Cin amanar Yesu
Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin. (Mattiyu 26:14-15)
Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin. Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.” Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.” Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Sa’an nan ya je ya rataye kansa. Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin ma’aji, da yake kuɗin jini ne.” Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi. Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yă zuwa yau. Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Isra’ila suka sa a kansa, suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.” (Mattiyu 27:3-10)
Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su. Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi. (Markus 14:10-11)
Shaiɗan kuwa ya shiga Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun. Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su. Suka kuwa yi murna, suka yarda su ba shi kuɗi. (Luka 22:3-5)
(Da ladar da ya samu saboda muguntarsa Yahuda ya sayi wani fili; a can ya fāɗi da kā, jikinsa ya fashe, hanjinsa kuma duk suka zubo. (Ayyukan Manzanni 1:18)
An sayar da ɗan’uwa zuwa bauta
Saboda haka sa’ad da Fataken Midiyawa suka iso, sai ’yan’uwansa suka ja Yusuf daga rijiyar, suka sayar da shi a bakin shekel ashirin na azurfa wa mutanen Ishmayel, waɗanda suka ɗauke shi zuwa Masar. (Farawa 37:28)
Kuɗin da aka biya don duba
Sai dattawan Mowab da na Midiyawa suka tashi, suka ɗauki kuɗi don duba. Da suka zo wurin Bala’am sai suka faɗa masa abin da Balak ya ce. (Ƙidaya 22:7)
Amma Bala’am ya amsa musu ya ce, “Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba. (Ƙidaya 22:18)
‘Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba, kuma dole in faɗa abin da Ubangiji ya ce ne kawai’? (Ƙidaya 24:13)
Kuɗin da aka bayar don yunƙurin hallaka Yahudawa
In ya gamshi sarki, bari a yi doka, don a hallaka su, zan kuma sa talenti dubu goma na azurfa a cikin ma’ajin fada saboda mutanen da suka aikata wannan sha’ani.” Saboda haka sarki ya zare zoben hatimi daga yatsarsa, ya ba wa Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban Yahudawa. Sarki ya ce wa Haman, “Ka riƙe kuɗin, ka kuma yi da mutanen yadda ka ga dama.” (Esta 3:9-11)
Mordekai ya faɗa masa duk abin da ya faru da shi, haɗe da yawan kuɗin da Haman ya yi alkawari zai zuba a ma’ajin fada don a hallaka Yahudawa. (Esta 4:7)
Kuɗin da aka biya don a cutar da Samson
Bayan ɗan lokaci, sai ya shiga ƙaunar wata mace, mai suna Delila a Kwarin Sorek. Sai shugabannin Filistiyawa suka tafi wurinta suka ce, “Ki yi ƙoƙari ki ga ko za ki rarrashe shi yă nuna miki asirin ƙarfinsa da yadda za mu iya shan ƙarfinsa don mu ɗaura shi mu yi nasara a kansa. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu ɗari ɗaya na azurfa.” (Mahukunta 16:4-5)
Da Delila ta gane ya gaya mata kome yanzu, sai ta aika saƙo zuwa ga shugabannin Filistiyawa ta ce, “Ku ƙara zuwa sau ɗayan nan, ai, ya gaya mini kome.” Saboda haka shugabannin Filistiyawa suka dawo tare da azurfa a hannuwansu. (Mahukunta 16:18)
Kuɗin da aka biya don kisa
Suka ba shi shekel saba’in na azurfa daga haikalin Ba’al-Berit, Abimelek kuwa ya yi amfani da shi ya yi hayar ’yan tauri waɗanda suka zama masu binsa. (Mahukunta 9:4)