An umarce mu kada mu yi ƙyashi
Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.” (Fitowa 20:17)
Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi sha’awar gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko bayinsa maza da mata, ko saniyarka, ko jakinsa, ko dai wani abin da yake na maƙwabtanka.” (Maimaitawar Shari’a 5:21)
Ku ƙone siffar allolinsu da wuta. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariyar da aka rufe allolin da ita, Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku. (Maimaitawar Shari’a 7:25)
An yi barazanar hukunci saboda ƙyashi
Amma, ba za ku ɗauki wani abin da za a hallaka ba, idan kuka yi haka, za ku jawo masifa da hallaka a kan mutanen Isra’ila a inda kuka sauka. (Yoshuwa 6:18)
Taku ta ƙare, ku da kuke shirya makirci, ku da kuke ƙulle-ƙullen mugunta a kan gadonku! Da gari ya waye sai ku fita ku aikata mugunta domin ikon aikatawa yana hannunku. Kukan yi ƙyashin gonaki ku kuma ƙwace su, ku yi ƙyashin gidaje ku kuma ƙwace. Kukan zalunci mutum, ku ƙwace masa gidansa, har ku ƙwace masa gādonsa. Saboda haka, Ubangiji ya ce, “Ina shirya wa waɗannan mutane bala’i, yadda ba za ku iya ceton kanku ba. Ba za ku ƙara tafiya kuna taƙama ba, gama zai zama lokacin bala’i ne. (Mika 2:1-3)
Misalin hukunci saboda ƙyashi
Isra’ilawa sun yi zunubi, sun karya sharaɗin da na yi musu. Sun ɗauki waɗansu abubuwan da aka keɓe; sun yi sata, sun yi ƙarya, sun ɓoye su cikin kayansu. Shi ne ya sa Isra’ilawa suka kāsa yin tsayayya da abokan gābansu; suka juya suka gudu domin za a hallaka su. Ba zan sāke kasancewa tare da ku ba sai in kun hallaka duk abin da aka keɓe don hallaka. “Tashi, ka je ka tsarkake mutane. Ka ce musu su tsarkake kansu, su yi shiri domin gobe; gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, a cikinku akwai abubuwan da aka keɓe, ya Isra’ilawa. Ba za ku iya yin tsayayya da abokan gābanku ba sai in kun rabu da abubuwan nan da aka haramta. “ ‘Da safe ku zo kabila-kabila. Kabilar da Ubangiji ya ware, za tă zo gaba gida-gida; gidan da Ubangiji ya ware, za su zo gaba iyali-iyali. Iyalin kuma da Ubangiji ya ware, za su zo gaba mutum bayan mutum. Mutumin da aka same shi da haramtattun abubuwan kuwa za a ƙone shi, duk da mallakarsa domin ya karya sharaɗin da Ubangiji ya yi muku, ya yi abin kunya a Isra’ila!’ ” Kashegari da sassafe Yoshuwa ya sa Isra’ilawa suka fito kabila-kabila, aka ware kabilar Yahuda. Gidan Yahuda suka zo gaba, sai aka ware gidan Zera, aka sa suka fito iyali-iyali, sai aka ware Zabdi. Yoshuwa kuwa ya sa iyalin Zabdi suka fito mutum-mutum, sai kuwa aka ware Akan ɗan Karmi, ɗan Zimri, ɗan Zera na kabilar Yahuda. Sai Yoshuwa ya ce wa Akan, “Ɗana, sai ka ba Ubangiji, Allah na Isra’ila ɗaukaka, ka yi masa yabo. Ka gaya mini abin da ka yi; kada ka ɓoye mini.” Akan kuwa ya amsa ya ce, “Gaskiya ne! Na yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila zunubi. Ga abin da na yi. A cikin ganimar, na ga doguwar riga mai kyau irin ta Babilon, da shekel ɗari biyu na azurfa, da kuma sandan zinariya mai nauyin shekel hamsin, sai raina ya so su, na kuwa kwashe su. Na tona rami a cikin ƙasa a tentina; na ɓoye.” Sai Yoshuwa ya aiki ’yan aika suka tafi da gudu zuwa tenti ɗin, haka kuwa suka same su a ɓoye a tentinsa, da azurfa a ƙarƙashi. Suka kwashe kayan daga tenti ɗin suka kawo wa Yoshuwa da sauran Isra’ilawa, suka baza su a gaban Ubangiji. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka ɗauki Akan ɗan Zera, da azurfar, doguwar rigar, sandan zinariya, ’ya’yansa maza da mata, shanunsa, jakuna da tumaki, tentinsa da duk abin da yake da shi, suka kai su Kwarin Akor. Yoshuwa ya ce, “Me ya sa ka jawo mana wahala haka? Ubangiji zai kawo maka wahala kai ma a yau.” Sai dukan Isra’ilawa suka jajjefe shi, bayan da suka gama jifarsa sai suka ƙone sauran. (Yoshuwa 7:11-25)
Misalan ƙyashi da aka bayar domin koya mana
To, waɗannan abubuwa misalai ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi. (1 Korintiyawa 10:6)
Masu ƙyashi ba za su gāji Mulkin Allah ba
Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. (1 Korintiyawa 6:9-10)
Mai ƙyashi mai bautar gumaka ne
Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba. (Afisawa 5:3)
Ku dai tabbata, ba wani mai fasikanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah. (Afisawa 5:5)
Kada ka yi tarayya da mai bi mai ƙyashi
Na rubuta muku cikin wasiƙata, kada ku yi haɗa kai da masu aikin lalata. Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya. Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum. (1 Korintiyawa 5:9-11)
Misalin mai ibada da bai yi ƙyashi ba
Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba. (Ayyukan Manzanni 20:33)
Allah zai iya iko da ƙyashi
Sau uku a shekara, dukan mazanku za su bayyana a gaban Ubangiji Mai Iko Duka, Allah na Isra’ila. Zan kore al’umma daga gabanku, in fadada kan iyakarku, babu wanda zai yi ƙyashin ƙasarku a lokutan nan uku na shekara da kuka haura don ku bayyana a gaban Ubangiji, Allahnku. (Fitowa 34:23-24)
An yi amfani da ƙyashi don kwatanta aikin Shari’a
Me za mu ce ke nan? Dokar zunubi ce? Sam, ko kaɗan! Tabbatacce ai, da ban san mene ne zunubi ba in ba ta wurin doka ba. Gama da ban san mene ne ƙyashi yake ba tabbatacce in ba don doka ta ce, “Kada ka yi ƙyashi ba.” Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne. (Romawa 7:7-8)