Kasuwanci
Suka yi jigilar kekunan yaƙi daga Masar a bakin shekel ɗari shida na azurfa, doki ɗaya kuma a kan ɗari da hamsin. Sun kuma yi jigilarsu suna sayarwa ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa. (1 Sarakuna 10:29)
“Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” In ji mai saya; sa’ad da ya tafi yana taƙama a kan ya iya ciniki. (Karin Magana 20:14)
Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.” Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace. A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan.” (Yaƙub 4:13-15)
Sakamakon zina ga kuɗi
...don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam. (Karin Magana 5:10)
Ba zai karɓi duk wata biya ba; zai ƙi cin hanci, kome yawansu. (Karin Magana 6:35)
Duk mai ƙaunar hikima kan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wanda yake ma’amala da karuwai kan lalatar da dukiyarsa. (Karin Magana 29:3)
Zuciyar mutum
Kada ka ci abincin mai rowa, kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi; gama shi wani irin mutum ne wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin. Zai ce maka, “Ci ka sha,” amma zuciyarsa ba ta tare da kai. Za ka yi amai ɗan abin da ka ci dukan daɗin bakinka kuwa zai tafi a banza. (Karin Magana 23:6-8)
Mutanena sukan zo wurinka, yadda suka saba su zauna a gabanka don su saurari maganarka, amma ba sa aiki da abin da suka ji. Da bakunansu suna nuna ƙauna, amma zukatansu cike da haɗama suke don ƙazamar riba. (Ezekiyel 33:31)
Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya. Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma. Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki. (Yaƙub 3:14-16)
Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba. Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku. (Yaƙub 4:2-3)
Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci. (2 Bitrus 2:3)
Dokar Tsohon Alkawari game da aure
In ba ka jin daɗinta, ka bar tă tafi inda take so. Ba za ka sayar da ita ko ka yi da ita kamar baiwa ba, da yake ka ƙasƙantar da ita. (Maimaitawar Shari’a 21:14)
Wasu ba su damu da kuɗi ba
Duba, zan zuga mutanen Medes su yi gāba da su, su da ba su kula da azurfa ba kuma ba sa damuwa da zinariya. (Ishaya 13:17)
Gibeyonawa suka ce, “Ba mu da ’yanci mu nemi zinariya ko azurfa daga wurin Shawulu ko gidansa, ba mu kuwa da wani ’yanci mu sa a kashe wani a Isra’ila.” Dawuda ya ce, “To, me kuke so in yi muku?” (2 Sama’ila 21:4)
Dabam-dabam
Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji yă albarkace ki ’yata. Wannan alheri ya fi wannan da kika nuna da farko. Ba ki gudu kin bi saurayi, mai arziki ko matalauci ba. (Rut 3:10)
Mutane kan la’anci mai ɓoye hatsi yana jira ya yi tsada, amma albarka kan zauna a kan wanda yake niyya ya sayar. (Karin Magana 11:26)
Gara ka zama kai ba kome ba ne amma kana da bawa da ka mai da kanka kai wani ne alhali kuwa ba ka da abinci. (Karin Magana 12:9)
Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita; ka nemi hikima, horo da fahimi. (Karin Magana 23:23)
Aka yi jana’izarsa tare da mugaye, aka binne shi tare da masu arziki, ko da yake bai taɓa yin wani tashin hankali ba, ko a sami ƙarya a bakinsa. (Ishaya 53:9)
Sa’an nan ya ce musu, “Saboda haka duk malamin dokokin da ya horu game da koyarwar mulkin sama, yana kama da maigida wanda yakan fitar daga ɗakin ajiyarsa sababbin dukiya da kuma tsofaffi.” (Mattiyu 13:52)
A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini. Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni. (Markus 5:25-26)
Sai shugaban ƙungiyar sojan ya ce, “Sai da na biya kuɗi mai yawa kafin in zama ɗan ƙasa.” Bulus ya ce, “Ni kuwa an haife ni ɗan ƙasa.” (Ayyukan Manzanni 22:28)
Kada ka ci masu adalci tara
Ba shi da kyau a hukunta marar laifi, ko a bulale shugaba saboda mutuncinsu. (Karin Magana 17:26)
Hukunce-hukuncen Ubangiji
A wannan rana, a kowane wuri inda akwai kuringa dubu da kuɗinsu ya kai shekel dubu na azurfa, ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne kawai za su kasance a can. (Ishaya 7:23)
Duk da haka za a keɓe ribarta da kuɗin shigarta wa Ubangiji; ba za a yi ajiyarsu ko a ɓoye su. Ribarta za tă tafi ga waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada, don su sami yalwataccen abinci da tufafi masu kyau. (Ishaya 23:18)
Almasihu zai yi nasara
Duba, bawana zai aikata abubuwa da hikima; za a tā da shi a kuma ɗaga shi da ɗaukaka ƙwarai. (Ishaya 52:13)
Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala, kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi, zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai, nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa. (Ishaya 53:10)
Ba za a iya sayen dangantaka da Ubangiji ba
