Aiki

Aiki daga Allah ne kuma dole ne, amma ya kamata a daidaita shi da hutu da sujada. Dukan aiki na gaskiya mai daraja ne idan an yi shi domin Allah. An la’anci ragwanci, kuma ana hana yin aiki fiye da kima.

Ra’ayin Littafi Mai Tsarki game da aiki

Aiki dole ne

Ubangiji kansa ma’aikaci ne

Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa. Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi. (Farawa 2:2-3)
To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi. (Farawa 2:8)
Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yă zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.” (Yohanna 5:17)

Ana bukatarsa a Tsohon Alkawari

Kwana shida za ka yi dukan aikinka, (Fitowa 20:9)
“Kwana shida za ku yi aikinku, amma a rana ta bakwai, kada ku yi aiki, saboda saniyarku da jakinku su huta, haka kuma bawan da aka haifa a gidanku, da kuma baƙon da yake a cikinku yă wartsake. (Fitowa 23:12)
“Kwana shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai za ku huta; ko da lokacin noma ne, ko lokacin girbi, sai ku huta. (Fitowa 34:21)
Kwanaki shida za ka yi aiki, ka kuma yi dukan aikinka, (Maimaitawar Shari’a 5:13)

Ana bukatarsa a Sabon Alkawari

Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata. (Afisawa 4:28)
...ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku. Mun yi wannan, ba don ba mu da ’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi. Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.” Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci. (2 Tessalonikawa 3:8-12)

Ana sa ran aiki

Mutum yakan tafi aikinsa, zuwa wurin aikinsa har yamma. (Zabura 104:23)

Bukatar yin aiki ba sakamakon zunubi ba ce

Mutum yakan tafi aikinsa, zuwa wurin aikinsa har yamma. (Zabura 104:23)

Ubangiji ya umarci mutane su yi aiki bayan faɗuwa, amma aiki ya fi wuya

Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’ “Za a la’anta ƙasa saboda kai. Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka. Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za ka kuwa ci ganyayen gona. Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa, da yake daga cikinta aka yi ka. Gama kai turɓaya ne, kuma ga turɓaya za ka koma.” Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi. (Farawa 3:17-19, 23)
Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.” (Farawa 5:29)

Dukan aiki na gaskiya mai daraja ne

Misalan sana’o’in masu ibada

Manomi

Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi. (Farawa 2:15)
Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi. (Farawa 4:2)
Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi. (Farawa 9:20)
Mutanen fa, makiyaya ne; suna kiwon dabbobi, sun kuma zo tare da garkunansu da shanunsa da kuma kome da suka mallaka.’ (Farawa 46:32)
Fir’auna ya tambayi ’yan’uwan, “Mece ce sana’arku?” Suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Bayinka makiyaya ne, kamar yadda kakanninmu suke.” (Farawa 47:3)
Amos ya amsa wa Amaziya, “Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi, amma ni makiyayi ne, kuma ina lura da itatuwan al’ul. (Amos 7:14)

Ma’aikacin gida

...sai Yusuf ya sami tagomashi a idanunsa, ya kuma zama mai hidimarsa. Fotifar ya sa shi yă zama shugaba a gidansa, ya kuma danƙa masa kome da yake da shi. (Farawa 39:4)

Ma’aikatan gwamnati da shugabanni

Saboda haka Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ga shi na sa ka zama shugaban dukan ƙasar Masar.” (Farawa 41:41)
Suka faɗa masa, “Yusuf yana da rai! Gaskiya, shi ne mai mulkin dukan Masar.” Gaban Yaƙub ya fāɗi, domin bai gaskata su ba. (Farawa 45:26)
Bayan na dudduba abubuwa, sai na miƙe tsaye na ce wa manyan gari da shugabanni da kuma sauran jama’a, “Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna da Ubangiji, wanda yake mai girma da banrazana, ku yi yaƙi don ’yan’uwanku, da ’ya’yanku maza da mata, da matanku da kuma gidajenku.” (Nehemiya 4:14)
Ya mai da shi shugaban gidansa, mai mulki a bisa dukan abin da ya mallaka, (Zabura 105:21)
Sai sarki ya ɗora Daniyel a babban matsayi ya kuma sanya shi mai mulki a kan dukan yankin ƙasar Babilon; ya kuma ɗora shi yă zama mai kula da duk masu hikima. (Daniyel 2:48)
Ya gamshi Dariyus ya naɗa muƙaddasai 120 su yi shugabanci a duk fāɗin masarautar, ya naɗa mutum uku a bisa waɗannan muƙaddasan, Daniyel yana ɗaya daga cikin mutum ukun nan. Sai aka sa muƙaddasan nan a ƙarƙashin waɗannan uku ɗin domin kada sarki ya yi hasarar kome. (Daniyel 6:1-2)
Ni, Daniyel, na gaji matuƙa na kuma yi rashin lafiya na kwanaki masu yawa. Sa’an nan sai na tashi na ci gaba da hidimar sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ya fi ƙarfin fahimtata. (Daniyel 8:27)
Saboda haka ya kama hanya, a kan hanyarsa kuwa sai ya sadu da wani mutumin Itiyofiya, wanda yake bābā, hafsa mai muhimmanci wanda yake lura da dukan ma’ajin Kandas (wanda yake nufin “sarauniyar mutanen Itiyofiya”). Mutumin nan ya tafi Urushalima ne domin yin sujada, (Ayyukan Manzanni 8:27)

Masunta

Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne. (Mattiyu 4:18)
Yayinda Yesu yake tafiya a gaɓar Tekun Galili, sai ya ga Siman da ɗan’uwansa Andarawus, suna jefa abin kamun kifi a cikin tafkin, domin su masunta ne. (Markus 1:16)
Ba da ɓata lokaci ba, ya kira su, sai suka bar mahaifinsu Zebedi a cikin jirgin ruwan, tare da ’yan haya, suka kuwa bi shi. (Markus 1:20)

Sana’o’in gini

Wannan ba shi ne ɗan kafinta nan ba? Ba mahaifiyarsa ba ce Maryamu, ’yan’uwansa kuma Yaƙub, Yusuf, Siman da Yahuda ba? (Mattiyu 13:55)
Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa. (Markus 6:3)
A can ya sadu da wani mutumin Yahuda mai suna Akwila, ɗan garin Fontus, wanda ya je can ba da daɗewa ba daga Italiya tare da matarsa Firiskila, gama Kalaudiyus ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya tafi yă gan su, da yake shi ma mai ɗinkin tenti ne kamar su, sai ya zauna ya yi aiki tare da su. (Ayyukan Manzanni 18:2-3)

Masu karɓar haraji

Yana cikin tafiya, sai ya ga Lawi, ɗan Alfayus zaune a inda ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai Lawi ya tashi, ya bi shi. (Markus 2:14)
Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” (Luka 5:27)
Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma. (Luka 19:2)

Ɗan kasuwa

Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yadunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus. (Ayyukan Manzanni 16:14)

Ka yi aiki kamar ga Ubangiji

Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah. (1 Korintiyawa 10:31)
Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin bangirma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi. Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su sa’ad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku. Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba. Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce. Ku kuma masu bayi, dole ku bi da bayinku da kyau. Ku daina ba su tsoro. Ku tuna, ku da su, Maigida ɗaya kuke da shi a sama, kuma ba ya nuna bambanci. (Afisawa 6:5-9)
Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa. (Kolossiyawa 3:17)
Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa. (Kolossiyawa 3:23-24)

