Allah ne mai mallakar kome
Allah ne mai mallakar kome a duniya
...ya albarkaci Abram yana cewa, “Allah Mafi Ɗaukaka Mahaliccin sama da ƙasa yă albarkace Abram. (Farawa 14:19)
Amma Abram ya ce, wa sarkin Sodom, “Na ɗaga hannu ga Ubangiji Allah Mafi Ɗaukaka, Mahaliccin sama da ƙasa, na riga na rantse (Farawa 14:22)
Musa ya amsa, “To, da kyau, da zarar na fita daga birnin, zan yi addu’a ga Ubangiji, tsawar za tă tsaya, ƙanƙarar kuma za tă daina, don ku sani cewa duniya ta Ubangiji ce. (Fitowa 9:29)
Yanzu, in kuka yi mini cikakken biyayya, kuka kuma kiyaye yarjejjeniyata, to, za ku zama keɓeɓɓiyar taska a gare ni a cikin dukan al’ummai. Ko da yake duk duniya tawa ce, (Fitowa 19:5)
Sammai, har da sama sammai, da duniya, da kome da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne. (Maimaitawar Shari’a 10:14)
Girma da iko da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji, gama kome a sama da ƙasa naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji; an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka. “Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne. Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya. Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne. (1 Tarihi 29:11, 14-16)
Wane ne yake bi na bashi da dole in biya? Duk abin da yake ƙarƙashin sama nawa ne. (Ayuba 41:11)
Zabura ta Dawuda. Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta, duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta; (Zabura 24:1)
Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba, gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta. (Zabura 50:12)
Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne. (Zabura 82:8)
Sammai naka ne, haka kuma duniya; ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta. (Zabura 89:11)
A hannunsa ne zurfafan duniya suke, ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne. Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa. (Zabura 95:4-5)
Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka. (Zabura 104:24)
...gama “Duniya da duk abin da yake cikinta na Ubangiji ne.” (1 Korintiyawa 10:26)
Misali da ke kwatanta mallakar Allah
“Har wa yau, za a kwatanta shi da mutumin da zai yi tafiya, wanda ya kira bayinsa ya kuma danƙa musu mallakarsa. Ga guda, ya ba shi talenti biyar na kuɗi, ga wani talenti biyu, ga wani kuma talenti ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Sa’an nan ya yi tafiyarsa. Mutumin da ya karɓi talenti biyar, nan da nan ya tafi ya yi kasuwanci da su har ya sami ribar talenti biyar. Haka ma, wannan mai talenti biyu, shi ma ya yi riba biyu. Amma mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ɗin, ya tafi, ya tona rami, ya ɓoye kuɗin maigidansa. “Bayan an daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo, ya kuma daidaita lissafi da su. Mutumin da ya karɓi talenti biyar, ya kawo ƙarin talenti biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’ “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’ “Mutumin da yake da talenti biyu, shi ma ya zo ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’ “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’ “Sa’an nan mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan sha’ani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba. Saboda haka na ji tsoro, na je na ɓoye talentinka a ƙasa. Ga abinka.’ “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba? To, in haka ne, ai, da ka sa kuɗina a banki, don sa’ad da na dawo da na karɓi abina da riba. “ ‘Karɓi talentin daga hannunsa ku ba wanda yake da talenti goma. (Mattiyu 25:14-28)
Ubangiji ne ke riƙe da kome tare
Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama. (Ibraniyawa 1:3)
Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe. (Kolossiyawa 1:17)