“Ku zo, dukanku masu jin ƙishi, ku zo wurin ruwaye; ku kuma da ba ku da kuɗi, ku zo, ku saya ku kuma ci! Ku zo, ku saya ruwan inabi da madara ba tare da kuɗi ba ba za ku kuma biya kome ba. Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba, ku kuma yi wahala a kan abin da ba za ku ƙoshi ba? Ku saurara, ku saurare ni, ku kuma ci abin da yake da kyau, ranku kuma zai ji daɗin abinci mafi kyau. (Ishaya 55:1-2)
An daidaita rashin aminci da karuwanci
Kowace karuwa kan karɓi kuɗi, amma kina ba da kyautai ga dukan kwartayenki, kina ba su cin hanci don su zo wurinki daga ko’ina don alherai marasa ƙa’ida. Saboda haka cikin karuwancinki kin sha bamban da saura; babu wanda yake binki saboda alheranki. Ke dai dabam ce, gama kikan biya kuma ba mai biyanki. (Ezekiyel 16:33-34)
Dokoki game da firistoci da ƙasa
Ba za su sayar da shi ko su musayar da wani sashensa ba. Wannan shi ne mafi kyau na ƙasar ba kuma za a jinginar da ita ga wani ba, gama mai tsarki ce ga Ubangiji. (Ezekiyel 48:14)
Marasa ibada ba su ɗauki Ubangiji da daraja ba
Na faɗa musu cewa, “In kun ga ya fi kyau, ku biya ni; in kuwa ba haka ba, ku riƙe.” Saboda haka suka biya ni azurfa talatin. Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji. (Zakariya 11:12-13)
Za a ƙara wa wanda yake da shi; za a karɓe dukan abin wanda ba shi da shi
Ya ci gaba da cewa, “Ku lura da abin da kuke ji da kyau. Mudun da ka auna da shi, da shi za a auna maka, har ma a ƙara. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda kuma ba shi da shi, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe daga gare shi.” (Markus 4:24-25)
An yi amfani da kuɗi don kwatanta farin cikin mala’iku game da ceto
“Ko kuwa in wata mace tana da kuɗi na azurfa guda goma, sa’an nan ɗaya ya ɓata, ashe, ba za tă ƙuna fitila, ta share gidan, ta nema a hankali, har sai ta samu ba? In ta same shi, sai ta kira ƙawayenta da maƙwabtanta wuri ɗaya, ta ce musu, ‘Ku taya ni murna, na sami kuɗina da ya ɓata.’ Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.” (Luka 15:8-10)
Ra’ayin mallaka a ikilisiyar farko
Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare. Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa. (Ayyukan Manzanni 2:44-45)
Dukan masu bi kuwa zuciyarsu ɗaya ne, nufinsu kuwa ɗaya. Babu wani da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, amma sun raba kome da suke da shi. Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka. Babu mabukata a cikinsu. Lokaci-lokaci waɗanda suke da gonaki ko gidaje sukan sayar da su, su kawo kuɗi daga abin da suka sayar, su ajiye a sawun manzannin, a kuma raba wa kowa gwargwadon bukatarsa. Yusuf, wani Balawe daga Saifurus, wanda manzanni suke kira Barnabas (wanda yake nufin Ɗan Ƙarfafawa) ya sayar da wata gonar da ya mallaki ya kuma kawo kuɗin ya ajiye a sawun manzanni. (Ayyukan Manzanni 4:32-37)
Mutanen da suka san Ubangiji suna barin mugayen abubuwa masu tsada
Da yawa cikin waɗanda suka gaskata yanzu suka zo a fili suka furta mugayen ayyukansu. Waɗansu masu yin sihiri suka kawo naɗaɗɗun littattafansu wuri ɗaya suka kuwa ƙone su a gaban jama’a. Sa’ad da aka lissafta yawan kuɗin naɗaɗɗun littattafan nan, sai jimillar ta kai darik dubu hamsin. (Ayyukan Manzanni 19:18-19)
Kuɓutarwa
Ga Saratu kuwa ya ce, “Ina ba wa ɗan’uwanki shekel dubu na azurfa, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa cewa ba ki da laifi.” (Farawa 20:16)
Ganima, washe
Sa’an nan ’ya’yan Yaƙub maza suka bi kan gawawwakin, suka washe arzikin birni saboda an ɓata ’yar’uwarsu. Suka kwashe garkunansu na shanu da jakuna, da kuma kome na mutanen a birnin da kuma cikin gonaki. Suka kwashe dukan dukiyarsu da dukan matansu da ’ya’yansu, suka kwashe kome da yake cikin gidaje. (Farawa 34:27-29)
Da Isra’ilawa suka komo daga bin Filistiyawa sai suka washe sansanin Filistiyawa. (1 Sama’ila 17:53)
Ben-Hadad sarkin Aram kuwa ya tattara mayaƙansa gaba ɗaya. Sarakuna talatin da biyu suka tafi tare da shi haɗe da dawakansu da kekunan yaƙinsu. Ya haura ya yi wa Samariya kwanto, ya kuma yaƙe ta. Ya aika da ’yan aika zuwa cikin birnin wurin Ahab sarkin Isra’ila yana cewa, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce, ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne. Mafi kyau cikin matanka da ’ya’yanka nawa ne.’ ” Sarkin Isra’ila ya amsa, ya ce, “Kamar dai yadda ka faɗa, ranka yă daɗe, sarki. Ni da dukan abin da nake da shi, naka ne.” Sai ’yan aikan suka sāke dawo suka ce, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce, ‘Na aika ka ba da azurfarka da zinariyarka, matanka da kuma ’ya’yanka. Amma war haka gobe zan aika shugabannina su bincika fadanka da kuma gidajen shugabanninka. Za su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi.’ ” Dattawa da dukan mutane suka amsa, suka ce, “Kada ka saurare shi ko ka yarda da abin da yake bukata.” (1 Sarakuna 20:1-6, 8)