Wasu mutane suna ɗaukar aiki a matsayin aikin banza

Wace riba ce mutum yake samu daga wahalar da yake fama a duniya? (Mai Hadishi 1:3)
Na yi ayyuka masu girma. Na gina gidaje wa kaina na kuma shuka gonakin inabi. Na yi lambuna da wuraren shaƙatawa, na shuka itatuwa masu ’ya’ya iri-iri a cikinsu. Ban hana kaina duk wani abin da idona ya yi sha’awarsa ba; ban hana zuciyata wani jin daɗi ba. Zuciyata ta yi murna da dukan aikina, wannan kuwa shi ne ladan dukan famata. Duk da haka sa’ad da na duba dukan aikin hannuwana, da abin da na yi fama don in samu, sai kome ya zama ba shi da amfani, naushin iska ne kawai; babu wata riba a duniya. (Mai Hadishi 2:4-5, 10-11)
Na ƙi jinin dukan abubuwan da na yi wahala ina yi a duniya, gama dole in bar su wa na bayana. Wa ya sani ko zai zama mai hikima ko kuma wawa? Duk da haka zai mallaki dukan aikin da na yi da ƙoƙarina da kuma dabarata a duniya. Wannan ma ba shi da amfani. Saboda haka zuciyata ta fara karaya a kan dukan faman aikina a duniya. Gama mutum zai yi aikinsa da dukan hikimarsa, da saninsa, da gwanintarsa, sa’an nan dole yă bar dukan abin da ya mallaka ga wani wanda bai yi wahalar kome a ciki ba. Wannan ma ba shi da amfani, hasara ce mai yawa. Me mutum zai samu daga aikin da ya yi duka, da irin ɗawainiyar da ya sha a kan yin aikin a duniya? Dukan kwanakinsa aikinsa damuwa ce da ɓacin zuciya; ko da dare ma hankalinsa ba a kwance yake ba. Wannan ma ba shi da amfani. Ba abin da mutum zai yi da ya fi yă ci, yă sha, yă ji wa ransa daɗi daga aikinsa. Na lura cewa wannan ma, ya fito daga hannun Allah ne, (Mai Hadishi 2:18-24)
Wace riba ce ma’aikaci yake da ita saboda wahalarsa? Na ga nawayar da Allah ya ɗora a kan mutane. Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce. (Mai Hadishi 3:9-10, 13)
Sai na gane cewa, duk wata fama da duk wata nasara sun samo asali daga kishin da mutum yake yi na maƙwabcinsa ne. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai. Wawa yakan kame hannuwansa yă kuma lalatar da kansa. Gara tafin hannu guda cike da kwanciyar rai da tafin hannu biyu cike da tashin hankali da harbin iska kawai. (Mai Hadishi 4:4-6)
Sa’an nan na gane cewa abu mai kyau ne, daidai ne kuma mutum yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗin aikin da ya yi a ’yan kwanakin da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum daga faman wahalarsa a duniya a cikin ’yan kwanakin da Allah ya ba shi a duniya, gama wannan shi ne rabonsa. Ban da haka ma, sa’ad da Allah ya ba wa mutum dukiya da wadata, ya kuma ba shi zarafi yă ji daɗinsu, ya kuma amince da rabonsa, sai yă ji daɗin aikinsa, wannan kyauta ce ta Allah. (Mai Hadishi 5:18-19)
Dukan ƙoƙarin da mutum yake yi, yana yi ne domin bakinsa, duk da haka bai taɓa gamsar da abin da yake marmari. (Mai Hadishi 6:7)

Ya kamata aikinmu ya zama aikin da Allah ya nufa domin mu

Na zaɓi mahaifinka daga cikin dukan kabilar Isra’ila yă zama firist nawa don yă yi hidima a bagade, don yă ƙona turare mai ƙanshi, don kuma yă sanya doguwar riga a gabana. Na kuma ba wa iyalin mahaifinka dukan hadaya ta ƙonawa da Isra’ila suka miƙa. (1 Sama’ila 2:28)
Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu; ka albarkaci mana aikin hannuwanmu, I, ka albarkaci aikin hannuwanmu. (Zabura 90:17)
Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa. (Yohanna 4:34)
Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yă zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.” (Yohanna 6:27)
“Gama sa’ad da Dawuda ya gama hidimar nufin Allah a zamaninsa, sai ya yi barci; aka binne shi tare da kakanninsa jikinsa kuwa ya ruɓe. (Ayyukan Manzanni 13:36)
...aikin zai bayyana kansa, domin za a nuna shi a sarari a Ranar. Wuta ce za tă bayyana aikin, wutar kuwa za tă gwada ingancin aikin kowa. In abin da kowane mutum ya gina ya tsaya, zai sami lada. In ya ƙone, zai yi hasara, amma zai sami ceto, sai dai kamar wanda ya bi ta tsakiyar wuta ne. (1 Korintiyawa 3:13-15)
Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi. (Afisawa 2:10)

Aikin da zai ɗaukaka Ubangiji

Na ɗaukaka ka a duniya ta wurin gama aikin da ka ba ni. (Yohanna 17:4)

Yana da amfani a san takamaiman aikin da Ubangiji yake da shi domin mu

Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba. Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba. Sai ya ce musu, “Abokai, kuna da kifi kuwa?” Suka amsa suka ce, “A’a.” Ya ce musu, “Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.” Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi. Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan. Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne. Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi. Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.” Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba. (Yohanna 21:3-11)

Aiki banza ne ba tare da Ubangiji ba

Waƙar haurawa. Ta Solomon. In ba Ubangiji ne ya gina gida ba, masu gininta suna wahala a banza ne. In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba, masu tsaro suna yin tsaro a banza. (Zabura 127:1)
Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara. (Karin Magana 16:3)

Kada a sami son kai a cikin aiki

Allah, “Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi.” Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu. (Romawa 2:6, 8)
Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan. Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau. (2 Korintiyawa 5:9-10)
Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya. Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma. Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki. (Yaƙub 3:14-16)

Kada ka nemi girma domin kanka

Ya kamata ka nemi manyan abubuwa wa kanka? Kada ka neme su. Gama zan aukar da masifa a kan dukan mutane, in ji Ubangiji, amma duk inda ka tafi zan bar ka ka kuɓutar da ranka.’ ” (Irmiya 45:5)

Ka yi ƙarfi, ka yi ƙarfin hali, kada kuma ka jinkirta

“Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, gama kai za ka bi da mutanen nan har su karɓi ƙasar da na yi wa kakanninsu alkawari zan ba su. Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je. (Yoshuwa 1:6-7)
Shi ne wanda zai gina gida saboda Sunana. Zai zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa. Zan kafa kujerar sarautarsa a bisa Isra’ila har abada.’ Ta haka za ka yi nasara in ka mai da hankali ga kiyaye ƙa’idodi da dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa saboda Isra’ila. Ka yi ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya. zinariya da azurfa, tagulla da ƙarfe, masu sana’a waɗanda suka wuce ƙirge. Yanzu ka fara aiki, Ubangiji kuma ya kasance tare da kai.” (1 Tarihi 22:10, 13, 16)
Dawuda ya kuma ce wa Solomon ɗansa, “Ka yi ƙarfin hali, ka kuma yi aikin. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya, gama Ubangiji Allah, Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ko yă yashe ka ba, sai an gama dukan aikin saboda hidimar haikalin Ubangiji. (1 Tarihi 28:20)
Amma game da ku, ku ƙarfafa kada ku fid da zuciya, gama za a ba ku ladan aikinku.” (2 Tarihi 15:7)
Amma yanzu ka ƙarfafa, ya Zerubbabel,’ in ji Ubangiji. ‘Ka ƙarfafa, ya Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist. Ku ƙarfafa, dukanku mutanen ƙasar,’ in ji Ubangiji, ‘ku yi aiki. Gama ina tare da ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. (Haggai 2:4)