Takamaiman abubuwan da Allah ya mallaka
Ƙasa
“ ‘Kada a sayar da gona ɗinɗinɗin, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi ne kawai, kuma ’yan haya nawa. (Firistoci 25:23)
Zinariya da azurfa
Kika kuma ɗauki kayan ado masu kyau da na ba ki, kayan adon da aka yi da zinariya da azurfa, kika yi wa kanki gumakan maza kika kuma yi ta yin karuwanci da su. (Ezekiyel 16:17)
‘Da zinariya da azurfa duka nawa ne,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. (Haggai 2:8)
Dabbobi
...gama kowace dabbar kurmi nawa ne, da kuma shanu a kan dubban tuddai. Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsu kuma halittun filaye nawa ne. (Zabura 50:10-11)
Allah ne ke iko da kowane al’amari
Ubangiji ne ke iko da dukan al’amura a duniya
Girma da iko da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji, gama kome a sama da ƙasa naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji; an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka. Wadata da girma daga gare ka suke; kai ne mai mulkin dukan abubuwa. A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka. (1 Tarihi 29:11-12)
Ubangiji yana yin abin da ya ga dama, a sammai da kuma a duniya, cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu. (Zabura 135:6)
Akan jefa ƙuri’a a kan cinya, amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne. (Karin Magana 16:33)
Ubangiji ne yake bi da matakan mutum, Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa? (Karin Magana 20:24)
Ya ce, “Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin; hikima da iko nasa ne. Yana sāke lokuta, yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu. Yana ba da hikima ga masu hikima kuma ilimi ga masu basira. (Daniyel 2:20-21)
Ubangiji yana barin yanayi mai wuya ya faru
Dukan ’yan’uwansa maza da mata da duk waɗanda suka san shi a dā suka zo suka ci abinci tare da shi a cikin gidansa. Suka ta’azantar da shi suka ƙarfafa shi game da duk wahalar da Ubangiji ya auka masa, kowannensu kuma ya ba shi azurfa da zobe na zinariya. (Ayuba 42:11)
...saboda daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta mutane za su san cewa babu wani in ban da ni. Ni ne Ubangiji, kuma babu wani. Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu, ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i; ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa. (Ishaya 45:6-7)
Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika in ba Ubangiji ne ya umarta ba? Ba daga bakin Maɗaukaki ne bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba? (Makoki 3:37-38)
Idan aka busa ƙaho a ciki birni mutane ba sa yin rawar jiki? Sa’ad da bala’i ya auko wa birni, ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba? (Amos 3:6)
Ubangiji yana amfani da kowane yanayi domin alheri a rayuwar masu ibada
Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. (Romawa 8:28)
Misalin Ubangiji ya bar yanayi mai wuya domin alheri na ƙarshe
Yanzu dai, kada ku damu, kada kuma ku yi fushi da kanku saboda kun sayar da ni a nan, gama Allah ya aiko ni gabanku ne don in ceci rayuka. Ga shi shekaru biyu ke nan ake yunwa a ƙasar, kuma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba. Amma Allah ya aiko ni gabanku ne don in adana muku raguwa a duniya, in kuma ceci rayukanku ta wurin ceto mai girma. “Saboda haka fa, ba ku ba ne kuka aiko ni nan, Allah ne. Ya mai da ni mahaifi ga Fir’auna, shugaban dukan gidansa da kuma mai mulkin dukan Masar. Yanzu sai ku gaggauta zuwa wurin mahaifina ku faɗa masa, ‘Abin da ɗanka Yusuf ya ce; Allah ya mai da ni shugaban dukan Masar. Gangaro wurina; kada ka jinkirta. (Farawa 45:5-9)
Ra’ayin mutumin jiki game da ikon al’amura