Isra’ila suka fatattaki Yahuda, kowa kuwa ya tsere zuwa gidansa. Ya kwashi ɗaukan zinariya da azurfa da duk kayan da aka samu a haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin fadan. Ya kuma kwashi bayi sa’an nan ya koma Samariya. (2 Sarakuna 14:12, 14)
Sa’ad da Yehoshafat da jama’arsa suka je kwasar ganima, sai suka sami shanu masu yawan gaske, da kayayyaki, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka yi ta kwasa har suka gaji. Kwana uku suka yi suna kwasar ganimar saboda yawanta. (2 Tarihi 20:25)
Tun daga zamanin kakanninmu har zuwa yanzu, zunubanmu suna da yawa. Domin zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu aka kama mu, aka wulaƙanta mu, muka zama bayi a hannun sarakuna waɗansu ƙasashe. (Ezra 9:7)
Dokar sarki ta ba wa Yahudawa a kowace birni izini su taru, su kuma kāre kansu, domin su hallaka, su kashe, su kuma hallaka kowace ƙungiyar mayaƙa, na kowace ƙasa, ko lardi, da wataƙila za su kai musu, da matansu, da yaransu hari; su kuma washe mallakar abokan gābansu. (Esta 8:11)
Yahudawa suka karkashe dukan abokan gābansu da takobi, suka karkashe waɗanda suka ƙi jininsu, suka kuma hallaka su yadda suka ga dama. ’ya’ya maza goma na Haman ɗan Hammedata, abokin gāban Yahudawa. Amma ba su taɓa dukiyarsu ba. (Esta 9:5, 10)
“Kaiton Assuriya, sandar fushina, a hannun da kulkin fushina yake! Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah, na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi, don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima, yă tattake su kamar laka a tituna. (Ishaya 10:5-6)
Sa’ad da Ubangiji ya gama dukan aikinsa gāba da Dutsen Sihiyona da Urushalima, zai ce, “Zan hukunta sarkin Assuriya saboda fariya na gangancin zuciyarsa da kuma kallon reni na idanunsa. Gama ya ce, “ ‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan, da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi. Na kau da iyakokin ƙasashe, na washe dukiyarsu; a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu. Kamar yadda mutum yakan miƙa hannu cikin sheƙar tsuntsu haka hannuna ya je ya washe dukiyar al’ummai; kamar yadda mutane sukan tattara ƙwai, haka na tattara dukan ƙasashe; ba tsuntsun da ya kakkaɓe fikafiki, ko yă buɗe baki don yă yi kuka.’ ” (Ishaya 10:12-14)
Za su washe dukiyarki, kayan cinikinki kuma su zama ganima; za su rurrushe katangarki su ragargaza gidajenki masu kyau su kuma zubar da duwatsunki, katakanki da kuma tarkacenki a cikin teku. (Ezekiyel 26:12)
Takobi zai zo a kan Masar, azaba za tă zo a kan Kush. Sa’ad da kisassu za su fāɗi a Masar, za a kwashe dukiyarta a tafi a rushe harsashinta. (Ezekiyel 30:4)
...ko da ma ya ci gaba cikin ’yan’uwansa. Iskar gabas daga Ubangiji za tă zo, tana hurawa daga hamada; maɓulɓularsa za tă kafe rijiyarsa kuma ta bushe. Za a kwashi kaya masu daraja na ɗakin ajiyarsa ganima. (Hosiya 13:15)
Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Abokin gāba zai ƙwace ƙasar, zai saukar da mafakarku, zai washe kagarunku.” (Amos 3:11)
Bai kamata ki bi ta ƙofofin mutanena a ranar bala’insu ba, ko ki rena su a cikin masifarsu a ranar bala’insu, ko ki ƙwace dukiyarsu a ranar bala’insu ba. (Obadiya 1:13)
Amma za a washe Isuwa ƙaƙaf, a kuma yaye ɓoyayyiyar dukiyarsa! A ranan nan kin tsaya kawai kina zuba ido yayinda baƙi suke washe dukiyar ɗan’uwanki, baƙi kuma suka shiga ta ƙofofinsa suka jefa ƙuri’a don a rarraba Urushalima, kin tsaya kina kallo kamar ɗaya daga cikin abokan gābansa. (Obadiya 1:6, 11)
“Ki tashi ki yi sussuka, ya Diyar Sihiyona, gama zan ba ki ƙahonin ƙarfe; zan ba ki kofatan tagulla domin ki ragargaje al’ummai masu yawa.” Za ki ba Ubangiji dukan dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba, wadatarsu kuma ga Ubangiji dukan duniya. (Mika 4:13)
A washe azurfa; a washe zinariya; dukiyarsu ba ta da iyaka, arzikinsu kuma ba ya ƙarewa. Ta zama wofi, an washe ta, an tuɓe ta! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa, jikuna suna rawa, fuskoki duk sun kwantsare! (Nahum 2:9-10)
Kaiton birni mai zub da jini, wadda take cike da ƙarairayi, cike da ganima, wadda ba a rasa masu fāɗawa cikin wahala! (Nahum 3:1)
“Dukansu ba za su yi masa tsiya, suna yin masa ba’a da dariya ba, suna cewa, “ ‘Kaito ga wannan wanda ya tara wa kansa kayan sata ya kuma wadatar da kansa da kayan ƙwace! Har yaushe wannan abu zai ci gaba?’ Masu binka bashi ba za su taso maka nan da nan ba? Ba za su farka su sa ka fargaba ba? Ta haka ka zama ganima a gare su. Domin ka washe al’ummai masu yawa, mutanen da suka rage za su washe ka. Domin ka zub da jinin mutane; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu. (Habakkuk 2:6-8)