Za mu fuskanci wahaloli sa’ad da muke aikin da Ubangiji yake da shi domin mu

Sai mutanen da suke zama a wurin suka fara yin ƙoƙari su sa mutanen Yahuda su karaya, suka sa su ji tsoron ci gaba da ginin. Suka yi hayar mashawarta don su ga cewa sun ɓata ƙoƙarinsu dukan kwanakin mulkin Sairus sarkin Farisa har zuwa kwanakin mulkin Dariyus sarkin Farisa. (Ezra 4:4-5)
Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa. (Karin Magana 23:4)
Da abokan gābanmu suka ji muna sane da shirinsu, Allah kuma ya wargaje shirin nan, sai duk muka dawo ga katangar, kowa ya kama aikinsa. Daga wannan rana zuwa gaba, rabin mutane suka yi aiki, yayinda sauran rabin suka kintsa da māsu, da garkuwa, da bakkuna da makamai. Shugabanni suka goyi bayan dukan mutanen Yahuda waɗanda suke ginin katanga. Waɗanda suke ɗaukan kaya suka yi aikinsu da hannu ɗaya, suna kuma riƙe da makami a ɗaya hannun, kuma kowane mai gini ya ɗaura takobinsa a gefe yayinda yake aiki. Amma mutum mai busa ƙaho ya kasance tare da ni. Sai na ce wa manyan gari, da shugabanni, da sauran jama’a, “Aikin nan babba ne kuma mai yawa, ga shi muna a rarrabe nesa da juna a katangar. Duk inda kuka ji an busa ƙaho, sai ku taru a wurin. Allahnmu zai yi yaƙi dominmu!” Saboda haka muka ci gaba da aiki, rabin mutane suna riƙe da māsu, daga wayewar gari har zuwa fitowar taurari. A wannan lokaci na kuma ce wa mutane, “A sa kowane mutum da mataimakinsa su zauna a Urushalima da dare, domin a yi tsaro da dare, da safe kuma a kama aiki.” (Nehemiya 4:15-22)
...saboda haka sai na aika musu da wannan amsa, na ce, “Ina cikin babban aiki, ba zan kuwa iya gangarawa ba. Don me zan bar aikin yă tsaya don in gangara zuwa wurinku?” Suka dai yi ƙoƙari su tsoratar da mu, suna cewa, “Hannuwansu za su rasa ƙarfin yin aiki, ba kuwa za su ƙare aikin ba.” Amma na yi addu’a na ce, “Yanzu, ya Allah, ka ƙarfafa hannuwana.” (Nehemiya 6:3, 9)

Ka yi aiki tuƙuru

Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta, amma mai aiki tuƙuru yakan ɗauki mallakarsa da muhimmanci. (Karin Magana 12:27)
Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima. (Mai Hadishi 9:10)
Ka shuka irinka da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka. (Mai Hadishi 11:6)

Misalan ma’aikata masu ƙwazo

“Na kasance tare da kai shekaru ashirin. Tumakinka da awakinka ba su yi ɓarin ciki ba, ban kuwa ci raguna daga garkunanka ba. Ban kawo dabbobinka da namun jeji suka yayyaga; na kuma ɗauki hasarar ba? Ka nemi in biya dukan abin da aka sace da rana ko da dare. Yanayin da na kasance ke nan, da rana na sha zafin rana da dare kuma na sha sanyi, ga rashin barci. (Farawa 31:38-40)
Na kuma faɗa musu game da yadda alherin Allahna yake tare da ni da kuma abin da sarki ya faɗa mini. Suka amsa, suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Sai suka fara wannan aiki mai kyau. (Nehemiya 2:18)
Sai muka sāke ginin katangar sai da duka ta kai rabin tsayinta, gama mutane sun yi aiki da dukan ƙarfinsu. (Nehemiya 4:6)
Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina. (Ayyukan Manzanni 20:34)
Har yă zuwa wannan sa’a, yunwa da ƙishirwa muke ciki, muna sanye da tsummoki, ana wulaƙanta mu, ba mu kuma da gida. Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka la’anta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre; (1 Korintiyawa 4:11-12)
Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara. (2 Korintiyawa 11:27)
Don haka ne ina fama, ina kuma ƙoƙari da duk ƙarfin nan da Kiristi ya ba ni. (Kolossiyawa 1:29)
Ba shakka kuna iya tunawa, ’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah. (1 Tessalonikawa 2:9)
...ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku. (2 Tessalonikawa 3:8)

Yunwa tana sa mu yi aiki

Marmarin cin abinci yakan yi wa ɗan ƙodago aiki; yunwarsa kan sa ya ci gaba. (Karin Magana 16:26)

Ya kamata a fara biyan ma’aikata masu ƙwazo

Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona. (2 Timoti 2:6)

Amfanin aiki / aiki tuƙuru

Biyan bukatu

Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne. (Karin Magana 12:11)
Duk wanda ya lura da itacen ɓaure, zai ci ’ya’yansa, kuma duk wanda ya lura da maigidansa za a girmama shi. (Karin Magana 27:18)
Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace, amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe. (Karin Magana 28:19)

Riba da dukiya

Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya. Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya. (Karin Magana 10:4-5)
Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri, amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa. (Karin Magana 13:11)
Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai. (Karin Magana 14:23)
Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci. (Karin Magana 21:5)

Rai mai gamsuwa

Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai. (Karin Magana 13:4)

Shugabanci

Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki, amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta. (Karin Magana 12:24)

Barci mai daɗi

Barcin ma’aikaci daɗi gare shi, ko yă ci kaɗan ko da yawa, amma yalwar mai arziki ba ta barinsa yă iya yin barci. (Mai Hadishi 5:12)

Farin ciki

Waƙar haurawa. Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa. Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka. (Zabura 128:1-2)

Kada ka yi aiki fiye da kima

Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna. (Zabura 127:2)

Kada ka yi aiki fiye da kima don ka yi arziki

Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa. (Karin Magana 23:4)

An la’anci ragwanci

Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima! Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki, duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi. (Karin Magana 6:6-8)
Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya. (Karin Magana 10:5)
Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu, haka malalaci yake ga wanda ya aike shi. (Karin Magana 10:26)
Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta, amma mai aiki tuƙuru yakan ɗauki mallakarsa da muhimmanci. (Karin Magana 12:27)
An tare hanyar rago da ƙayayyuwa, amma hanyar mai aikata gaskiya buɗaɗɗiyar hanya ce. (Karin Magana 15:19)
Wanda yake ragwanci a aikinsa ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa. (Karin Magana 18:9)
Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa! (Karin Magana 19:24)
Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!” Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!” (Karin Magana 22:13)
Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya, zaki mai faɗa yana yawo a tituna!” Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa, haka rago yake jujjuya a gadonsa. Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa. Rago yana gani yana da hikima fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu. (Karin Magana 26:13-16)

