘Kullum za ku tanada ɗan rago bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji; kowace safiya za ku tanada shi. Tare da shi za ku tanada hadaya ta gari kowace safiya, da ya haɗa da kashi ɗaya bisa shida na efa tare da kashi ɗaya bisa uku na mai ga garin da aka cuɗa. Miƙawar wannan hadaya ta gari ga Ubangiji dawwammamiyar farilla ce. Saboda haka za a tanada ɗan rago da hadaya ta gari da kuma mai kowace safiya don hadaya ta ƙonawa ta kullum. (Ezekiyel 46:11-15)

Na yardar rai

Sa’ad da sarki ya ba da hadaya ta yardar rai ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa ce ko hadayun salama ne, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko hadayarsa ta salama yadda yakan yi a ranar Asabbaci. Sa’an nan ya fita, bayan kuma ya fita, sai a rufe ƙofar. (Ezekiyel 46:12)

Misalan hadayu

Sai sarki da dukan Isra’ila, suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji. Solomon ya miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, shanu dubu ashirin da biyu, tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan Isra’ilawa suka keɓe haikalin Ubangiji. A wannan rana sarki ya tsarkake sashe na tsakiyar fili a gaban haikalin Ubangiji, a can kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, da kitsen hadaya ta salama, gama bagaden tagulla a gaban Ubangiji ya yi ƙanƙanta sosai da za a miƙa hadayun ƙonawa, hadayun hatsi, da kuma kitsen hadayun salama. (1 Sarakuna 8:62-64)
“Ga abin da Sairus sarkin Farisa yake shela, “ ‘Ubangiji Allah na sama ya ba ni iko in yi mulkin duniya duka, ya kuma zaɓe ni in gina masa haikali a Urushalima cikin Yahuda. Duk inda akwai mutumin Yahuda da ya rage, sai mutanen da suke zama kusa da shi, su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da kuma dabbobi, tare da kyautai na yardar rai saboda Gidan Allah wanda yake a Urushalima.’ ” Dukan maƙwabtansu kuwa suka taimake su da gudummawa na kayan azurfa da na zinariya, da kaya, da dabbobi, da kuma kyautai masu daraja bisa bayarwar yardar rai da suka yi. (Ezra 1:2, 4, 6)
Za ka kuma tafi da zinariya da azurfa waɗanda sarki da mashawartansa suka ba da kyautar yardar rai ga Allah na Isra’ila, wanda haikalinsa ke a Urushalima, haɗe da duk zinariya da azurfan da za ka iya samu a Babilon, da kuma duk bayarwar yardar rai daga mutane da firistoci, domin haikalin Allahnsu da yake a Urushalima. Ka tabbata ka yi amfani da kuɗin nan don ka sayi bijimai, da raguna, da ’yan raguna, da hadayu na gari, da na sha, ka kuma miƙa su a kan bagade na haikalin Allahnka a Urushalima. Sa’an nan kai da ’yan’uwanka Yahudawa ku yi abin da kuka ga ya fi kyau da sauran zinariya da azurfa ɗin bisa ga nufin Allah. Duk kuma wani abin da ake bukata domin haikalin Allahnka, daga ɗakunan ajiya sarki za ka fitar da kuɗin. Yanzu fa ni, Sarki Artazerzes, ina ba da umarni ga kowane ma’aji na Kewayen Kogin Yuferites su tanada duk abin da Ezra firist, wanda kuma yake malamin Dokar Allah na sama zai bukaci, har zuwa talenti ɗari na azurfa, da mudu ɗari na alkama, da garwa ɗari na ruwan inabi, da garwa ɗari na man zaitun, da kuma gishiri ba iyaka. (Ezra 7:15-18, 20-22)

Idan baiwarka ta ruhaniya bayarwa ce, ka yi amfani da ita

Muna da baye-baye dabam-dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yă yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa. In ta hidima ce; sai yă yi hidima. In kuma ta koyarwa ce, sai yă koyar; in ta ƙarfafawa ce, sai yă ƙarfafa; in kuma ta ba da taimako ce don biyan bukatun waɗansu, sai yă yi haka hannu sake; in ta shugabanci ce, sai yă yi shugabanci da himma; in ta nuna jinƙai ce, sai yă yi haka da fara’a. (Romawa 12:6-8)

Ka bayar domin biyan bukatu

Da suka gwada a mudu, wanda ya tattara da yawa bai sami mafi yawa ba, wanda kuma ya tattara kaɗan bai sami ƙanƙani ba. Kowane mutum ya tattara daidai bukatarsa. (Fitowa 16:18)
Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. Amma ya yi kyau dai a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu. Wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara da yawa, bai tara fiye da bukatarsa ba, wanda kuma ya tara kaɗan, bai kāsa masa ba.” (2 Korintiyawa 8:13-15)