Ku yi kururuwa, ku da kuke zaune a yankin kasuwa; za a hallaka dukan ’yan kasuwanku, dukan waɗanda suke kasuwanci da azurfa za su lalace. Za a washe dukiyarsu, a rurrushe gidajensu. Za su gina gidaje amma ba za su zauna a ciki ba; za su shuka inabi amma ba za su sha ruwansa ba.” Azurfarsu ko zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba a ranar fushin Ubangiji.” A cikin zafin kishinsa za a hallaka dukan duniya gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya nan da nan. (Zefaniya 1:11, 13, 18)
Saboda haka, muddin ina raye,” in ji Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, “tabbatacce Mowab za tă zama kamar Sodom, Ammonawa kuma kamar Gomorra, ƙasa mai ciyayi da rammukan gishiri, ƙasa marar amfani har abada. Raguwar mutanena za su washe su; waɗanda suka rage na al’ummata za su gāda ƙasarsu.” (Zefaniya 2:9)
Salon rayuwa
Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. Amma ya yi kyau dai a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu. Wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara da yawa, bai tara fiye da bukatarsa ba, wanda kuma ya tara kaɗan, bai kāsa masa ba.” (2 Korintiyawa 8:13-15)
Ina kuma so mata su lura su yi wa kansu adon da ya cancanta, da rigunan da suka dace, ba da adon kitso ko sa kayan zinariya ko lu’ulu’u ko kuma tufafi masu tsada ba, (1 Timoti 2:9)
Mayar da abin da aka ɗauka
“Idan mutane suka yi faɗa, ɗayan ya jefa ɗayan da dutse, ko ya naushe shi amma bai mutu ba, sai dai ya yi ta jiyya, idan mutumin ya sāke tashi ya yi tafiya ko da yana dogarawa da sanda ne, wanda ya buge shi zai kuɓuta, sai dai zai biya diyyar lokacin da ya ɓata masa, yă kuma lura da shi, har yă warke sarai. (Fitowa 21:18-19)
“Idan mutum biyu suna faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka za a biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara. (Fitowa 21:22)
“In bijimi ya kashe namiji ko ta mace, dole a jajjefe bijimin har yă mutu, ba za a kuma ci namansa ba. Amma mai bijimin ba shi da laifi. In, har an san bijimin da wannan hali, an kuma yi wa mai shi gargaɗi, amma bai ɗaura shi ba, har ya kashe namiji ko ta mace, za a jajjefe bijimin tare da mai shi, har su mutu. Amma fa, in an bukace shi yă biya, zai biya don yă fanshi ransa ta wurin biyan abin da aka aza masa. (Fitowa 21:28-30)
In bijimin ya kashe bawa ko baiwa, mai shi zai biya shekel talatin na azurfa wa maigidan bawan, a kuma a jajjefe bijimin. “In mutum ya bar rami a buɗe, ko ya haƙa rami bai kuma rufe ba, sai saniya ko jaki ya fāɗi a ciki, Mai ramin zai biya rashin da aka yi wa mai shi, matacciyar saniyan ko jakin, zai zama na mai ramin. “In bijimin mutum ya raunana bijimin wani, har ya mutu, sai mutanen biyu su sayar da mai ran, su raba kuɗin daidai, haka ma su yi da mai ran. Amma fa, in tun can, an san bijimin yana da wannan halin faɗa, duk da haka mai shi bai ɗaura shi ba, dole mai shi yă biya, dabba domin dabba, matacciyar dabbar kuwa tă zama nasa. (Fitowa 21:32-36)
Shugabanni
Sama’ila kuwa ya ce wa mutanen da suke roƙo yă naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa. Ya ce musu, “Ga abin da sarkin da zai yi mulkinku zai yi. Zai kwashe ’ya’yanku yă sa su yi aiki da kekunan yaƙi da dawakansa, waɗansu za su riƙa gudu a gaban keken yaƙinsa. Zai karɓi gonakinku mafi kyau da gonakin inabinku da gonakin zaitunku yă ba wa ma’aikatansa. Zai kuma karɓi zakan hatsinku da na inabinku yă ba shugabannin fadarsa da sauran masu hidimarsa. Zai ƙwace bayinku maza da mata, da shanunku, da jakunanku mafi kyau domin su yi masa aiki. Zai karɓi zakan dabbobinku, ku kanku za ku zama bayinsa. (1 Sama’ila 8:10-11, 14-17)
“ ‘Sarki zai kasance da fili da ya yi iyaka da kowane gefe na yankin wuri mai tsarki da kuma mallakar birnin. Zai miƙe ya yi wajen yamma daga gefen yamma ya kuma yi wajen gabas daga gefen gabas, yana miƙewa a tsawo daga wajen yamma zuwa wajen gabashin iyaka don yă yi hannun riga da rabon kabilan. Wannan fili zai zama mallakarsa a Isra’ila. Kuma sarakunana ba za su ƙara zaluntar mutanena ba amma za su bar gidan Isra’ila ya mallaki ƙasar bisa ga kabilansu. (Ezekiyel 45:7-8)
Annabci
Irmiya ya ce, “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, Hananel ɗan Shallum ɗan’uwan mahaifinka zai zo wurinka ya ce, ‘Saya filina a Anatot, domin a matsayinka na dangi na kurkusa hakkinka ne kuma kai ya wajaba ka saye shi.’ saboda haka sai na saye filin a Anatot daga hannun Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina na kuma auna masa shekel goma sha bakwai na azurfa. ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka ɗauki waɗannan takardun ciniki, wanda aka liƙe da wanda ba a liƙe ba, ka sa su a cikin tulun yumɓu don kada su lalace. Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa za a sāke saye gidaje, filaye da gonakin inabi a wannan ƙasa.’ (Irmiya 32:6-7, 9, 14-15)