Sakamakon ragwanci

Yunwa

Ragwanci kan jawo zurfin barci, mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa. (Karin Magana 19:15)
Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome. (Karin Magana 20:4)

Talauci

Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku? Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta, talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari rashi kuma kamar ɗan fashi. (Karin Magana 6:9-11)
Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya. (Karin Magana 10:4)
Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai. (Karin Magana 14:23)
Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce; ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci. (Karin Magana 20:13)
...gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki. (Karin Magana 23:21)
Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci; ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe. Na yi tunani a zuciyata na kuwa koyi darasi daga abin da na gani. Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta, sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari. (Karin Magana 24:30-34)
In mutum rago ne, sai tsaiko yă lotsa, in hannuwansa ba masa yin kome, ɗaki yakan yi yoyo. (Mai Hadishi 10:18)

Mutuwa

Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki. (Karin Magana 21:25)

Rai mai yunwa

Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai. (Karin Magana 13:4)

Aikin tilas

Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki, amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta. (Karin Magana 12:24)

Ka keɓe lokaci daga aiki domin hutu da sujada

Asabaci

Ubangiji ya kafa Asabaci

Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa. Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi. (Farawa 2:2-3)
Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki. (Fitowa 20:11)
Zai zama alama tsakanina da Isra’ilawa har abada, gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama da ƙasa, a rana ta bakwai kuma ya daina aiki, ya kuma huta.’ ” (Fitowa 31:17)
Gama a wani wuri ya yi magana a kan rana ta bakwai cikin waɗannan kalmomi, “A rana ta bakwai kuwa Allah ya huta daga dukan aikinsa.” gama duk wanda ya shiga hutun Allah, shi ma yakan huta daga nasa aiki, kamar yadda Allah ya huta daga nasa. (Ibraniyawa 4:4, 10)

Ana bukatar Asabaci a Tsohon Alkawari

A rana ta fari, za ku yi taro mai tsarki, haka kuma za ku sāke yi a rana ta bakwai. Kada ku yi aiki a waɗannan ranaku, sai dai ku shirya abinci domin kowa, abin da za ku yi ke nan kawai. (Fitowa 12:16)
Kwana shida za ka yi dukan aikinka, amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai. (Fitowa 20:9-10)
“Kwana shida za ku yi aikinku, amma a rana ta bakwai, kada ku yi aiki, saboda saniyarku da jakinku su huta, haka kuma bawan da aka haifa a gidanku, da kuma baƙon da yake a cikinku yă wartsake. (Fitowa 23:12)
“Kwana shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai za ku huta; ko da lokacin noma ne, ko lokacin girbi, sai ku huta. (Fitowa 34:21)
Kwana shida za ku yi aiki, amma rana ta bakwai za tă zama rana mai tsarki, Asabbaci ne na hutu ga Ubangiji. Duk wanda ya yi aiki a wannan rana dole a kashe shi. (Fitowa 35:2)
“ ‘Akwai kwanaki shida da za ku iya yin aiki, amma rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, rana mai tsarki ga jama’a. Kada ku yi wani aiki a ko’ina kuke da zama, Asabbaci ne ga Ubangiji. (Firistoci 23:3)
Kwanaki shida za ka yi aiki, ka kuma yi dukan aikinka, amma rana ta bakwai, Asabbaci ne ga Ubangiji Allahnka. A kanta ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko saniyarka, ko jakinka, ko wani daga dabbobinka, ko baƙo a ƙofofinka, don bayinka maza da mata su ma su huta, kamar ka. (Maimaitawar Shari’a 5:13-14)
“Sa’ad da maƙwabta suka kawo kayayyaki ko hatsi don su sayar a ranar Asabbaci, ba za mu saya daga gare su a ranar Asabbaci ko a rana mai tsarki ba. Kowace shekarar Asabbaci ba za mu nome ƙasa ba kuma za mu yafe kowane irin bashi. (Nehemiya 10:31)
Ga abin da Ubangiji yana cewa, ku yi hankali kada ku ɗauki kaya a ranar Asabbaci ko ku shigar da shi ta ƙofofin Urushalima. Kada ku fitar da kayan gidajenku ko ku yi wani aiki a ranar Asabbaci mai tsarki, yadda na umarci kakanni-kakanninku. Amma in kuka yi hankali kuka yi mini biyayya, in ji Ubangiji, ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofi a ranar Asabbaci ba, amma kuka kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba tare da yin wani aiki a cikinta ba, (Irmiya 17:21-22, 24)

Hukunci saboda rashin kiyaye Asabaci

Kwana shida, za a yi aiki, amma a rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, mai tsarki ga Ubangiji. Duk wanda ya yi wani aiki a Asabbaci, za a kashe shi. (Fitowa 31:15)
Yayinda Isra’ilawa suke ciki hamada, sai aka sami wani mutum yana tattara itace a ranar Asabbaci. Waɗanda suka gan shi, suka kawo shi wurin Musa da Haruna da dukan taro, sai suka sa shi a gidan waƙafi don ba su riga sun san abin da za a yi da shi ba tukuna. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Dole mutumin yă mutu. Dole dukan taron su jajjefe shi a bayan sansani.” (Ƙidaya 15:32-35)
A waɗannan kwanaki, na ga mutane a Yahuda suna matse ruwan inabi a ranar Asabbaci suna kuma kawo hatsi suna labta su a kan jakuna, tare da ruwan inabi, ’ya’yan inabi, ɓaure da kaya iri-iri. Suna kuma kawowa dukan wannan cikin Urushalima a ranar Asabbaci. Saboda haka na gargaɗe su a kan sayar da abinci a wannan rana. Mutane daga Taya waɗanda suke zama a Urushalima suna shigar da kifi da kaya iri-iri na ’yan kasuwa suna kuma sayar da su a Urushalima a ranar Asabbaci wa mutanen Yahuda. Sai na tsawata wa manyan Yahuda na ce musu, “Wanda irin mugun abu ke nan kuke yi, kuna ƙazantar da ranar Asabbaci? Kakanninku ba su yi irin waɗannan abubuwa ba, har Allahnmu ya kawo dukan masifun nan a kanmu da kuma a kan wannan birni? Yanzu kuna tsokanar fushi mai yawa a kan Isra’ila ta wurin ƙazantar da Asabbaci.” (Nehemiya 13:15-18)
“Sa’ad da ka faɗa musu wannan duka, ba za su saurare ka ba; sa’ad da ka kira su, ba za su amsa ba. (Irmiya 7:27)

Shekarar hutu

“Shekara shida za ku nome gonakinku ku girbe amfanin gonar, amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun. (Fitowa 23:10-11)
Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai ya ce, “Yi wa Isra’ilawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, dole ƙasar kanta ta kiyaye Asabbaci ga Ubangiji. Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu. Amma a shekara ta bakwai, ƙasar za tă sami hutun Asabbaci, Asabbaci ga Ubangiji. Kada ku yi shuki a gonakinku, ko kuwa ku aske gonakinku na inabi. Kada ku girbe abin da ya yi girma ba tare da ku kuka shuka ba, ko ku girbe inabin da ba ku aske ba. Ƙasar za tă kasance da shekarar hutu. (Firistoci 25:1-5)
“Sa’ad da maƙwabta suka kawo kayayyaki ko hatsi don su sayar a ranar Asabbaci, ba za mu saya daga gare su a ranar Asabbaci ko a rana mai tsarki ba. Kowace shekarar Asabbaci ba za mu nome ƙasa ba kuma za mu yafe kowane irin bashi. (Nehemiya 10:31)