Na kuma ga wani abu a duniya. Ba kullum maguji ne yake nasara a tsere ba, ba kullum jarumi ne yake yin nasara ba, ba kullum mai hikima ne da abinci ba ba kullum mai basira ne yake da wadata ba ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba; amma sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu. (Mai Hadishi 9:11)
Takamaiman al’amura da abubuwan da Ubangiji ke iko da su
Ubangiji yana bi da zukatan mutane
A hannun Ubangiji zuciyar sarki kamar ruwan rafi ne wanda yake bi da shi duk inda ya so. (Karin Magana 21:1)
Ubangiji zai iya sa masu ibada su sami tagomashi a gaban wasu
Ubangiji ya kasance tare da shi; ya nuna masa alheri, ya kuma sa ya sami tagomashi a idanun mai gadin kurkukun. (Farawa 39:21)
Suka yi kwana bakwai suna Bikin Burodi Marar Yisti, suna cike da farin ciki, gama Ubangiji ya cika su da farin ciki don ya sa sarkin Assuriya ya canja tunaninsa, ya taimake su cikin aikin gidan Allah, Allah na Isra’ila. (Ezra 6:22)
A kuma ba ni wasiƙa zuwa ga Asaf, sarkin daji, yă ba ni katako don yin ƙofofin kagara na kusa da fadar haikali da kuma don katangar birni, da na wurin da zan zauna?” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni. Na kuma faɗa musu game da yadda alherin Allahna yake tare da ni da kuma abin da sarki ya faɗa mini. Suka amsa, suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Sai suka fara wannan aiki mai kyau. (Nehemiya 2:8, 18)
Misalin Isra’ilawa sun washe Masarawa
“Zan kuma sa mutanen su sami tagomashi daga wurin Masarawa, saboda sa’ad da za ku fita, ba za ku fita hannu wofi ba. Kowace mace ta tambayi maƙwabciyarta, da kuma duk wata macen da take cikin gidanta, kayayyakin azurfa da na zinariya da kuma na riguna, waɗanda za ku sa wa ’ya’yanku maza da mata. Ta haka nan za ku washe Masarawa.” (Fitowa 3:21-22)
Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Musa ya umarce su, suka roƙi Masarawa kayan adonsu na azurfa da na zinariya, da kuma tufafi. Ubangiji kuwa ya sa Isra’ilawa suka yi farin jini a wurin Masarawa, Masarawa kuma suka saki hannu wa mutanen, suka ba su duk abin da suka roƙa; ta haka Isra’ilawa suka washe Masarawa. (Fitowa 12:35-36)
Ubangiji yana sa wasu mutane su taurare
Zan kuma taurare zuciyar Fir’auna, zai kuwa bi su. Na shirya wannan domin in nuna ɗaukakata a bisa Fir’auna da ƙungiyar sojansa. Bayan wannan, mutanen Masar za su sani ni ne Ubangiji.” Sai Isra’ilawa suka yi haka. (Fitowa 14:4)
Amma Sihon sarkin Heshbon ya ƙi yă bar mu mu wuce a ciki. Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruhunsa ya taurare don yă ba da shi a hannuwanku kamar yadda ya yi yanzu. (Maimaitawar Shari’a 2:30)
Ubangiji yana iko da ƙyashin zuciya
Sau uku a shekara, dukan mazanku za su bayyana a gaban Ubangiji Mai Iko Duka, Allah na Isra’ila. Zan kore al’umma daga gabanku, in fadada kan iyakarku, babu wanda zai yi ƙyashin ƙasarku a lokutan nan uku na shekara da kuka haura don ku bayyana a gaban Ubangiji, Allahnku. (Fitowa 34:23-24)
Ubangiji yana iko da al’ummai
Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance. (Ayyukan Manzanni 17:26)
Amma mutumin Allah ya zo wurinsa ya ce, “Ya sarki, waɗannan runduna daga Isra’ila ba za su tafi tare da kai ba, gama Ubangiji ba ya tare da Isra’ila, ba ya nan da wani cikin mutanen Efraim. Ko da ma ya tafi ya yi faɗa da ƙwazo a cikin yaƙi, Allah zai tumɓuke shi a gaban abokan gāba, gama Allah yana da iko yă taimaka ko yă tumɓuke.” Amaziya ya tambayi mutumin Allah ya ce, “Amma game da talenti ɗarin da na biya saboda waɗannan rundunonin Isra’ila fa?” Mutumin Allah ya amsa, “Ubangiji zai ba ka fiye da wannan.” (2 Tarihi 25:7-9)
“Kaiton Assuriya, sandar fushina, a hannun da kulkin fushina yake! Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah, na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi, don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima, yă tattake su kamar laka a tituna. (Ishaya 10:5-6)