Ko da yake za a ba da birnin ga Babiloniyawa, kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka ce mini, ‘Saye fili da azurfa ka kuma sa a shaida cinikin.’ ” (Irmiya 32:25)
Rikici ya yi girma ya zama sandar da za a hukunta mugunta; babu wani daga cikin mutanen da za a bari, babu wani dukiyarsu da za a bari, babu wani abin amfani. Lokaci ya yi! Ranar ta gabato! Kada mai saya ya yi farin ciki ko kuwa mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama hasala tana a kan dukan jama’a. Mai sayarwa ba zai mayar da ƙasar da ya sayar tuntuni ba muddin dukansu suna da rai, gama ba za a sauya wahayin da ya shafi dukan jama’a ba. Saboda zunubansu, babu ɗayansu da zai adana ransa. “ ‘Za su zubar da azurfarsu a tituna, zinariyarsu kuma za tă zama ƙazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu a ranar hasalar Ubangiji ba. Ba za su ƙosar da yunwansu ko su cika cikinsu da shi ba, gama su ne sanadin tuntuɓensu cikin zunubi. (Ezekiyel 7:11-13, 19)
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar, tunani zai shiga cikin zuciyarka za ka kuma ƙirƙiro muguwar dabara. Za ka ce, “Zan kai hari wa ƙasar da ƙauyukanta ba su da katanga; zan fāɗa wa mutanen da suke zamansu kurum cikin salama, dukansu suna zama babu katanga babu ƙofofi ko ƙyamare. Zan washe in kwashe ganima in kuma juye hannuna gāba da kufai da aka sāke zaunar da mutanen da aka tattara daga al’ummai, masu yawan shanu da kayayyaki, masu zama a tsakiyar ƙasa.” Sheba da Dedan da ’yan kasuwar Tarshish da dukan ƙauyukanta za su ce maka, “Ka zo ka kwashe ganima ne? Ka tattara jama’arka don ka yi waso, ka kuma kwashe azurfa da zinariya, ka kwashe shanu da kayayyaki ka kuma ƙwace ganima mai yawa?” ’ (Ezekiyel 38:10-13)
Sa’ad da yankuna mafi arziki suke ji kome lafiya yake, zai kai musu hari kuma Zai aikata abin da kakanninsa ba su taɓa yi ba. Zai rarraba abin da aka kwaso daga yaƙi, da ganima, da dukiya ga dukan mabiyansa. Zai kuma yi shiri yă kai wa mafaka hari, amma na ɗan lokaci ne kawai. (Daniyel 11:24)
A maimakonsu, zai ɗaukaka allahn kagarai; allahn da kakanninsa ba su ko sani ba, shi ne zai miƙa masa zinariya, da azurfa, da duwatsu masu daraja, da abubuwa masu tsada. (Daniyel 11:38)
Zai mallaki dukiyoyi na zinariya, da na azurfa, da dukan abubuwa masu tsada na Masar. Zai kuma ci Libiyawa da Kush da yaƙi. (Daniyel 11:43)
Ranar Ubangiji tana zuwa sa’ad da za a raba muku ganimar da aka washe daga gare ku. Zan tara dukan al’ummai su yaƙi Urushalima; za a ci birnin da yaƙi, za a washe gidaje, a kuma yi wa mata fyaɗe. Rabin birnin zai je bauta, amma ba za a kwashe sauran mutanen daga birnin ba. (Zakariya 14:1-2)
Yahuda ma za tă yi yaƙi a Urushalima. Za a tattara dukiyar al’umman da suke kewaye, za a tara zinariya da azurfa masu yawan gaske tare da tufafi. (Zakariya 14:14)
“Haka ma aka yi a zamanin Lot. Mutane suna ci, suna sha, suna saya, suna sayarwa, suna shuki, suna kuma gine-gine. (Luka 17:28)
Amma fa ka san wannan, za a yi lokutan shan wahala a kwanakin ƙarshe. Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, (2 Timoti 3:1-2)
Sai na ji wani abu mai ƙara kamar wata murya a tsakiyar halittu huɗun nan masu rai tana cewa, “Kwatan alkama don albashin aikin yini, da kuma kwata uku na sha’ir don albashin yini guda, kada kuwa ka ɓata man da ruwan inabi!” (Ru’uya ta Yohanna 6:6)
Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka. Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan! (Ru’uya ta Yohanna 6:15-16)
Sauran ’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba. Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba. (Ru’uya ta Yohanna 9:20-21)
Ta kuma tilasta wa kowa, manya da yara, mawadata da matalauta, ’yantattu da bayi, don a yi musu alama a hannun dama ko a goshi, don kada kowa yă saya ko yă sayar, sai dai yana da alamar, wadda take sunan dabbar ko kuma lambar sunanta. (Ru’uya ta Yohanna 13:16-17)
Macen tana saye da tufafi masu ruwan ja da shunayya, tana ƙyalli da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai. Tana riƙe da kwaf na zinariya a hannunta, cike da abubuwa masu banƙyama da kuma ƙazantar zinace zinacenta. (Ru’uya ta Yohanna 17:4)
Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.” (Ru’uya ta Yohanna 18:3)
“Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi; kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane. “Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’ Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki su ce, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja, mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai! Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’ “Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa. Sa’ad da suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi ihu su ce, ‘An taɓa samun birni kamar wannan babban birnin kuwa?’ Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a teku suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa! Cikin sa’a ɗaya ta hallaka!’ (Ru’uya ta Yohanna 18:11-19)