Sakamakon rashin kiyaye shekarar hutu

Sa’an nan ƙasar za tă ji daɗin hutun shekarun Asabbacinta, a dukan lokutan da take kango, ku kuwa kuna a ƙasar abokan gābanku, sa’an nan ƙasar za tă huta ta ji daɗin asabbatanta. (Firistoci 26:34)
Gama za su gudu su bar ƙasar, ƙasar kuwa ta ji daɗin asabbatanta yayinda take kango muddin ba su ciki. Za su biya hukuncin zunubansu domin sun ƙi dokokina, suka kuma yi ƙyamar farillaina. (Firistoci 26:43)

Shekarar Murna

Shekara ta hamsin za tă zama ta murna a gare ku; kada ku yi shuki, kada kuma ku yi girbi abin da ya yi girma da kansa, ko ku girbe inabin da ba ku lura da shi ba. (Firistoci 25:11)

Bukukuwan addini a Tsohon Alkawari

Idin Ƙetarewa

A rana ta farko, za ku yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi na kullum ba. (Ƙidaya 28:18)
A rana ta bakwai, za ku yi tsattsarkan taro, amma ba za a yi aikin da aka saba yi kullum ba. (Ƙidaya 28:25)
Kwana shida za ku ci burodi marar yisti, a rana ta bakwai kuma sai ku yi taro ga Ubangiji Allahnku, a cikin wannan rana ba za ku yi kowane irin aiki ba. (Maimaitawar Shari’a 16:8)

Ranar Kafara

“Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare ku. A rana ta goma ga wata na bakwai, dole ku yi mūsu kanku, ba kuwa za ku yi wani aiki ba, ko da mutum baƙo ne a cikinku ko kuwa ɗan ƙasa, (Firistoci 16:29)
“Rana ta goma ta wata bakwai, za tă zama Ranar Kafara. Sai ku yi taro mai tsarki don ku yi mūsun kanku ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji. Kada ku yi aiki a ranar, gama Ranar Kafara ce, sa’ad da za a yi kafara saboda ku a gaban Ubangiji Allahnku. Duk wanda bai yi mūsun kansa a wannan rana ba, dole a raba shi daga mutanensa. Zan hallaka duk wani da ya yi aiki a wannan rana daga mutanensa. Sam ba za ku yi wani aiki ba. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce, wa tsararraki masu zuwa, a ko’ina kuke da zama. (Firistoci 23:27-31)

Idin Gurasa Marar Yisti

A rana ta fari, ku yi taro mai tsarki, ba kuwa za ku yi aiki na kullum ba. Kwana bakwai za ku miƙa hadaya ga Ubangiji da wuta. A rana ta bakwai ɗin ku yi taro mai tsarki, ba za ku kuwa yi aiki na kullum ba.’ ” (Firistoci 23:7-8)

Idin Bukkoki

“Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar goma sha biyar ga wata na bakwai, za a fara Bikin Tabanakul na Ubangiji, zai kuma ɗauki kwana bakwai. A ranar farko za tă zama ta taro mai tsarki, kada ku yi aiki na kullum. Kwana bakwai za ku miƙa hadayun da aka yi da wuta ga Ubangiji, a rana ta takwas, ku yi taro mai tsarki, ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji. Wannan ranar rufewar taro ce; kada ku yi aiki na kullum. (Firistoci 23:34-36)
“ ‘A rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. Ku yi biki ga Ubangiji har kwana bakwai. “ ‘A rana ta takwas kuwa za a yi tsattsarkan taro, ban da aikin da aka saba. (Ƙidaya 29:12, 35)

Bukukuwan addini dabam-dabam

A wannan rana za ku yi taro mai tsarki, ba kuwa za ku yi aiki na kullum ba. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa, a ko’ina kuke da zama. (Firistoci 23:21)
“Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar farko ga wata na bakwai, za tă zama ranar hutu, rana ce ta tuni da yin taro mai tsarki na sujada da za a fara busar ƙaho. Kada ku yi aiki na kullum, amma ku miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.’ ” (Firistoci 23:24-25)
“ ‘A ranar nunan fari, sa’ad da za ku miƙa wa Ubangiji hadayar sabon hatsi, a lokacin Bikin Makoni, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. (Ƙidaya 28:26)
“ ‘A rana ta farko ga wata na bakwai, a yi tsattsarkan taro, kada kuma a yi aikin da aka saba na kullum. Rana ce don busa ƙahoni. (Ƙidaya 29:1)
“ ‘A rana ta goma ga wannan watan bakwai, za a yi tsattsarkan taro. Ba za ku ci abinci ba, ba kuma za ku yi aiki ba. (Ƙidaya 29:7)

Rabon Allah a cikin aiki

Allah yana ba da ƙwarewar aiki

Ka faɗa wa dukan gwanayen da na ba su hikima a irin abubuwan nan, cewa su yi tufafi saboda Haruna, don a tsarkakewarsa, domin yă yi mini hidima a matsayin firist. (Fitowa 28:3)
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda, na kuma cika shi da Ruhun Allah, fasaha, azanci, da kuma sani cikin kowace irin sana’a, (Fitowa 31:1-3)
Ban da haka, na zaɓi Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, don yă taimake shi. Na kuma ba da fasaha ga dukan masu aikin sana’ar hannu, don yin duk abin da na umarce ka. (Fitowa 31:6)
Sa’an nan ya ce wa Isra’ilawa, “Duba Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, daga kabilar Yahuda, ya kuma cika shi da Ruhun Allah, da fasaha, azanci da kuma sani cikin dukan sana’ar hannu, don yă ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta waɗanda za yi da zinariya, da azurfa da kuma tagulla. Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta. Ya kuma ba Bezalel da Oholiyab ɗan Ahisamak, daga kabilar Dan, iyawa don koya wa waɗansu. Ya cika su da fasaha don yin kowane irin aikin sana’a, zāne-zāne, ɗinke-ɗinke shuɗi, shunayya da jan zare, da lallausan lilin, da kuma masu yin saƙa, sun gwaninta ƙwarai cikin kowane irin aikin hannu da kuma zāne-zāne. (Fitowa 35:30-35)
Saboda haka Bezalel, Oholiyab da kowane mutumin da Ubangiji ya ba shi basira da iyawa, na sanin yadda za a yi duk aikin shirya wuri mai tsarki, za su yi aiki yadda Ubangiji ya umarta.” Sa’an nan Musa ya kira Bezalel da Oholiyab da kowane mutumin da Ubangiji ya ba shi iyawa da kuma wanda ya yi niyya yă yi aiki. (Fitowa 36:1-2)
Bari Ubangiji ya ba ka basira da fahimi sa’ad da ya sa ka shugaba a bisa Isra’ila, saboda ka kiyaye dokar Ubangiji Allahnka. (1 Tarihi 22:12)
Allah ya ce wa Solomon, “Da yake wannan ne sha’awar zuciyarka, ba ka kuwa nemi wadata, arziki ko girma ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, da yake kuma ba ka nemi tsawon rai ba, amma ka nemi hikima da sani don ka shugabanci jama’ata wadda na naɗa ka sarki, saboda haka za a ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka wadata, arziki da girma, waɗanda babu wani sarki kafin kai da ya taɓa kasance da su kuma babu wani a bayanka da zai kasance da su.” (2 Tarihi 1:11-12)
Dukan sarakunan duniya sun nemi su sadu da Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa. (2 Tarihi 9:23)
Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai. (Mai Hadishi 2:26)
Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki. (Daniyel 1:17)
Yana sāke lokuta, yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu. Yana ba da hikima ga masu hikima kuma ilimi ga masu basira. Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina. Kai ka san hikima da iko, ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.” (Daniyel 2:21, 23)

Allah yana ba da nasara

Ubangiji kuwa yana tare da Yusuf, Yusuf kuwa yi nasara, ya zauna a gidan mutumin Masar maigidansa. Sa’ad da maigidansa ya ga cewa Ubangiji yana tare da Yusuf, kuma cewa Ubangiji ya ba shi nasara a kome da ya yi, (Farawa 39:2-3)
Bari Ubangiji yă sāka maka saboda abin da ka yi. Bari Ubangiji, Allah na Isra’ila yă sāka maka a yalwace, a ƙarƙashin fikafikan da ka sami mafaka.” (Rut 2:12)
“Yanzu, ɗana, Ubangiji ya kasance tare da kai, bari kuma ka yi nasara ka kuma gina gidan Ubangiji Allahnka, kamar yadda ya ce za ka yi. (1 Tarihi 22:11)
Na kuma faɗa musu game da yadda alherin Allahna yake tare da ni da kuma abin da sarki ya faɗa mini. Suka amsa, suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Sai suka fara wannan aiki mai kyau. Na amsa musu na ce, “Allah na sama zai ba mu nasara. Mu bayinsa za mu tashi mu fara gini, amma game da ku kam, ba ku da rabo cikin Urushalima, ba ku da wani hakki ko wani abin tunawa.” (Nehemiya 2:18, 20)
Da abokan gābanmu suka ji muna sane da shirinsu, Allah kuma ya wargaje shirin nan, sai duk muka dawo ga katangar, kowa ya kama aikinsa. Sai na ce wa manyan gari, da shugabanni, da sauran jama’a, “Aikin nan babba ne kuma mai yawa, ga shi muna a rarrabe nesa da juna a katangar. Duk inda kuka ji an busa ƙaho, sai ku taru a wurin. Allahnmu zai yi yaƙi dominmu!” (Nehemiya 4:15, 19-20)
Cikin kwana hamsin da biyu aka gama gina katangar, a ranar ashirin da biyar ga watan Elul. Sa’ad da dukan abokan gābanmu suka ji haka, dukan al’umman da suke kewaye da mu suka ji tsoro, suka rasa ƙarfin halinsu, domin sun gane cewa wannan aiki an yi shi da taimakon Allahnmu ne. (Nehemiya 6:15-16)
Ga wannan zancen Yohanna ya amsa ya ce, “Mutum yakan karɓi kawai abin da aka ba shi ne daga sama. (Yohanna 3:27)

A ƙarshe Allah ne ke iko da ƙarin girma

Wadata da girma daga gare ka suke; kai ne mai mulkin dukan abubuwa. A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka. (1 Tarihi 29:12)
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗi a cikinka ya sa ka a kan kujerar sarautarsa a matsayin sarki don ka yi mulkin domin Ubangiji Allahnka. Saboda ƙaunar Allahnka wa Isra’ila da kuma sha’awarsa na riƙe su har abada, ya naɗa ka sarki a bisansu, don ka yi adalci da kuma gaskiya.” (2 Tarihi 9:8)
Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum. Amma Allah ne mai yin shari’a, yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani. (Zabura 75:6-7)
Ya, sarki, kai ne sarkin sarakuna. Allah na sama ya ba ka iko da girma da suna; a cikin hannunka ya sanya ɗan adam, da namun jeji da tsuntsayen sama. A duk inda suke zaune, ya maishe ka ka yi mulki a bisansu kai ne kan zinariyan nan na siffar. (Daniyel 2:37-38)
Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama. (Daniyel 5:21)

Allah zai iya ƙarfafa mutane su yi aiki

Saboda haka Ubangiji ya motsa zuciyar Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, wanda yake gwamna a Yahuda, da kuma zuciyar Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da kuma zukatan dukan raguwar jama’ar. Suka zo suka fara aiki a gidan Ubangiji Maɗaukaki, Allahnsu, (Haggai 1:14)

Hakkin mai ɗaukar aiki da na ma’aikaci

Hakkin mai ɗaukar aiki

Ka biya albashi mai adalci

“Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci, ɗakunansa na sama kuma ta hanyar rashin gaskiya, yana sa mutanen ƙasarsa suna aiki a banza ba ya biyansu wahalarsu. (Irmiya 22:13)
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. (Malaki 3:5)

Misalin cinikin albashi mai adalci

...sai Laban ya ce masa, “Don kawai kai dangina ne na kusa, sai kawai ka yi mini aiki a banza? Faɗa mini abin da albashinka zai zama.” (Farawa 29:15)
Ya ƙara da cewa, “Faɗa albashinka, zan kuwa biya shi.” (Farawa 30:28)

Hukunci ga waɗanda ba sa biyan albashi mai adalci

Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku. (Yaƙub 5:1)
Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe. Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki. (Yaƙub 5:3-4)

Misali da ke kwatanta biyan albashi mai adalci

“Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa. Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa. “Wajen sa’a ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome. Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’ Saboda haka suka tafi. “Ya sāke fita a sa’a ta shida da kuma sa’a ta tara, ya sāke yin haka. Wajen sa’a ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’ “Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ “Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’ “Sa’ad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira ma’aikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara daga waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’ “Ma’aikatan da ka ɗauka wajen sa’a ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda. Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda. Sa’ad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar. Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin sa’a ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’ “Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba? Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka. Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’ “Saboda haka fa, na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na ƙarshe.” (Mattiyu 20:1-16)

Ka biya ma’aikaci nan da nan

“ ‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace. “ ‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana. (Firistoci 19:13)
Kada ku zalunci ɗan ƙodago matalauci da mabukaci, ko da shi ɗan’uwanku ne mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a cikin garuruwanku. Ku biya kuɗin aikinsa kowace rana kafin fāɗuwar rana, domin shi matalauci ne, yana kuma sa rai a kan wannan hakkin ne, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har yă zama laifi a gare ku. (Maimaitawar Shari’a 24:14-15)

Ka yi adalci da gaskiya

Masu bayi, ku riƙe bayinku da kyau da kuma daidai, domin kun san cewa ku ma kuna da Ubangiji a sama. (Kolossiyawa 4:1)

Kada ka yi barazana, sai dai ka yi wa ma’aikaci hidima

Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba. Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce. Ku kuma masu bayi, dole ku bi da bayinku da kyau. Ku daina ba su tsoro. Ku tuna, ku da su, Maigida ɗaya kuke da shi a sama, kuma ba ya nuna bambanci. (Afisawa 6:7-9)

Ka saurari ƙorafin ma’aikata

“In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu, sa’ad da suke da damuwa da ni, me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni? Me zan ce lokacin da ya tambaye ni? Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba? (Ayuba 31:13-15)

Ka ba wa ma’aikaci isasshen hutu ko ka sha sakamako

Suna cewa, ‘Don me muka yi azumi, ba ka kuma gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, ba ka kuma lura da wannan ba?’ “Duk da haka a ranar azuminku, kuna yi yadda kuka ga dama kuna kuma zaluntar dukan ma’aikata. (Ishaya 58:3)