Mutane marasa gaskiya a ikilisiya da wuraren addini
In dai kuka canja hanyoyinku da ayyukanku kuma kuna aikata adalci da junanku, in ba ku zalunci baƙo, maraya ko gwauruwa ba kuma in ba ku zub da jinin marar laifi a wannan wuri ba, in kuma ba ku bi waɗansu alloli da za su cuce ku ba, to, zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasar da na ba kakanninku har abada abadin. Amma ga shi, kuna dogara ga maganganu na ruɗami marasa amfani. “ ‘Za ku yi sata da kisa, ku yi zina da rantsuwar ƙarya, kuna ƙone turare wa Ba’al kuna kuma bin waɗansu allolin da ba ku sani ba, Wannan gidan da ake kira da Sunana ya zama kogon ’yan fashi ne a gare ku? Amma ina kallo! In ji Ubangiji. (Irmiya 7:5-9, 11)
Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne, firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su, annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa, “Ba Ubangiji yana tare da mu ba? Ba bala’in da zai zo mana.” (Mika 3:11)
Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai. Ya ce musu, “A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’ amma kuna mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ” (Mattiyu 21:12-13)
Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru, ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki. Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’? Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’” (Markus 11:15-17)
Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya. Ya ce musu, “A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan addu’a,’ amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ” (Luka 19:45-46)
A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi. Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu. Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, “Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!” (Yohanna 2:14-16)
Yanzu a shirye nake in ziyarce ku sau na uku, ba zan kuma nawaita muku ba, don ba kayanku nake so ba, ku nake so. Gama ba yara ne da ɗaukar nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukar nauyin yaran. (2 Korintiyawa 12:14)
To, dole mai kula da Ikkilisiya yă kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba. (1 Timoti 3:2-3)
Haka masu hidima a cikin ikkilisiya; su ma, su zama maza da sun cancanci girmamawa, masu gaskiya, ba masu yawan shan ruwan inabi ba, ba masu kwaɗayin ƙazamar riba ba. (1 Timoti 3:8)
...da yawan tankiya tsakanin mutane masu mugun hali, waɗanda aka raba su da gaskiya, suke kuma tsammani cewa bin Allah wata hanya ce ta samun kuɗi. Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. (1 Timoti 6:5-6)
Gama akwai ’yan tawaye da yawa, masu surutun banza da masu ruɗi, musamman ƙungiyar masu kaciya. Dole a hana su yin magana, domin suna kawo rushewar iyalai ta wurin koyar da abubuwan da bai kamata su koyar ba don neman ƙazamar riba. (Titus 1:10-11)
Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗan’uwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana. Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula, ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima; (1 Bitrus 5:1-2)
Ra’ayi
Wanda yake son kuɗi ba zai taɓa ƙoshi ba
Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe; duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu. Wannan ma ba shi da amfani. Kamar yadda kaya suke haɓaka, haka ma masu amfani da su. Kuma wane amfani ne suke ga mai shi in ba ciyar da idanunsa a kansu ba? (Mai Hadishi 5:10-11)
Ayoyi dabam-dabam
Ruwa da yawa ba zai iya kashe ƙauna ba, koguna ba za su iya kwashe ta ba. In wani zai bayar da dukan dukiyar gidansa don ƙauna, za a yi masa dariya ne kawai. (Waƙar Waƙoƙi 8:7)
...zai zama abu ɗaya ga firist kamar yadda yake ga mutane, ga maigida kamar yadda yake ga bawa, ga uwargijiya kamar yadda yake ga baiwa, ga mai sayarwa kamar yadda yake ga mai saya, ga mai karɓan rance kamar yadda yake ga mai ba da rance, ga mai karɓan bashi kamar yadda yake ga mai ba da bashi. (Ishaya 24:2)
Gama ga abin Ubangiji yana cewa, “An sayar da ke ba da kuɗi ba, kuma ba da kuɗi za a fanshe ki ba.” (Ishaya 52:3)
Zinariya ta rasa kyanta, hasken zinariya ya dushe! An warwatsar da tsarkakakkun duwatsu masu daraja a kan tituna. Dubi samarin Sihiyona masu daraja, waɗanda a dā darajarsu ta isa nauyin zinariya, yanzu ana ɗaukar su a matsayin tukwanen ƙasa, aikin maginin tukwane! (Makoki 4:1-2)
“Amma ba su kula ba, suka kama gabansu, ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya kuma ya tafi kasuwancinsa. (Mattiyu 22:5)