Idan mai ɗaukar aiki marar gaskiya ne, ma’aikata ma za su zama marasa gaskiya

In mai mulki yana sauraran ƙarairayi, dukan ma’aikatansa za su zama mugaye. (Karin Magana 29:12)

Kulawa ta musamman ga ma’aikata masu bi

“In ka sayi mutumin Ibraniyawa a matsayin bawa, zai bauta maka shekara shida. Amma a shekara ta bakwai, za ka ’yantar da shi, yă tafi ’yantacce, ba tare da ya biya kome ba. (Fitowa 21:2)
In ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa, namiji ko ta mace, ya sayar da kansa gare ka, ya kuma bauta maka shekaru shida, a shekara ta bakwai dole ka ’yantar da shi. Sa’ad da kuka sake shi, kada ku bar shi yă tafi hannu wofi. Ku ba shi kyautai hannu sake daga tumakinku, daga masussukarku, da kuma daga wurin matsewar inabinku. Ku ba shi yadda Ubangiji Allahnku ya albarkace ku. (Maimaitawar Shari’a 15:12-14)

An albarkaci mai ɗaukar aiki saboda ma’aikata masu ibada

Amma Laban ya ce masa, “In na sami tagomashi daga gare ka, ina roƙonka ka zauna. Na gane ta wurin duba cewa Ubangiji ya albarkace ni saboda kai.” (Farawa 30:27)
Daga lokacin da ya sa shi shugaban gidansa da kuma a kan dukan abin da yake da shi, sai Ubangiji ya albarkaci gidan mutumin Masar saboda Yusuf. Albarkar Ubangiji tana a kan kome da Fotifar yake da shi a gida da kuma a jeji. (Farawa 39:5)

Mai ɗaukar aiki mai aminci

Ban da haka ma, daga shekara ta ashirin ta Sarki Artazerzes, sa’ad da aka naɗa ni in zama gwamnansu a ƙasar Yahuda, har zuwa shekara ta talatin da biyu na mulkinsa, shekara sha biyu ke nan, ko ni, ko ’yan’uwana, ba wanda ya ci abincin da akan ba wa gwamna. (Nehemiya 5:14)
Amma gwamnonin farko, waɗanda suka riga ni, sun ɗaura wa mutane kaya mai nauyi suka karɓi shekel arba’in na azurfa daga gare su haɗe da abinci da kuma ruwan inabi. Har bayin masu mulki ma sun nawaya wa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda ina tsoron Allah. (Nehemiya 5:15)
A maimakon haka, na miƙa kaina ga aiki a kan wannan katanga. Na tattara dukan mutanena a can don aikin; ba mu samar wa kanmu wata gona ba. (Nehemiya 5:16)
Bugu da ƙari, Yahudawa da shugabanni ɗari da hamsin suna ci daga teburina, haka ma waɗanda suka zo wurinmu daga ƙasashen da suke kewaye. (Nehemiya 5:17)
Kowace rana akan shirya mini saniya ɗaya, zaɓaɓɓun tumaki shida da waɗansu kaji, kuma kowace kwana goma akan tanadar da ruwan inabi na kowane iri a yalwace. Duk da haka, ban taɓa nemi a ba ni abincin da akan ba wa gwamna ba, domin wahala ta yi wa jama’a yawa. (Nehemiya 5:18)

Mai ɗaukar aiki marar aminci

...ganin haka sai Masarawa suka ƙara musu wahala. Suka baƙanta wa Isra’ilawa rai da bauta mai wuya, ta wurin sa su yin tubali da yumɓu, da kuma kowace irin bauta a gonaki. A cikin dukan ayyukansu, Masarawa ba su ji tausayinsu ba ko kaɗan. (Fitowa 1:13-14)

Ka zaɓi ma’aikata da kyau

Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa. (Karin Magana 26:10)

Hakkin ma’aikata

Ka zama mai aminci

A kan haka, shugabannin nan uku da muƙaddasan nan suka yi ƙoƙari su sami wani laifi a kan Daniyel a yadda yake tafiyar da aikin shugabancinsa, amma ba su samu ba. Ba su same shi da wani laifin cin hanci ba, domin shi amintacce ne kuma babu wani aibi a kansa ko rashin kula. (Daniyel 6:4)

Ka bauta wa mai ɗaukar aiki mai ibada da ƙarin aminci

Waɗanda suke da iyayengiji masu bi, to, kada su yi musu reni domin su ’yan’uwa ne. A maimako, sai ma su fi bauta musu, saboda waɗanda suke cin moriyar hidimarsu masu bi ne, ƙaunatattu ne kuma a gare su. Waɗannan su ne abubuwan da za ka koya musu ka kuma gargaɗe su. (1 Timoti 6:2)

Nasara na iya zama sakamakon amincin ma’aikaci

Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya, kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansa. (Karin Magana 17:2)
Duk wanda ya lura da itacen ɓaure, zai ci ’ya’yansa, kuma duk wanda ya lura da maigidansa za a girmama shi. (Karin Magana 27:18)
Daniyel kuwa ya bunkasa a lokacin mulkin Dariyus da kuma mulkin Sairus na Farisa. (Daniyel 6:28)

Misalin ma’aikata masu aminci har ba a bukaci lissafi ba

Ba su bukaci wani bayani daga waɗanda aka ba wa kuɗin don su biya ma’aikatan ba, domin sun yi aikinsu da aminci. (2 Sarakuna 12:15)
Amma ba sa bukata su ba da bayanin kuɗin da aka danƙa musu domin suna aikinsu da aminci.” (2 Sarakuna 22:7)

Misalin ma’aikata masu aminci da ake kula da su

Mutanen fa suka yi aiki da aminci. Shugabanninsu, su ne Yahat da Obadiya, Lawiyawa zuriyar Merari da Zakariya da Meshullam, zuriyar Kohat. Dukan Lawiyawa waɗanda suke gwanaye a kayan kiɗi, (2 Tarihi 34:12)

Ma’aikaci mai aminci albarka ne ga mai ɗaukar aiki

Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi haka ɗan saƙo mai aminci wanda aka aika; ya wartsakar da ran waɗanda suka aike shi. (Karin Magana 25:13)

Ka yi biyayya ga mai ɗaukar aiki domin a zahiri kana bauta wa Ubangiji ne

Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin bangirma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi. Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su sa’ad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku. Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba. Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce. (Afisawa 6:5-8)
Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji. Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa. (Kolossiyawa 3:22-24)
Ka koya wa bayi su yi wa iyayengijinsu biyayya cikin kowane abu, su yi ƙoƙari su gamshe su, kada su mayar musu da magana, kada kuma su yi musu sata, sai dai su nuna za a iya amince da su sosai, don ta kowace hanya su sa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu ta zama abin ɗaukan hankali. (Titus 2:9-10)

Har ma sa’ad da kake aiki ga mai ɗaukar aiki marar hankali

Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku da matuƙar ladabi, ba kawai ga waɗanda suke da kirki da masu sauƙinkai ba, amma har ga masu zafin rai ma. Gama abin yabo ne in mutum ya yi haƙuri cikin zafin wahalar rashin adalci saboda yana sane da Allah. (1 Bitrus 2:18-19)

Ka girmama mai ɗaukar aikinka

Duk waɗanda suke ƙarƙashin bauta, ya kamata su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci girmamawa matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwarmu. (1 Timoti 6:1)
Ka koya wa bayi su yi wa iyayengijinsu biyayya cikin kowane abu, su yi ƙoƙari su gamshe su, kada su mayar musu da magana, (Titus 2:9)

Kada ka yi wa abokan aikinka ƙazafi

“Kada ka baza ƙarairayi game da bawa ga maigidansa, in ba haka ba, zai la’ance ka, za ka kuwa sha wahala a kan haka. (Karin Magana 30:10)

Ka gamsu da albashinka

Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.” (Luka 3:14)

Ka yi aiki da mutunci

...bayan an ɗan jima sai matar maigidansa ta fara sha’awar Yusuf, sai ta ce, “Zo ka kwana da ni!” Amma ya ƙi. Ya ce mata, “Ga shi kome yana a ƙarƙashina, don haka ne ma maigidana bai dami kansa da wani abu a cikin gidan nan ba; kome da ya mallaka, ya danƙa ga kulawata. Babu wani da ya fi ni a wannan gida. Maigidana bai hana ni kome ba sai ke, saboda ke matarsa ce. Yaya fa, zan yi irin wannan mugun abu, in yi zunubi wa Allah?” (Farawa 39:7-9)

Ƙa’idojin aiki da kasuwanci gaba ɗaya

Kada ka yi tarayyar kasuwanci da marasa bi

Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu? Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? Me ya haɗa mai bi da marar bi? Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? Gama mu haikalin Allah mai rai ne. Kamar yadda Allah ya ce, “Zan zauna tare da su, in yi tafiya a cikinsu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.” Saboda haka, “Sai ku fito daga cikinsu, ku keɓe kanku, in ji Ubangiji. Kada ku taɓa wani abu marar tsabta, zan kuma karɓe ku.” (2 Korintiyawa 6:14-17)

Ka gina kasuwanci kafin ka gina gida

Ka gama aikinka ka kuma shirya gonakinka; bayan haka, ka gina gidanka. (Karin Magana 24:27)

Aiki mai amfani yakan kawo ɗan rikici

Inda ba shanu, wurin sa wa dabbobi abinci zai kasance ba kome, amma daga ƙarfin saniya ce yalwar girbi kan fito. (Karin Magana 14:4)

Za a girmama mutane masu ƙwarewa

Kana ganin mutumin da yake da gwaninta a cikin aikinsa? Zai yi wa sarakuna hidima; ba zai yi hidima wa mutanen da ba su iya ba. (Karin Magana 22:29)

Kada ka yi taƙama da gobe a kasuwanci

Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.” Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace. A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan.” (Yaƙub 4:13-15)

Ka kula da sha’aninka kana aiki da hannuwanka

Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku, don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa. (1 Tessalonikawa 4:11-12)

Wani lokaci marasa ibada suna tsananta wa masu ibada don su kāre mugun kasuwanci

Wani maƙerin azurfa, mai suna Demetiriyus wanda yake ƙera siffar ɗakunan tsafin Artemis da azurfa, ba ƙaramin ciniki yake kawo wa mutane masu sana’an nan ba. Sai ya tara su wuri ɗaya, tare da masu irin wannan sana’ar ya ce, “Ku jama’a, kun san muna samun kuɗin shiga sosai daga wannan sana’a. Kuma kuna ji kuna gani yadda Bulus ɗin nan ya shawo kan mutane da yawa ya kuma sa suka bauɗe a nan a Afisa da dukan lardin Asiya. Yana cewa alloli da mutum ya ƙera ba alloli ba ne ko kaɗan. Akwai hatsari, ba kawai cewa sana’armu za tă rasa sunanta mai daraja ba, amma za a yi banza da ɗakin tsafin Artemis alliyarmu mai girma, alliyar kanta wadda ake bauta a ko’ina a yankin Asiya da kuma duniya, za a raba ta da darajarta.” Da suka ji haka, sai suka yi fushi ƙwarai suka fara ihu suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!” (Ayyukan Manzanni 19:24-28)

Ubangiji zai iya amfani da aiki domin ya ƙasƙantar da mu

...gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka. Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya; suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako. (Zabura 107:11-12)

Ana bukatar biya mai adalci domin kaya da hidima

“Don haka, ka ba da umarni a yanka mini itatuwan al’ul na ƙasar Lebanon. Ma’aikatana za su haɗa hannu da ma’aikatanka, ni kuwa zan biya ka albashin ma’aikatanka kamar yadda ka faɗa. Gama ka san cewa babu wani a cikinmu da ya iya yanka itacen katako kamar Sidoniyawa.” (1 Sarakuna 5:6)
...don su tanada mini katakai da yawa, domin haikalin da zan gina dole yă zama mai girma da kuma ƙasaitacce. Zan ba wa bayinka masu yankan katakai waɗanda suka yanka katako, garwa niƙaƙƙen alkama dubu ashirin, garwan sha’ir dubu ashirin da randunan ruwan inabi dubu ashirin da kuma randunan man zaitun dubu ashirin.” (2 Tarihi 2:9-10)

Misalin biya marar adalci

A ƙarshen shekaru ashirin da Solomon ya ɗauka yana gina haikalin Ubangiji da fadan sarki, sai Sarki Solomon ya ba wa Hiram sarkin Taya garuruwa ashirin a yankin Galili, gama Hiram ya tanada masa da dukan katakai al’ul da na fir, da kuma zinariyar da ya bukaci domin aiki. Amma sa’ad da Hiram ya zo daga Taya don yă ga garuruwan da Solomon ya ba shi, sai bai ji daɗi ba. (1 Sarakuna 9:10-12)

Ritaya

“Wannan ya shafi Lawiyawa ne, wato, mazan da suka kai shekara ashirin da biyar, ko fiye, za su zo su yi aiki a Tentin Sujada, amma in suka kai shekaru hamsin da haihuwa, dole su huta daga wannan aiki na yau da kullum, su kuma daina aiki. Za su iya taimakon ’yan’uwansu cikin tafiyar da ayyuka a Tentin Sujada, amma su kansu ba za su yi aikin ba. Haka fa za ka ba wa Lawiyawa aikinsu.” (Ƙidaya 8:24-26)

Mace mai kirki tana aiki tuƙuru kuma albarka ce ga gidanta

Wa yake iya samun mace mai halin kirki? Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai. Mijinta yana da cikakken amincewa da ita kuma ba ya rasa wani abu mai daraja. Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakin ranta. Takan zaɓi ulu da lilin ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki. Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne tana kawo abincinta daga nesa. Takan farka tun da sauran duhu; ta tanada wa iyalinta abinci ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi. Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta; daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi. Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru; hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta. Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare. Da hannunta take riƙe abin kaɗi ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta. Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata. Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta; gama dukansu suna da tufafi masu kauri. Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa; tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya. Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni inda yakan zauna a cikin dattawan gari. Takan yi riguna na lilin ta sayar; takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara. Ƙarfi da mutunci su ne suturarta; za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa. Tana magana da hikima, kuma umarnai mai aminci yana a harshenta. Tana lura da sha’anin gidanta kuma ba ta cin abincin ƙyuya. ’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka; haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa, (Karin Magana 31:10-28)
Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah. (Titus 2:4-5)

Neman abubuwan banza yana kawo talauci

Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne. (Karin Magana 12:11)
Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace, amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe. (Karin Magana 28:19)