Sai wani mutum daga cikin taron ya ce masa, “Malam, ka ce wa ɗan’uwana ya raba gādon da ni.” Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai, wa ya naɗa ni alƙali, ko mai sulhu a tsakaninku?” Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.” (Luka 12:13-15)
Yesu ya ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki wanda aka yi wa manajansa zargin yin banza da dukiyarsa. Sai ya kira manajan, ya tambaye shi, ‘Me nake ji haka a kanka? Ka kawo lissafin aikinka, domin ba za ka iya cin gaba da aikinka ba.’ “Sai manajan ya ce cikin tunaninsa, ‘Maigidana zai kore ni daga aiki, me zan yi? Ba ni da ƙarfin noma, kuma ina jin kunyan yin bara. Na san abin da zan yi, don mutane su karɓe ni a gidajensu, bayan an kore ni daga aiki a nan.’ “Sai ya kira kowane ɗaya da maigidansa yake bin bashi. Ya tambayi na farkon ya ce, ‘Nawa ne maigidana yake bin ka?’ “Ya amsa ya ce, ‘Garwar mai na zaitun guda ɗari tara.’ “Manajan ya ce, ‘Ga takardarka, ka zauna maza ka mai da shi ɗari huɗu.’ “Ya kuma tambayi na biyun, ‘Kai fa, nawa ne ake bin ka?’ “Sai ya amsa ya ce, ‘Buhunan alkama dubu.’ “Ya ce, ‘Ga takardarka, ka mai da shi ɗari takwas.’ “Maigidan kuwa ya yabi manajan nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama ’yan duniyan nan suna da wayon yin hulɗa da junansu fiye da ’yan haske. Ina gaya muku, ku yi amfani da dukiya na wannan duniya, domin ku sami wa kanku abokai. Saboda bayan dukiyar ta ƙare, za a karɓe ku a wuraren zama da sun dawwama. “Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba. In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya? In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiyar wani ba, wa zai ba ku dukiya naku, na kanku? “Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya dāge ga yi wa ɗaya bauta, sa’an nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.” Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki. (Luka 16:1-14)
Sa’ad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi, ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yă karɓi Ruhu Mai Tsarki.” Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi! Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba. Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka. Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma daure cikin zunubi.” Sai Siman ya amsa ya ce, “Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda ni don kada ko ɗaya daga cikin abin da ka faɗa ya same ni.” (Ayyukan Manzanni 8:18-24)
...kamar dai yadda nake ƙoƙarin faranta wa kowa rai, ta kowace hanya. Gama ba don kaina kaɗai nake yi ba, sai dai don amfanin mutane da yawa, don su sami ceto. (1 Korintiyawa 10:33)
A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da shan masifu. cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne. (2 Korintiyawa 6:4, 10)
Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah. Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba. Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah. Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku, ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka. Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne. (Kolossiyawa 3:1-5)
Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya, (1 Timoti 4:4)
Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau. (Ibraniyawa 10:34)
Ta wurin bangaskiya ne Musa, sa’ad da ya yi girma, ya ƙi a kira shi ɗan diyar Fir’auna. Ya zaɓa yă sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yă ji daɗin sha’awace-sha’awacen zunubi na ɗan lokaci. Ya ɗauki wulaƙancin da yake sha saboda Kiristi ya fi dukiyar Masar daraja, domin ya sa ido ga ladansa. (Ibraniyawa 11:24-26)
Alheri duk da kuɗin da aka bayar domin mugunta
Yowab ya ce wa mutumin da ya ba shi labarin, “Mene! Ka ga shi? Don me ba ka buge shi har ƙasa nan da nan ba? Ai, da na ba ka shekel goma na azurfa da abin ɗamarar jarumi.” Amma mutumin ya ce wa Yowab, “Ko da za a auna mini azurfa dubu a hannuna, ba zan miƙa hannuna in taɓa ɗan sarki ba. A kunnuwanmu fa sarki ya umarce ka, da Abishai, da Ittai cewa, ‘Ku tsare saurayin nan Absalom a madadina.’ (2 Sama’ila 18:11-12)
Ɗan haya na yaƙi
Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu. Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura, ya yi yaƙi da Yahuda, ya kuma gina Rama don yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa, sarkin Yahuda. Sai Asa ya ɗauki dukan azurfa da kuma zinariyar da suka rage a ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma nasa fadan, ya ba da su ga wani shugabansa, ya kuma aika da su zuwa ga Ben-Hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus. Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakanina da kai, kamar yadda ta kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, ina aika maka kyautai na azurfa da na zinariya. Yanzu fa sai ka janye yarjejjeniyarka da Ba’asha sarkin Isra’ila, don yă janye daga gare ni.” Ben-Hadad ya yarda da maganar Sarki Asa, ya kuma aika shugabannin sojojin mayaƙansa ya yi yaƙi da garuruwan Isra’ila. Ya kame Iyon, Dan, Abel-Bet-Ma’aka da dukan Kinneret, haɗe da Naftali. (1 Sarakuna 15:16-20)
Sai Rezin sarkin Aram, da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su kai wa Urushalima hari, suka kuma kewaye Ahaz, amma ba su iya shan ƙarfinsa ba. Ahaz ya ɗauki azurfa da zinariyar da suke a haikalin Ubangiji da suke kuma a ma’ajin fada ya aika wa sarkin Assuriya kyauta. Sai sarkin Assuriya ya ji roƙonsa. Ya tashi ya fāɗa wa Damaskus da hari ya kuma kame ta. Ya kwashi mazaunanta zuwa Kir, ya kuma kashe Rezin. (2 Sarakuna 16:5, 8-9)
Sai Asa ya ɗauki azurfa da zinariya daga ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma na fadansa ya aika wa Ben-Hadad sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus. Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakani na da kai kamar yadda ya kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Dubi ina aika maka azurfa da zinariya. Yanzu ka yanke yarjejjeniya da Ba’asha sarkin Isra’ila domin yă janye daga gare ni.” Ben-Hadad ya yarda da Sarki Asa ya kuma aika da manyan hafsoshin mayaƙansa a kan garuruwan Isra’ila. Suka ci Iyon, Dan, Abel-Mayim da kuma dukan biranen ajiya na Naftali. (2 Tarihi 16:2-4)
Shari’a a kotu
Amma laifofinku sun raba ku da Allahnku; zunubanku sun ɓoye fuskarsa daga gare ku, saboda kada yă ji. Babu wani mai ce a yi adalci; babu wani mai nema a dubi al’amarinsa da mutunci. Sun dogara a gardandamin banza suna ƙarairayi; suna ɗaukar cikin ɓarna, su haifi mugunta. (Ishaya 59:2, 4)
“Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku. Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe. (Mattiyu 5:25-26)
In kuma wani yana so yă yi ƙararka yă ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma. (Mattiyu 5:40)
In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa ’yar cikin ma. Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka. (Luka 6:29-30)
Yayinda kake kan hanyar zuwa kotu da maƙiyinka, ka yi matuƙar ƙoƙari ku shirya tun kuna kan hanya. In ba haka ba, zai kai ka gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma ya jefa ka a kurkuku. Ina gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.” (Luka 12:58-59)
In wani a cikinku yana da damuwa da wani, don me zai kai ƙara a gaban marasa bi, maimakon yă kai ƙara a gaban tsarkaka? Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa za ku yi wa duniya shari’a, ai, kun isa ku yi shari’a a kan ƙananan damuwoyi ke nan. Ba ku san cewa za mu yi wa mala’iku shari’a ba? Balle al’amuran da suka shafi duniyan nan! Saboda haka, in kuna da damuwa game da irin waɗannan al’amura, sai ku naɗa alƙalai ko cikin waɗanda ba kome ba ne a ikkilisiya! Na faɗi haka ne don ku ji kunya. Ashe, ba za a iya samun wani a cikinku mai hikima wanda zai iya sasanta tsakanin masu bi ba? Me zai sa ɗan’uwa yă kai ƙarar ɗan’uwa, a gaban marasa bi? Ƙarar junanku ma da kuke yi, ai, kāsawa ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura ko an zambace ku? Amma ga shi ku da kanku kuna cuta, kuna kuma zamba, har ma ga ’yan’uwanku ne kuke yi wannan. (1 Korintiyawa 6:1-8)
Mugaye suna gāba da aikin Allah idan zai ci musu kuɗi
Wata rana muna tafiya zuwa wurin yin addu’a, sai muka sadu da wata baranya mai ruhun aljani mai duba. Takan samo wa mutanenta kuɗi da yawa, duban da take yi. Wannan yarinya kuwa ta bi Bulus da kuma sauranmu, tana ihu tana cewa, “Waɗannan mutane bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, suna sanar da ku hanyar ceto.” Ta yi ta faɗin haka har kwanaki masu yawa. A ƙarshe Bulus ya damu ƙwarai sai ya juya ya ce wa aljanin, “A cikin sunan Yesu Kiristi na umarce ka, ka rabu da ita!” Nan take aljanin ya rabu da ita. Da iyayengijin baranyar suka ga hanyar samun kuɗinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila suka ja su zuwa cikin kasuwa don su fuskanci hukuma. (Ayyukan Manzanni 16:16-19)
Wani maƙerin azurfa, mai suna Demetiriyus wanda yake ƙera siffar ɗakunan tsafin Artemis da azurfa, ba ƙaramin ciniki yake kawo wa mutane masu sana’an nan ba. Sai ya tara su wuri ɗaya, tare da masu irin wannan sana’ar ya ce, “Ku jama’a, kun san muna samun kuɗin shiga sosai daga wannan sana’a. Kuma kuna ji kuna gani yadda Bulus ɗin nan ya shawo kan mutane da yawa ya kuma sa suka bauɗe a nan a Afisa da dukan lardin Asiya. Yana cewa alloli da mutum ya ƙera ba alloli ba ne ko kaɗan. Akwai hatsari, ba kawai cewa sana’armu za tă rasa sunanta mai daraja ba, amma za a yi banza da ɗakin tsafin Artemis alliyarmu mai girma, alliyar kanta wadda ake bauta a ko’ina a yankin Asiya da kuma duniya, za a raba ta da darajarta.” (Ayyukan Manzanni 19:24-27)